ALLAHU Akbar! Allah ya yi wa jaruma a Kannywood, Zainab Umar, rasuwa.
Zainab ta rasu a daren jiya Alhamis, 5 ga Satumba, 2024 da misalin ƙarfe 8:00 a gidan mijin ta da ke Layin ‘Yan Kifi, Rigasa, Kaduna, bayan fama da ciwon ciki na kwana biyu.
An yi jana’izar ta a ƙofar gidan mijin nata a yau Juma’a da misalin ƙarfe 9:00 na safe, daga nan aka kai ta gidan ta na gaskiya.
Marigayiyar, mai kimanin shekara 27 a duniya, ta rasu ta bar mijin ta da ɗa ɗaya.
Zainab ta na ɗaya daga cikin ‘ya’yan kamfanin shirya finafinai na Gidaje Films da ke Tudun Wada, Kaduna.
Shugaban kamfanin, Sabi’u Muhammad Gidaje, ya shaida wa wakilin mu cewa, “Zainab ta taɓa aure, bayan ta fito daga gidan miji ne ta shigo harkar fim. Amma da yake Allah na son ta rasu a ɗakin mijin ta ne, ba ta daɗe da komawa ɗakin mijin nata ba, Allah ya ɗauki rayuwar ta.”
Wasu daga cikin finafiinan da ta fito a ciki sun haɗa da ‘Duhun Zuciya’, ‘Manyan Mata’, ‘Fansar Waye’ da ‘Yan Nepa’.
Allah ya jiƙan Zainab da rahama, ya albarkaci dukkan abin da ta bari, amin.
![]()







