A SAFIYAR shekaranjiya Talata, Allah ya azurta sanannen mawaƙi a Kannywood kuma ɗan jarida, Alhaji Abubakar Yarima, da ɗa namiji.
Maiɗakin sa, Malama Safina Muhammad Rabi’u, wadda ita ce matar sa ta biyu, ta haihu da misalin ƙarfe 10:00 na safe a asibitin Mu’awiyya da ke Tudun Nufawa, Kaduna.
Abubakar Yarima ya raɗa wa jaririn suna Muhammad Sani.
Mawaƙin ya shaida wa mujallar Fim cewa yanzu ‘ya’yan sa 14.
Haka kuma ya ce ya maida sunan ɗan sa ne da ya rasu a ruwa shekara uku da suka wuce.
