• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, May 17, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Tinubu ba za ta goyi bayan dokokin auren jinsi ko tarayyar masu luwaɗi da maɗigo ba – Minista 

by WAKILIN MU
July 4, 2024
in Nijeriya
0
Gwamnatin Tinubu ba za ta goyi bayan dokokin auren jinsi ko tarayyar masu luwaɗi da maɗigo ba – Minista 

Alhaji Mohammed Idris

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ba za ta goyi bayan duk wani yunƙuri na auren jinsi ko ɗaure wa ‘yan luwaɗi da masu maɗigo a Nijeriya ba.

Ministan ya faɗi haka ne a yayin da yake martani kan labarin da aka yaɗa a ranar Alhamis cewa Gwamnatin Tarayya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da aka yi a ƙasar Samoa, wadda za ta ba da dama a hukumance ga ‘yan luwaɗi da masu maɗigo a Nijeriya.

A rahoton da wasu kafafen yaɗa labarai suka buga, an ruwaito cewa yarjejeniyar ta ƙunshi wasu tanade-tanade ne waɗanda ke buƙatar goyon bayan kare haƙƙin ‘yan luwaɗi da masu maɗigo a matsayin sharaɗin samun tallafin kuɗi da sauran taimako daga ƙasashen da suka ci gaba.

Lamarin dai ya haifar da ce-ce-ku-ce, inda wasu malaman addini da masu rajin kare haƙƙin ɗan’adam ke sukar gwamnati kan amincewa da yarjejeniyar da ta yi.

To amma a ƙarin hasken da ya yi kan yarjejeniyar, Minista Idris ya ce ai Nijeriya tana da dokoki tun tuni waɗanda suka haramta auren jinsi ko tarayyar ‘yan luwaɗi da masu maɗigo, kuma dokokin sun girmi wannan yarjejeniyar ta Samoa da ake ta ce-ce-ku-ce a kan ta.

Ya ce, “A ranar 28 ga Yuni, 2024 ne gwamnatin Nijeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar Samoa ɗin a sakatariyar Ƙungiyar Ƙasashen Afirka, Karibbiyan da Pacific (OACPS) a birnin Brussels na ƙasar Beljiyam.

“An fara tattaunawa kan yarjejeniyar tun a shekarar 2018, a lokacin taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 73. Ɗaukacin ƙasashe membobin Tarayyar Turai su 27 da ƙasashe 47 daga cikin 79 na OACPS ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a garin Apia da ke Tsibirin Samoa a ranar 15 ga Nuwamba, 2018.

“Nijeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Juma’a, 28 ga Yuni, 2024. Hakan ya biyo bayan nazarin da ta yi tare da tuntuɓar Kwamitin Ministoci da Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki ta kafa tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Waje da Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya.

“An tabbatar da cewa babu ɗaya daga cikin Tanade-tanade 103 na yarjejeniyar waɗanda suka saɓa wa Kundin Tsarin Mulki na 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima ko dokokin Nijeriya, da sauran wasu dokoki.

“Bugu da ƙari, amincewar da Nijeriya ta yi yana ƙunshe da sanarwa mai ɗauke da kwanan wata 26 ga Yuni, 2024, inda ta fayyace fahimtar ta da kuma yanayin yarjejeniyar a ƙarƙashin ikon ta na cewa ba a amince da duk wani tanadi da ya saɓa wa dokokin Nijeriya ba.

“Yana da kyau a lura da cewa akwai dokar da aka kafa a Nijeriya game da dangantakar auren jinsi ɗaya tun a cikin 2014.”

A ƙarshe, ministan ya ce, “Ya zama wajibi a tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, kasancewar ta gwamnati mai bin ƙa’ida, ba za ta shiga wata yarjejeniya ta ƙasa da ƙasa wadda za ta cutar da ƙasa da ‘yan ƙasar ta ba.

“Yarjejeniyar Samoa ba komai ba ce illa wani muhimmin tsarin doka na haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen ƙungiyar OACPS da Tarayyar Turai don inganta cigaba mai ɗorewa, da yaƙi da sauyin yanayi da illolin sa, da samar da damar zuba jari, da samar da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe membobin OACPS a matakin ƙasa da ƙasa.”

Loading

Tags: luwaɗi da maɗigoMohammed IdrisShugaba Bola Ahmed TinubuYarjejeniyar Samoa
Previous Post

Jarumar Kannywood, Raihan Ƙamshi ta yi bikin zagayowar ranar haihuwar ta

Next Post

Za a ɗaura auren tsohuwar jarumar Kannywood Sadiya Gyale a yau

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Za a ɗaura auren tsohuwar jarumar Kannywood Sadiya Gyale a yau

Za a ɗaura auren tsohuwar jarumar Kannywood Sadiya Gyale a yau

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!