• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Tinubu za ta ba da fifiko wajen amfani da na’urorin zamani a gidajen rediyo da talbijin, inji Minista

by DAGA WAKILIN MU
October 26, 2023
in Nijeriya
0
Alhaji Mohammed Idris ya na jawabi a taron

Alhaji Mohammed Idris ya na jawabi a taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa amfani da kayan aiki na zamani a gidajen rediyo da talbijin na da muhimmanci ga gwamnatin Bola Tinubu.

Haka kuma ya jaddada alwashin gwamnati na bai wa harkokin bunƙasa kayan aikin rediyo, talbijin da shirya finafinai goyon baya saboda muhimmancin su ga bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Ya ce su na a sahun gaba wajen samun nasarar inganta tattalin arziki a ƙarƙashin ajandar Farfaɗo da Martabar Nijeriya ta ‘Hope Agenda’ da gwamnatin Tinubu ta himmatu a kai.

Da ya ke jawabi wurin taron AFRICAST na 13 a ranar Talata, otal ɗin Marriot da ke Ikeja, Legas, ministan ya nuna farin cikin sa, ganin yadda taron ya kasance ƙasaitacce, duba da yadda ya ke tafiya bisa kyakkyawan shugabanci, ake bajekolin ilmi da kuma samun damarmakin bunƙasa kasuwancin fasaha da na’urorin zamani.

Ya ce Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NBC) ta ƙirƙiro AFRICAST ne ganin yadda ake samun yawaitar kafa gidajen rediyo, talbijin da bunƙasar harkokin finafinai da sauran kafafen isar da saƙo.

Idris ya yaba wa masu shirya taron, wanda aka shirya tare da haɗin gwiwar NIFS, ya ce taron ya samar da wani dandalin da ƙwararru a harkokin finafinai da talbijin za su samu dama da lasisin bayyana hajar su.

Ya bayyana muhimmancin rawar da masu ƙirƙiro shirye-shirye, furodusoshi da masu yaɗa shirye-shirye ke takawa wajen nishaɗantarwa a duniya.

Sai ya nuna muhimmancin a riƙa samar da shirye-shirye masu nagarta wajen nishaɗantarwa da ilmantarwa.

Ministan ya jaddada ƙoƙarin da gwamnati ke yi domin komawa amfani da tsarin DSO wajen yaɗa labarai, tare da himma wajen rungumar duk wata hanyar yaɗa labarai ta zamani da ake amfani da ita a duniya.

Ministan, wanda ya riƙa bi ya na duba kayayyakin na’urorin yaɗa labarai da watsa shirye-shirye na zamani waɗanda aka bajekolin su a wurin, ya yaba da irin cigaban da aka samu ta hanyar ƙirƙiro sababbin na’urorin sauƙaƙa ayyukan yaɗa labarai da shirye-shirye.

Ya ce Shugaba Tinubu zai kasance jagora wajen rungumar shirin amfani da na’urorin zamani a kafafen yaɗa labarai a gidajen rediyo da talbijin na Gwamnatin Tarayya.

Loading

Previous Post

Shari’ar auren jaruma Sadiya Haruna da mijin ta G-Fresh: Kotu ta ɗage saurare zuwa 7 ga Nuwamba

Next Post

Bayan nasara a Kotun Ƙoli, Shugaba Tinubu zai ci gaba da aikin gina nagartacciyar ƙasa – Idris

Related Posts

Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina
Nijeriya

Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina

June 30, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin akwai tsaro a Abuja duk da gargaɗin da Amurka ta ba matafiya

June 23, 2025
Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya
Nijeriya

Kiran Gwamnatin Tarayya ga ‘yan jarida: Ku zama jigo wajen gina dimokiraɗiyyar Nijeriya

June 21, 2025
Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu
Nijeriya

Ministan Yaɗa Labarai ya yaba wa Hafsoshin Soji kan cigaban da aka samu a fannin tsaron ƙasa a shekaru biyu

June 20, 2025
Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Next Post
Alhaji Mohammed Idris ya na jawabi a lokacin taro da manema labarai

Bayan nasara a Kotun Ƙoli, Shugaba Tinubu zai ci gaba da aikin gina nagartacciyar ƙasa - Idris

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!