• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Tarayya ta fara gudanar da zauren tattaunawa na ministoci karo na biyu

by WAKILIN MU
February 22, 2025
in Nijeriya
0
Gwamnatin Tarayya ta fara gudanar da zauren tattaunawa na ministoci karo na biyu

Alhaji Mohammed Idris yana gabatar da jawabin buɗe taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MA’AIKATAR Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta fara zagaye na biyu na Zauren Tattaunawa na Ministoci, inda Ministan Raya Kiwon Dabbobi, Alhaji Idi Mukhtar; da Ministan Cigaban Yankuna, Injiniya Abubakar Eshiokpekha Momoh, da Ƙaramin Ministan sa, Alhaji Uba Maigari Ahmadu, suka gabatar da jawabai kan ayyukan ma’aikatun su.

Da yake gabatar da jawabin maraba, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana wannan zama da aka yi ranar Juma’a a matsayin dandalin da ke baje-kolin nasarorin da Gwamnatin Tinubu ta cimma a fannoni daban-daban.

Ya ce: “Ina maku maraba da zuwa zagaye na biyu na Zauren Tattaunawa na Ministoci na shekarar 2025. Kamar yadda kuka sani, a ranar Talata, 11 ga Fabrairu, 2025, na ƙaddamar da wannan jerin tarurruka na bana, inda na jaddada manyan nasarorin da aka cimma a ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.”

Ya ce Ma’aikatar Raya Kiwon Dabbobi da ta Cigaban Yankuna suna daga cikin sababbin ma’aikatun da Shugaban Ƙasa Tinubu ya ƙirƙira domin bunƙasa fannin kiwo da haɓaka cigaban yankuna a Nijeriya.

Jerin ministoci da jami’ai a taron

Ya ce: “Waɗannan ma’aikatun guda biyu su ne sababbi a ƙasar. An kafa Ma’aikatar Raya Kiwon Dabbobi a watan Yulin 2024 domin sauya damar kiwon dabbobi mai darajar biliyoyin daloli zuwa ingantaccen cigaban tattalin arziki ga ‘yan Nijeriya.

“Haka nan, an kafa Ma’aikatar Raya Yankuna a watan Oktoban 2024 domin kula da ayyukan hukumomin raya yankuna a faɗin ƙasar nan.

“Tun bayan kafuwar waɗannan ma’aikatun, ministocin sun fara aiki da himma, kuma sun zo a yau domin ƙarin bayani kan abin da suka aiwatar tun daga lokacin da aka ƙirƙiri ma’aikatun nasu.”

Ministan ya yaba da rawar da ‘yan jarida ke takawa wajen yaɗa labaran zaman tattaunawar ministocin, yana mai cewa su ne ginshiƙin isar da sahihan bayanai ga ‘yan Nijeriya.

Ya kuma buƙaci ‘yan jarida da su guji yaɗa rahotannin da ke da ruɗani ko kwaskwarima.

Ya ce: “Kafofin watsa labarai sun kasance abokan hulɗar da ba za a iya musantawa ba a ƙoƙarin mu na ci gaba da sanar da ‘yan Nijeriya kan manyan nasarorin da Gwamnatin Tinubu ta cimma.

“Ina kira ga ‘yan jarida da su tabbatar da cewa rahotannin da suka shafi waɗannan tarurruka na bayar da bayanai ana gabatar da su da cikakken adalci da inganci.

“Bai kamata a riƙa cusa son rai ko ɓata gaskiya wajen rahoto kan manufofi da shirye-shiryen gwamnati ba.

“Yana da kyau a samu sukar ra’ayi da bambancin fahimta domin dimokiraɗiyya, amma kada a bari ji-ta-ji-ta da karkatar da gaskiya su samu gurbi a muhawarar jama’a.”

Ya tabbatar da cewa gwamnati za ta yaɗa bayanan wannan zaman tattaunawar ta kafafen yaɗa labarai daban-daban domin tabbatar da gaskiya da karɓar ra’ayoyin jama’a.

Za a ci gaba da shirye-shiryen Zauren Tattaunawa na Ministocin, inda manyan jami’an gwamnati za su riƙa gabatar da bayanai kan cigaban da ake samu a fannoni daban-daban.

Mahalartan taron

Loading

Tags: Alhaji Idi MukhtarAlhaji Mohammed IdrisAlhaji Uba Maigari AhmaduInjiniya Abubakar Eshiokpekha MomohMa'aikatar Cigaban YankunaMa'aikatar Raya Kiwon DabbobiZauren Tattaunawar Ministoci
Previous Post

Furodusa a Kannywood, Fatima Lamaj ta zama Daraktar Bikin Baje Kolin Finafinai na Duniya na Kaduna

Next Post

Hotuna: Gwamna ya ziyarci Minista

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Hotuna: Gwamna ya ziyarci Minista

Hotuna: Gwamna ya ziyarci Minista

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!