• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, October 16, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Furodusa a Kannywood, Fatima Lamaj ta zama Daraktar Bikin Baje Kolin Finafinai na Duniya na Kaduna

by ABBA MUHAMMAD
February 21, 2025
in Labarai
0
Furodusa a Kannywood, Fatima Lamaj ta zama Daraktar Bikin Baje Kolin Finafinai na Duniya na Kaduna

Hajiya Fatima Ibrahim Ahmad (Lamaj)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Babban Daraktan Bikin Baje Kolin Finafinai na Duniya na Kaduna (Kaduna International Film Festival), Israel Kashim Audu, ya naɗa fitacciyar furodusa a Kannywood, Hajiya Fatima Ibrahim Ahmad (Lamaj), a matsayin daraktar bikin baje kolin finafinan.

A cikin sanarwar da ke ɗauke da sa hannunsa, Audu ya bayyana cewa: “Bikin Baje Kolin Finafinai na Duniya na Kaduna ta naɗa ki a matsayin daraktan bikin finafinai.”

Ya ce naɗin ya samo asali ne sakamakon gudummawar da ta bayar da kuma jajircewarta ga yanayin muhalli a Afirka da Nijeriya gaba ɗaya.

“Shekarun ki da gogewar ki a Nollywood musamman ma masana’antar finafinan Hausa ba za su iya wuce wa ba haka nan, kuma muna jin daɗin nasarar ki.”

Ya ƙara da cewa, a matsayin ta ta daraktar bikin baje koli, za ta kasance daraktar shirye-shirye na shirin ‘yar’uwar mu a taron finafinan Arewa da taron ƙirƙire-ƙirƙire na Afirka.

“Mun yi imanin cewa za ki kawo ɗimbin gogewa da shawarwari da kuma gudummawar ki ga Bikin Baje Kolin Finafinai na Duniya na Kaduna, don ci-gaban da’irar bikin finafinai a Nijeriya.”

Audu ya jaddada cewa bikin finafinai na Kaduna shi ne na farko a Arewacin Nijeriya da aka fara a shekarar 2018, wanda aka ƙirƙira domin bunƙasa al’adu, zane-zane, yawon shaƙatawa, zaman lafiya, ƙarfafawa da tallafawa matasa a fannonin ƙirƙire-ƙirƙire, da kuma kawar da gibi a masana’antar finafinai da ƙere-ƙere.

Baya ga wannan naɗi, an kuma naɗa daraktan a Kannywood, Alhaji Al-Amin Ciroma, a matsayin manaja na Bikin Baje Kolin Finafinai na Duniya na Kaduna.

Shi ma Al-Amin zai yi aiki a matsayin manaja na taron finafinan Arewa da taron ƙirƙire-ƙirƙire na Afirka.

Da take bayyana ra’ayinta kan naɗin da aka yi mata, Hajiya Fatima Lamaj ta nuna godiyarta, inda ta ce: “Assalamu alaikum. Alhamdu lillah! Babu abin da zan ce fa ce godiya ga Ubangiji Allah Subhanahu wa ta’ala, mai kowa mai komai. Godiya ta tabbata ga Manzon Allah shugaban duk wani halita. Mulki da ɗaukaka na Allah ne.”

Ta bayyana cewa ta fara ne a matsayin ma’aji a Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), daga nan kuma aka ba ta ƙarin matsayi a ƙungiyar AGN (Actors Guild of Nigeria).

“Da farko na kasance ‘treasurer’ a ƙungiyar masu shirya finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), bayan wannan zaɓe da Allah ya ba ni kujerar ‘treasurer’, sai kuma na samu cigaba a ƙungiyar AGN, wato ‘Actors Guild of Nigeria’, wanda president Dr. Emeka Rollers ya naɗa ni SSA on film in the Northern part of Nigeria, wato jihohi 19 na Arewacin Nijeriya, har Abuja. Sai kuma ga shi an ba ni wannan muƙami na director Kaduna International Film Festival, wanda Mista Isreal Audu ne founder.”

Lamaj ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a masana’antar finafinai da su fahimci muhimmancin bukukuwan baje kolin finafinai.

“Ina nenan haɗin kan duk wanda ke da ruwa da tsaki a duniyar industiri, dama ne a gare mu a Kannywood. Domin mutane da yawa ba su san mahimmancin film festivals ba, film festivals in dai ka yi ‘participating’ ko da film ɗin ka bai karɓu ba, kada mutum ya fidda rai ga samun nomination a gaba.”

Ta ƙara da cewa, shiga irin waɗannan bukukuwa na iya samar da haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki a masana’antar finafinai.

“Sannan shigar da fim zai iya ba ka damar haɗuwa da ‘yan kasuwar finafinai da masu shirya na duniya. Da fatan mutane za su maida hankali a kan ‘film festivals’ da shiga award, domin shiga award zai ƙara ma mutum CV ɗin sa da kuma tallata hajar sa.”

A ƙarshe, ta yi kira ga mutane da kada su raina ƙungiyoyi, domin suna da fa’idodi da za su amfana da su.

“Ina ma kowa fatan alheri, kuma kada mutum ya raina ƙungiya, domin duk ƙanƙantar ƙungiya ta na da damar da za ka amfana.”

Loading

Previous Post

Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta fara gudanar da zauren tattaunawa na ministoci karo na biyu

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya ta fara gudanar da zauren tattaunawa na ministoci karo na biyu

Gwamnatin Tarayya ta fara gudanar da zauren tattaunawa na ministoci karo na biyu

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!