• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, October 11, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Tsohuwar jarumar Kannywood Fati Ladan da mijin ta sun yi walimar cikar su shekara 10 da aure

by DAGA ABBA MUHAMMAD
December 20, 2023
in Ranar Murna
0
Tsohuwar jarumar Kannywood Fati Ladan da mijin ta sun yi walimar cikar su shekara 10 da aure

Yerima Shettima na ba Fati Ladan kek a baki

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A YAU Laraba, 20 ga Disamba, 2023 tsohuwar jarumar Kannywood, Hajiya Fati Ladan, da mijin ta, Alhaji Yerima Shettima, su ka cika shekara 10 cur da aure.

Domin yi wa Allah godiya da ya nuna masu wannan lokaci, an yi saukar Alƙur’ani yau da safe a gidan su da ke Yarima Close a cikin rukunin gidajen Jinya Close da ke Titin Kanta a cikin garin Kaduna.

Mahaddatan Alƙur’ani a bakin aiki

An fara gudanar da addu’o’i ga ma’auratan da kuma ƙasa baki ɗaya. Daga nan alarammomi su ka fara karatu bisa umarnin jagoran su.

An kammala saukar Alƙur’anin da misalin ƙarfe 10:40, sannan aka ƙara yin addu’o’in ƙarin zaman lafiya ga Fati da Yerima.

Bayan an gama, sai aka fito da abinci da abin sha, aka yi walima.

Da misalin ƙarfe 2:30 na rana, an yi ƙasaitacciyar walima ta ‘yan’uwa, ƙawaye, abokai da abokan arziki. Duk da cewa ba kowa aka gayyata ba, amma taron ya samu halartar ɗimbin mutane daga wurare daban-daban. An ci, an sha an gyatse.

Yerima Shettima, Fati da ‘ya’yan su

Bayan kammala ciye-ciye da tanɗe-tanɗe, sai ma’auratan su ka yanka kek don nuna farin cikin su da Allah ya nuna masu wannan rana.

Yerima da Fati sun ba junan su kek ɗin da su ka yanka a baki.

‘Yan’uwa da abokan arziki sun taya su murna tare da yi masu addu’ar ƙara danƙon so da ƙauna.

An tashi daga taron da misalin ƙarfe 5:30 na yamma.

Idan ba ku manta ba, a makon da ya gabata mujallar Fim ta kawo maku hirar da Fatin ta yi da manema labarai, inda ta ce Allah ya kashe ta a ɗakin mijin ta.

‘Yan Kannywood su ka halarci walimar sun haɗa da Abbas Sadiq, Jamilu Adamu Kochila, Zaharaddin Mando, Al-Amin Abdullahi Albani da Wasila Isma’il.

Allah ya ƙara masu zaman lafiya da danƙon soyayya.

Ango da amaryar shekara goma
Fati da Shettima
Ita ma ta na ba shi kek a baki

 

Loading

Tags: BikiFati Ladanshekara gomaWedding AnniversaryYerima Shettima
Previous Post

Cewar Tinubu: Gwamnati na za ta mutunta ‘yancin kafafen yaɗa labarai, za ta karɓi yabo, gyara da suka daga ‘yan jarida da marubuta

Next Post

Gwamnatin Tinubu za ta cusa son ƙasa a zukatan al’umma domin a yaƙi ta’addanci da hare-haren ‘yan bindiga – Minista

Related Posts

Furodusan ‘Wata Shida’, Hayatuddeen Yakubu ya sake aure wata 7 bayan rasuwar matar sa
Ranar Murna

Furodusan ‘Wata Shida’, Hayatuddeen Yakubu ya sake aure wata 7 bayan rasuwar matar sa

September 28, 2026
An ɗaura auren Faɗima ‘yar furodusan Kannywood marigayi Nura Shariff
Ranar Murna

An ɗaura auren Faɗima ‘yar furodusan Kannywood marigayi Nura Shariff

September 7, 2026
Farha, ‘yar tsohuwar jaruma Halima Atete, ta cika shekara ɗaya
Ranar Murna

Farha, ‘yar tsohuwar jaruma Halima Atete, ta cika shekara ɗaya

September 5, 2026
Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji
Ranar Murna

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji

August 24, 2026
An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki
Ranar Murna

An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki

August 23, 2026
Yadda marubuciya Aunty Baby ta yi bikin cikar shekara 51
Ranar Murna

Yadda marubuciya Aunty Baby ta yi bikin cikar shekara 51

August 19, 2026
Next Post
Gwamnatin Tinubu za ta cusa son ƙasa a zukatan al’umma domin a yaƙi ta’addanci da hare-haren ‘yan bindiga – Minista

Gwamnatin Tinubu za ta cusa son ƙasa a zukatan al'umma domin a yaƙi ta'addanci da hare-haren 'yan bindiga – Minista

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!