• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, November 2, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Tinubu za ta ba ‘yancin ‘yan jarida muhimmancin gaske – Minista

by DAGA WAKILIN MU
October 12, 2023
in Nijeriya
0
Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai Alhaji Mohammed Idris (a tsakiya) tare da Shugaban Ƙungiyar 'Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), Mista Chris Isiguzo, da Shugabar Ƙungiyar 'Yan Jarida Mata ta Nijeriya (NAWOJ), Ladi Bala, a lokacin ziyarar a ranar Talata

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai Alhaji Mohammed Idris (a tsakiya) tare da Shugaban Ƙungiyar 'Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), Mista Chris Isiguzo, da Shugabar Ƙungiyar 'Yan Jarida Mata ta Nijeriya (NAWOJ), Ladi Bala, a lokacin ziyarar a ranar Talata

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GWAMNATIN Bola Ahmed Tinubu da gaske ta ke yi wajen kula da ‘yancin ‘yan jarida, tare da ƙoƙarin ganin sun riƙa gudanar da aikin su ba tare da tsangwama ko wani cikas ba, a cewar Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris. 

Da ya ke jawabi a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), Idris ya kuma ce ma’aikatar sa za ta ƙara himma sosai wajen jaddada ‘yancin ‘yan jarida.

A cewar sa, ‘yancin ‘yan jarida da kafafen yaɗa labarai babban ginshiƙi ne wajen samun nasarar dimokiraɗiyya.

Kan haka ne ya ce gwamnati ta himmatu wajen tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida da kafafen yaɗa labarai.

Shugabannin ƙungiyar dai sun kai masa ziyarar ne a ranar Talata, 10 ga Oktoba, 2023.

Ministan ya bayyana manyan ƙalubalen da ‘yan jarida da kafafen yaɗa labarai ke fuskata, waɗanda ya ce sun haɗa da ‘yancin su, samun damar mallakar bayanai da kuma tsaron lafiya da rayukan su.

Ya ce NUJ ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ɗorewar dimokiraɗiyya. 

Ya hore su da a haɗa hannu domin samun ci gaba. Ya ce: “Muradin da mu ka sa a gaba shi ne mu tabbatar da cewa ‘yan jarida su na gudanar da aikin su ba tare da fargabar wata barazana ga lafiya ko rayuka ba.”

Sai dai kuma ya yi tsokacin cewa duk da ‘yancin ‘yan jarida abu ne mai matuƙar daraja a fagen yaɗa labarai, to kuma abu ne mai muhimmanci a ga cewa ana yin taka-tsantsan tare da bayar da labarai sahihai ga ‘yan Nijeriya.

A jawabin sa, Shugaban NUJ na ƙasa, Mista Chris Isiguzo, ya fayyace ƙalubalen da ‘yan jarida ke fuskanta, waɗanda su ka haɗa da ‘yancin ‘yan jarida, damar ba su bayanai a ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati, tsaron lafiya da rayukan su da kuma matsalolin na yau da kullum na tsadar rayuwa.

Ya ce ya na yi wa ministan kallon wani nagartaccen tsanin da za a taka domin a kai ƙololuwar wurin da za a iya magance waɗannan matsaloli.

Loading

Previous Post

Ba a kafa NBC don takura wa kafafen yaɗa labarai ba – Idris

Next Post

Mahaifin marubuciya Farida Gachi kuma Maigarin Gachi, Alhaji Adamu, ya riga mu gidan gaskiya

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Marigayi Alhaji Adamu Suleiman Gachi

Mahaifin marubuciya Farida Gachi kuma Maigarin Gachi, Alhaji Adamu, ya riga mu gidan gaskiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!