GWAMNATIN Jihar Zamfara ta fito da sababbin hujjoji na yadda tsohuwar gwamnatin Bello Matawalle ta yi sama-da-faɗi da kuɗin aikin filin jirgin sama.
A Juma’ar da ta gabata ne Matawalle ya musanta zargin sace biliyoyin kuɗi da sunan aikin jirgin saman.
A wata sanarwar manema labarai, wadda Kakakin gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a shafin sa na Facebook a ranar Litinin a Gusau, ta ce musanta wannan batu ba komai ba ne face rashin kunya da kuma kira wa kai fallasa.
Ya ƙara da cewa idan ma dai ban da Matawalle na ƙoƙarin wawantar da mutane, ya manta yadda a ranar 25 ga Oktoba, 2021 ya kira waya ya bada umurni aka fitar da naira biliyan 1 daga asusun Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi, wanda a ciki ne aka tura wa ɗan kwangilar aikin filin jirgin sama naira miliyan 825.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Gwamnatin Jihar Zamfara ba ta yi niyyar tanka wa mutumin da ake zargi da satar dukiyar al’umma ba. Sai dai kawai don a fayyace tsakanin gaskiya da ƙarya, musamman ma ganin cewa ya fito ya musanta zargin da ake yi masa.
“Babu makawa, satar rashin imanin da aka tafka da sunan samar da tashar jirgin sama a Zamfara ba komai ba ne idan ka kwatanta shi da irin manyan sace-sacen da tsohuwar gwamnatin Bello Matawalle ta yi.
“Tsabar ƙarya ne a ce wai kuɗin da ‘yan kwangila su ka gabatar da farko ya kai biliyan 28, amma tsohuwar gwamnatin ta zaftare shi zuwa biliyan 11. Babu wani ɗan kwangila da zai aminta a zaftare masa kuɗin aiki da kaso 61% ba tare da asalin aikin ya taɓu ba. Wannan ya sa shakku a asalin aikin tun farko. Ko ba komai Matawalle ya fallasa mana nagartar ɗan kwangilar da su ka kawo.
“Matawalle, ya yi iƙirarin cewa aikin na tashar jirgin sama wai an fara shi ne kan tsarin tallafin banki na ‘Contract Financing’. Wannan abin kunya har ina? Tsarin tallafin kuɗi da banki ke ba ɗan kwangila sunan sa ‘Contract Financing Facility’, shi kuma ana ƙulla shi ne tsakanin ɗan kwangila da banki, babu ruwan gwamnati a ciki. Don haka tsagoron ƙarya ce.
“Sannan batun wai kuɗaɗen da aka biya ɗan kwangilar an yi su bisa sahalewar Ma’aikatar Ayyuka, shi ma ƙarya ne. Hujjojin da mu ke da su, kuma waɗanda mu ka saki a yau, sun tabbatar da an biya kuɗin ne ba tare da bin duk wata ƙa’ida ba.
“Ko don tarihi, ya na da kyau a sani cewa an biya ‘yan kwangilar kaso 30% na aikin a matsayin biyan farko, inda aka ba su naira 3,465,569,736.90, wato naira biliyan 3.46, daga asusun Ma’aikatar Kuɗi ta Jiha, a ranar 19 ga Yuni, 2020.
“A matsayin biya na biyu, an sake tura masu naira biliyan 2, 310, 379, 824.60 daga asusun Ma’aikatar Kuɗin Jiha, a ranar 19 ga Yuni, da sunan bashi (wanda babu wannan tsarin sam a ƙa’idar gudanarwa ta gwamnati).
“An sake tura masu naira miliyan 825 daga asusun Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi a ranar 25 ga Oktoba, 2021 a matsayin biya na uku.
“Haka kuma batun da Matawalle ya yi na cewa ɗan kwangilar ya kammala wasu ayyukan da su ka haɗa da hanyar tafiyar jirgi, magudanan ruwa, babbar ƙofar shiga filin jirgin duk ƙarya ce. Shi ma akwai hotunan mun sake su.
“Iƙirarin wai an kammala wasu daga cikin ayyukan da kaso 50% zuwa 100% ma ƙarya ce. Ai filin jirgin na nan, duk wanda ke son gani da idon sa ya na iya zuwa don ganin irin ɓarnar da Matawalle ya yi.
“Hujjojin da mu ke da su sun tabbatar da cewa Hukumomin Kula da Filayen Jiragen Sama na Tarayya, irin su NCAA da NAMA, duk ba a shigar da su cikin lamarin ba a farko, wanda ya saɓa da ƙa’idar gudanarwa ta sashen sufurin jiragen sama.
“Da a ce da gaske tsohuwar gwamnatin Matawalle ta ke, da tun a wurin fitar da tsarin aikin filin jirgin saman za su nemi sahalewar waɗannan hukumomi.

“Mu na so Matawalle ya yi wa duniya bayanin dalilin da ya sa ya biya ɗan kwangila zunzurutun kuɗi har naira biliyan 6.78 kan aikin da su kan su sun tabbatar da cewa iyakar sa kaso 30%. Wanda kuma yanzu aka yi watsi da shi.
“Gwamnatin Dauda Lawal ba shaci-faɗi ta ke fitarwa ba, hujjoji ne waɗanda kowannen su ke da takarda.
“Kwamitin Amsar Mulki ya yi dogon nazari kan hulɗoɗin gwamnati, wanda rahoton wannan kwamiti na da matuƙar tada hankali.
“Da sannu za mu fitar wa da al’umma irin satar rashin imanin da Matawalle ya jagoranta a tsohuwar gwamnatin sa. Kuma babu ko tantama cewa duk waɗanda ke da hannu a irin waɗannan ayyuka na almundahana da babakere ba za su sha ba. Wannan ba komai ba ne daga cikin abubuwan takaicin da za mu fallasa wanda tsohuwar gwamnatin ta aikata.”