• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Harkar Fim: Na Gano Hanya Mai Bullewa – Tijjani Shehu Yahaya

by DAGA ISAH BAWA DORO
March 26, 2018
in Tattaunawa
0
Harkar Fim: Na Gano Hanya Mai Bullewa – Tijjani Shehu Yahaya
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

TIJJANI Shehu Yahayya ya na daya daga cikin furodusoshi da daraktocin da ke cin karen su ba babbaka a Kannywood. Kasancewar sa mai ilimi kuma masani a harkokin finafinan Hausa, ya yi karatuttuka wadanda su ka shafi shirin fim a kasashe irin su Ingila da Amerika. 

Tijjani shi ne mai shirya shirin nan mai yanka-yanka (series) mai suna ‘Yaki Da Zuciya’ wanda ake nunawa a tashoshin satalayit na Hausa. Bugu da kari, ya na daya daga cikin malaman da ke koyarwa a makarantar koyon fim ta Kano, wato Kano Film Academy. Mun tattauna da shi game da harkokin sa finafinan Hausa:



FIM: Ka gabatar da kan ka ga masu karatu.

 

TIJJANI: Suna na Tijjani Shehu Yahaya. Ni dai an haife ni a garin Kano, a unguwar Dakata. Na yi karatu na na firamare a Brigade, na yi makarantar Science Secondary School a Dawakin Kudu; na yi karatun NCE a Sa’adatu Rimi College of Education. Bayan na gama, sai na tafi Bayero University, a can na yi karatun digiri. 

Bayan na gama NCE, kafin na shiga jami’a, tun a lokacin na fara kasuwanci. Mun bude wani shagon buga sidi, daga nan mu ka fara editin. Da tafiya ta yi tafiya, sai mu ka shirya finafinai a karkashin mu wanda mu ka bude ni da yaya na, mai suna Crystal Player Multimedia, akalla yanzu an kai shekara goma sha bakwai.

FIM: Ya aka yi ka fara shirya fim din ka mai yanka-yanka (series), wato ‘Yaki da Zuciya’?

TIJJANI: Gaskiya sai da na yi tunani sosai. Na zauna da mutane irin su Mustapha Musty, Jazuli Garko, Ahmad Bifa, da sauran su. Na ke ce masu a yadda na ga duniya ta canza, idan ka yi fim abu daya ne, sannan abu ne wanda ya ke wucewa, me zan yi tunani kamar yadda na koyo a kasar waje sun nuna min ka yi abin da shekara 10 zuwa 20 ba za a manta da shi ba. Sai na samu wani ma’aikacin gidan TV na ce masa ina so in yi abin da zan dade ina yi. Mu ka yi shawara har ya ba ni misali, ya ke cewa yanzu idan ka duba Super Story tun mu na yara ake yin shi, ga shi har yanzu ana yi, kuma bai kare ba. Ya kara ba ni misali da irin su Danmagori, Danhaki, dukkan su shirye-shirye ne na Hausa kuma idan yanzu aka dawo ci gaba da yin su ba za su kare ba. Menene sirrin? Shi ne ni ma na yi tunanin fara wani series din mai suna ‘Yaki da Zuciya’.

FIM: Yaushe ka fara shirya shi?

TIJJANI: Gaba daya bai fi shekara biyu ba. Yanzu haka ina da episode 65.

FIM: Su wanene jaruman  shirin?

TIJJANI: Akwai wadanda su ke tsofaffin ’yan fim ne, irin su Mustapha Musty, Masa’uda ’Yar’agadas, Jamilu Yakasai, da sauran su. Shi shirin minti sha-biyar ne. Ina yin shi daki-daki; za ka ga jarumi idan ya fito a episode na farko ba za ka gan shi a na biyu ba, saboda labari ne na dauka a kan yadda rayuwar mutane ta ke, shi ne ake kira da social life.  Kusan duk labaran inda ka kalla ya na koya darasi ne ga rayuwar al’umma.

FIM: Me ya sa ka tsaya ga wannan shirin shi kadai, ba ka shirya finafinai?

TIJJANI: Gaskiya harkar fim din ce lokacin da na zo ta tabarbare, kuma lokaci ne ya zo. Ba wai rashin kasuwa ba ne ko ’yan kallo, zamani ne ya zo. Idan ka duba, a da kowa da dibidi ya ke kallo, yanzu kuwa idan za ka aje ka samu mai shirya fim cikin mutum dari ka ce masa akwai dibidi a gidan ka za ka ga shi ya ke shiryawa amma bai da ita. To ya za ka yi wa dan kallo shi kuma ya saya, wanda kai kan ka ba ka da ita? Me ya kawo wannan? Zamani ne! Ga ’yan download da masu yanar gizo sun zo. Yau za ka saki fim a garin nan, sai ka ga mutum daga Germany ya kira ka ya na “Fim din ka ya yi kyau!” Kai kuma ka na Kofar Wambai ka na hada-hadar kasuwanci; murna za ka yi ko bakin ciki? Bakin ciki za ka yi saboda ba saye ya yi ba; wani ne zai sayi faifai daya, kafin minti talatin ya baza shi a duniya. Ba ka saida kwafi dari ba amma sama da mutum dubu dari ya kalla. Ina riba ta ke?

FIM: Idan na fahimce ka, satar fasaha da tabarbarewar kasuwanci su ne su ka hana ka shirya fim.

TIJJANI: Gaskiya su ne. Amma yanzu akwai wani kwas da na je na yi a Ingila, kwanan nan na je a wata jami’a. To, ni ma yanzu ina shirin fara finafinai saboda na samo ilimin yadda ake raba shi a yanar gizo da kuma sinimomi da gidajen talbijin na yanar gizo wanda za su rika nuna shi yanka-yanka kuma su biya ka. Duk irin wadannan matsalolin su su ka sanya ni na je wannan karatun a Ingila wanda na samu hanyoyi da na san cewa za su bulle mana, ba ma ni kadai ba har da sauran mutanen da su ke harkar. 

Bari ka ji in ba ka misali. Abin da aka koya min a makaranta a kwas din da na yi, Digital Film and Distribution. Sai na nemi mai raba fim a kasar France. Ka ga France ba Turanci su ke ba, kuma ba Hausa ake yi ba, amma mai raba fim din nan sai ka ga zai iya raba abin da aka yi da Hausa, amma kai a tunanin ka ya zai yi? Abin da ya ke so, kafin ka tura masa shi ka yi masa subtitle din sa da Turanci. Idan ka yi subtitle mai kyau za su zauna su kalla, idan su ka kalla, su da kan su za su canza murya za ka ga ta koma ta Faransa, amma kuma hoton namu ne na nan. Wanda ya ke a Faransa zai kalli fim din har ya ji dadin ya kalli wani abu sabo da bai saba gani ba. Idan ka na da labari mai kyau duk duniya babu inda ba za a kalle ka ba. To ka ga wata sabuwar hanya ce wadda ba mu sani ba. Wannan abin shi ya tsoratar da mu har sai da na fita na samu wannan ilimin, yanzu kuma zan fara.

FIM: Kasancewar ka wanda ya ke da ilimi mai zurfi kuma ya yi karatu a wasu bangaren na harkar fim, ko akwai wani kokari da ka ke yi ko kuma ka ke shirin yi don amfanar da sauran ’yan’uwan ka wadanda ba su yi karatun ba domin amfanar da su?

TIJJANI: Babban kokarin da na yi na farko shi ne alhamdu lillahi yanzu akwai makaranta da aka bude ta koyon fim wadda ake kira da Kano Film Academy wadda ta ke karkashin Northwest University, Kano. To, ina daya daga cikin malaman makarantar, kuma da su ka neme mu sun fadi abubuwan da su ke so wanda sai mai karatu matakin digiri. Ni da man na je na yi kwas a kan fim din. Ina zuwa na yi masu magana sai su ka ce da man irin mu su ke nema, wanda mu biyu ne a wannan masana’antar, daga ni sai Ishaq Sidi Ishaq mu ke wannna koyarwar. To da na zo makarantar abin da su ka fara kallo na da shi shi ne na fi kusanci da harkar kasuwancin fim din; shi ne su ka ce to akwai wani kwas da man sunan shi Business of Filmmaking; hanya ce ta cinikayyar sabbin finafinai da su ke duniya. A kan shi ake so ka koya. Su ka ce babu wanda ya dace da wannan koyarwar sai ni, kuma su ka ba ni damar koyar da shi, wanda akalla mu na da dalibai 65 kuma ’yan Kannywood ne. Da yawa sun ga amfanin hakan, su na so su shigo makarantar.

FIM: Me ka ka ganin ya hana wasu ’yan fim shigowa makarantar? Mun ga kamar ku na da karancin dalibai.

TIJJANI: Yanzu fa aka fara, kuma ita kan ta makarantar ba wai ta bunkasa ba ne. Yanzu ta fara, kamar yadda na fadi maka. Mutane da yawa yanzu su na so su zo, saboda ka san yadda karatu ya ke a Arewa; wani za ka ga cewa ya san amfanin shi amma fa ba lallai ne ya kalli wurin ya je ba, kuma sana’ar sa ce. 

Babban abin da ya hana wasu shiga, wasu sun yi korafi a kan cewa kudin rijista ya yi yawa, wanda kuma ko’ina haka abin ya ke; yawancin dalibai za ka ga su na kuka da kudin makaranta. Sai dai mu abin da mu ke nuna masu, idan ka kwatanta wasu wuraren da ake karatu makamancin irin haka ba za su iya ba saboda tsadar sa.

FIM: Ya ka ke kallon yadda ake gudanar da harkar fim a Kannywood a yanzu, kasancewar ka wanda ya yi karatun fim a wasu kasashen?

TIJJANI: Ina kallon ta a kan abu daya ne. Gaskiya sai mutum ya tsaya ya yi dogon tunani ya yi amfani da ilimin sa, kuma harka ce wadda ba ta mutum daya ba. Ni har yanzu abin da na ke kokari shi ne na ga mun hada kan mu. Yanzu misali idan ina so na yi fim wanda ba a Najeriya kawai na ke so a kalla ba, duniya na ke so ta kalla, to ya zamana cewa akwai dama wadda za mu iya zama da kan mu an tabbatar da wanda ya yi abin ya yi mai inganci, sannan yawancin wadanda su ke harkar fim babu kudi a hannun su.

FIM: Wadanne hanyoyi ka ke ganin za a bi Kannywood ta ci gaba?

TIJJANI: Hanya ta farko, komai da ka ke gani ana yi a duniya akwai wanda ya fi ka sani. Babbar matsalar mu shi ne kasuwanci. Akwai distribution companies a duniya, sai ka neme su; su kuma aikin su kenan. Idan ka yi masu magana su kuma za su ba ka shawara ga abin da za ka yi ka sayar da fim din ka. To har yanzu masana’antar fim ba mu bi mu ga yadda duniya ta ke yi ba. Babbar matsalar mu kenan.

FIM: Wadanne nasarori ka samu ta fannin harkokin ka na finafinai?

TIJJANI: Nasara ta farko da zan fara magana ita ce a wannan shekarar ta 2017 na samu awards guda biyu. Ta farko African Magic (ANVCA), na samu Best TV Series da fim di na ‘Yaki Da Zuciya’. Sannan na kara samun award da  fim din a gasar AMMA Award, Best Series Film.

FIM: Amma wasu sun ce award din da ka samu a Legas (African Magic ANVCA) sayen ta ka yi. Ya abin ya ke?

TIJJANI: To, idan mutum ya ce ka sayi award a Legas ai shi ma sai ya je ya saya! Tunda abu ne wanda ba a titi ake shirya shi ba, masana aka tara su ka zabe mu, sannan an yi zaben ne ta hanyar intanet. Duk wanda ka ji ya na fadin haka, ya shiga ne bai samu ba. Kuma ka san halin mutanen mu! Idan har zan iya sayen award ai akwai wadanda su ka fi ni a industiri, me ya sa su ba su je sun saya ba? Kuma sun shiga.

FIM: Kai dan wace kungiya ce a Kannywood?

TIJJANI: Ina kungiyoyi da yawa. Ni ne mataimakin shugaban furodusoshi na KPA (Kannywood Producers Association). Ina kuma Kungiyar Daraktoci da Editoci, sannan ni memba ne a kungiyar Arewa Filmmakers. Wadannan kungiyoyin su na ke yi.

FIM: Menene burin ka a harkar fim?

TIJJANI: Ni buri na a harkar fim ba wani abu ba ne illa na ga cewa mun samu ci-gaba. Na biyu, na ga mun samu damar da za mu kai wani babban matsayi a duniyar finafinai.

Loading

Tags: Harkar Fim: Na Gano Hanya Mai Bullewa
Previous Post

Yanzu mawaka mun saki al’adun mu – Maryam Fantimoti

Next Post

Shekaru 19 da kafuwar mujallar Fim: Jajircewa ce ta kawo mu yau

Related Posts

MOPPAN: Za mu haɗa kai da ‘yan siyasa don kawo cigaban Kannywood – Shehu Hassan Kano
Tattaunawa

MOPPAN: Za mu haɗa kai da ‘yan siyasa don kawo cigaban Kannywood – Shehu Hassan Kano

June 30, 2025
Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 
Tattaunawa

Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 

March 1, 2025
Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah
Tattaunawa

Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah

November 13, 2024
Bikin auren ‘ya’ya na ya ɗaga daraja ta – Aminu Ala
Tattaunawa

Bikin auren ‘ya’ya na ya ɗaga daraja ta – Aminu Ala

August 2, 2024
Buri na in samar wa MOPPAN tsarin shugabancin da za a riƙa tunawa da ni – Habibu Barde
Tattaunawa

Buri na in samar wa MOPPAN tsarin shugabancin da za a riƙa tunawa da ni – Habibu Barde

March 13, 2024
Mahaifiyar Afakallahu ta kwanta dama
Tattaunawa

Afakallahu: Abin da mahaifiyar mu ta karantar da mu

March 11, 2024
Next Post

Shekaru 19 da kafuwar mujallar Fim: Jajircewa ce ta kawo mu yau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!