• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, June 6, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Tinubu za ta cusa son ƙasa a zukatan al’umma domin a yaƙi ta’addanci da hare-haren ‘yan bindiga – Minista

by ALI KANO
December 23, 2023
in Nijeriya
0
Gwamnatin Tinubu za ta cusa son ƙasa a zukatan al’umma domin a yaƙi ta’addanci da hare-haren ‘yan bindiga – Minista

Alhaji Mohammed Idris (a dama) tare da Janar Christopher Musa a lokacin ziyarar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
Alhaji Mohammed Idris (a dama) tare da Janar Christopher Musa a lokacin ziyarar

MINISTAN Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa ana ƙoƙarin cusa ƙaunar ƙasa a zukatan al’umma ne a matsayin wata dabara ta yaƙar muggan laifuka irin su hare-haren ‘yan bindiga, satar mutane, da ta’addanci a Nijeriya.

Mai tallafa wa ministan kan harkokin yaɗa labarai, Malam Rabi’u Ibrahim, ya ruwaito a cikin wata sanarwa ga manema labarai cewa Idris ya faɗi hakan ne a ranar Juma’a a Abuja lokacin da ya karɓi baƙuncin Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro (CDS), Janar Christopher Musa, wanda ya kai masa ziyarar aiki a ofishin sa.

Ministan ya ce sahihiyar hanyar da za a yaƙi aikata muggan laifuffuka ita ce a saka so da ƙaunar ƙasa da sadaukarwa a zukatan jama’a tare da haɗuwa wuri ɗaya a matsayin ‘yan ƙasa ɗaya al’umma ɗaya domin a dunƙule a yaƙi muggan laifuffuka.

Ya ce: “Tilas ne a dawo da batutuwan nan na sadaukar da kai da kuma so da ƙaunar ƙasa, domin mu samu irin haɗin kai da albarkar da dukkan mu mu ke nema. Mun ga yadda kyawawan ɗabi’un mu su ke ta sukurkucewa – tilas ne mu dawo da waɗannan kyawawan ɗabi’un kuma mu sake dawowa cikin hayyacin mu a matsayin ‘yan Nijeriya.

“Ya kamata mu sake zama mu ga inda mu ka kauce daga alƙibla da nufin yin gyaran da ya dace a yanzu.

“Na gode ƙwarai da wannan ziyara. Mu na ganin cewa irin haɗin gwiwar da ku ke so shi ne duk mu cure a wuri guda domin mu yaƙi ta’addanci kuma mu sama wa ƙasar nan haɗin kai, cigaba, da zaman lumana.

“Babu yadda za ku iya samun nasara a wannan yaƙi ba tare da babbar rawar da kafafen ɗaya labarai na Nijeriya da su kan su ‘yan Nijeriyar za su taka ba.”

Idris ya ce aikata muggan laifuffuka ya jawo ɓata suna sosai ga Nijeriya, don haka aikin da ya rataya a wuyan wannan ma’aikatar shi ne ta kyautata tare da sauya tunanin da ake yi game da ƙasar.

Ministan, wanda ya jaddada cewa yaɗa labarai na da muhimmanci ga yaƙi da ta’addanci, ya kuma ce haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatar tasa da hukumomin soja ya na da muhimmanci wajen samar da matsaya da za ta ƙarfafa tsaron ƙasa kuma ta inganta martabar ƙasar a idon duniya.

Idris ya ce nan ba da jimawa ba ma’aikatar za ta ƙaddamar da gangamin yekuwar sauya fasalin ƙasa a matsayin wani ƙoƙari na musamman da za a sanya sabon shauƙin ƙaunar ƙasa a zukatan al’umma.

“Waɗansu daga cikin waɗancan abubuwan da mu ke magana a kan su za su fara fitowa a bainar jama’a a farkon shekara mai zuwa lokacin da mu ke fatan Shugaban Ƙasa zai jagoranci gangamin yekuwar sauya fasalin ƙasa. Mu na so a sake tattaunawa kan wannan batu na ma’anar ɗan ƙasa”.

Haka kuma ministan ya buƙaci hukumomin soja da su dawo da tsarin nan na saƙa ‘yan jarida a cikin gumurzun yaƙi domin su samo bayanan farko na yadda ake yaƙi wanda ta hakan ne za a samar da labarai masu inganci.

Ana buga taken Nijeriya a lokacin ziyarar

Tun da farko sai da Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro ɗin, wato Janar Musa, ya ce ziyarar da su ka kai wa ministan ta na daga cikin dabarun su na yaƙi waɗanda ba na gumurzu ba ne domin su gina haɗin gwiwa tsakanin rundunonin soja da kafafen yaɗa labarai saboda ƙalubalen da sojoji ke fuskanta a yaƙin ta fuskoki daban-daban sun shafi jama’a ne inda su sojojin da su ‘yan ta’addan kowa so ya ke ya ja ra’ayin ‘yan Nijeriya.

Ya ce: “Wannan ya na daga cikin hanyoyin da mu ke bi na gudanar da al’amurra domin mu gina haɗin gwiwa tsakanin Rundunonin Soja da jama’ar ƙasa kuma babu inda ya fi cancanta mu fara da shi da ya fi inda labarai ke fitowa.”

Ya yi kira ga jama’a da su ba sojoji goyon baya a kan yaƙi da tada hankalin jama’a, ta’addanci, da hare-haren ‘yan bindiga.

Ya nanata cewa wannan yaƙi al’amari ne da ke buƙatar saka hannun dukkan ‘yan Nijeriya domin a murƙushe manyan masu aikata laifuffukan da ke kawo barazana ga ɗorewar ƙasar nan.

Musa ya ce gudanar da harkar yaɗa labarai cikin tsari wani babban ginshiƙi ne wajen yaƙi da ta’addanci domin yawancin ‘yan ta’addar an yaudare su har su ka tashi tsaye su na yaƙar ƙasar haihuwar su.

Ya ce ta hanyar gudanar da yaɗa labarai cikin tsari da kuma faɗakarwa, rundunar soja ta samu nasarar jawo hankalin wasu daga cikin ‘yan ta’addar su ka aje makaman su, su ka miƙa wuya ga gwamnati.

Ya yi bayyana cewa ya zuwa yanzu kimanin ‘yan ta’adda 140,000 ne su ka miƙa wuya ga rundunar soja a bisa kankin kan su.

Janar Musa ya ce yanzu aikata muggan laifuffuka ya tashi daga batun shauƙin aƙida zuwa son a samu kuɗi, inda ‘yan ta’adda ke samun ƙazamar riba ta hanyar satar mutane da kai hare-hare da sauran muggan laifuffuka.
Shugabannin hukumomin yaɗa labarai na gwamnati da su ka mara wa ministan baya wajen karɓar maziyarcin sun haɗa da Darakta-Janar na Hukumar Talbijin ta Ƙasa (NTA), Malam Abdulhamid Dembos; da takwaran sa na Hukumar Rediyo ta Nijeriya (FRCN), Dakta Mohammed Bulama; da na Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Ndace; na Hukumar Wayar Da Kai ta Ƙasa (NOA), Mista Lanre Issa-Onilu; na Hukumar Kula Da Gidajen Rediyo Da Talbijin ta Ƙasa (NBC), Mista Charles Ebuebu, da kuma Babban Sakataren Cibiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NPC), Mista Dili Ezughah.

Loading

Tags: Janar Christopher MusaMohammed Idrisrashin tsarota'addanci
Previous Post

Tsohuwar jarumar Kannywood Fati Ladan da mijin ta sun yi walimar cikar su shekara 10 da aure

Next Post

Ina hamdalar samun ‘ya’ya masu ilimi – Sadiya Garba Yakasai

Related Posts

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London
Nijeriya

Idris ya ƙaryata ji-ta-ji-tar an mayar da taron bayanin ministoci zuwa London

May 16, 2025
Next Post
Ina hamdalar samun ‘ya’ya masu ilimi – Sadiya Garba Yakasai

Ina hamdalar samun 'ya'ya masu ilimi - Sadiya Garba Yakasai

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!