*BABU DARAKTAN DA YA DAƊE YA NA CIN DUNIYAR SA DA TSINKE, TARE DA NUNA ƘWAREWA DA JAJIRCEWA A AIKI, KAMAR HASSAN GIGGS. MENENE SIRRIN NASARAR SA, KUMA WANE BURI YA KE SON CIMMAWA A NAN GABA?
GA duk wanda ya san yadda harkar fim ta ke tafiya, ya kwana da sanin cewa harka ce mai wuyar sha’ani wadda yau idan ta ɗaga ka, ana maka kirarin sai kai, to jibi sai a neme ka a rasa. Wani idan harkar ta yi wurgi da shi sai ka ji kamar ma ba a taɓa yin sa ba. Kaɗan ne daga cikin masu sana’ar su ke da nasibin da ya sa aka daɗe ana damawa da su.
Hassan Giggs ya na ɗaya daga cikin waɗanda su ka daɗe ana damawa da su tsawon shekaru, musamman a fagen aikin sa na bada umarni da kuma ɗaukar hoto. Domin jin sirrin nasarar sa, mujallar Fim ta yi hira ta musamman da shi.
FIM: Ka na daga cikin waɗanda su ka daɗe su na gudanar da harkar fim, kuma har yanzu ana damawa da kai, amma har yanzu wasu ba su san waye darakta Hassan Giggs ba.
HASSAN GIGGS: To assalamu alaikum. Da farko dai babu abin da zan ce sai dai godiya ga Allah, domin ni dai Hassan Giggs na shigo harkar fim tun ina tace hoto a 1995 a nan wani situdiyo da ke Zoo Road. Lokacin su marigayi Musa Jalingo su na zuwa daga Jalingo ni na ke tace masu fim da kuma manyan mutane. Na yi aikin finafinai da dama; a lokacin ba mu da kwamfuta da bidiyo. Mu ke haɗa hoton. Idan ka yi aikin sa’a guda a lokacin sai a ba ka N150. To haka dai na ke yi, har daga baya na yi karatu a kan ɗaukar hoto. Da man kafin na shigo harkar fim ina ɗaukar hoton. To da na je na yi karatun sai abin ya ƙara min ƙarfin gwiwa.
FIM: To kai da ka fara da ɗaukar hoto, ya aka yi ka rikiɗe ka zama mai bada umarni?
HASSAN GIGGS: To gaskiya lokacin da na zo na yi wasu finafinai da dama har wasu su ke ganin ni ba ɗan Kano ba ne, daga Jos na zo, har ma ake ganin na zo da wani salo wanda a lokacin shi ake yayi a fim, kuma ake ganin ni kaɗai na iya. Amma na san ba yi na ba ne, yin Allah ne. To hakan ya sa mutane su ka ba ni shawarar me ya sa ba zan fara yin daraktin ba, kuma wanda ya fi ba ni wannan shawarar shi ne Ali Nuhu. To shi ne na fara bada umarni a wani fim ɗi na mai suna ‘Alkuki’. To tun daga nan na fara, kuma har yanzu ina bada umarni, ina kuma ɗaukar hoto.

FIM: Tsawon lokacin da aka ɗauka ka na bada umarni da kuma ɗaukar hoto ka samu darasi da dama. Ya za ka kwatanta irin yadda abubuwa su ke gudana tsawon wannan lokacin?
HASSAN GIGGS: To da farko dai darakta mutum ne wanda ya ke son ya yi duk wani abu idan aka kawo masa labari sai ya duba ya ga yadda zai tsara labarin yadda zai gamsar da ɗan kallo. Don haka shi darakta mai isar da saƙo ne ga jama’a, kullum ana so darakta ya zamo mai ƙirƙirar sabon abu yadda zai burge ɗan kallo. To ni ina cikin mutanen da su ke ƙirƙiro abu wanda sai dai a ɗauka a waje na.
FIM: To amma kasancewar darakta shi ne jagora a fim, sai kuma a fim ɗin Hausa ake samun katsalandan daga furodusa, wani lokaci ma har da wanda ya ke zuwa kallon lokeshin, ka ji shi ma ya na cewa ga yadda ya kamata a yi.
HASSAN GIGGS: E haka ne, ana samun rashin fahimta tsakanin furodusa da darakta, amma duk daraktan da ya san abin da ya ke yi ya san shi furodusa shi ya ke kiran darakta. Idan aka zo yadda za a tsara fim sai an zauna an tattauna yadda fim ɗin zai tafi, amma yawanci ba ma yi, wanda kuma a nan ake tsarawa da duba daraktan da ya dace ga fim ɗin, don kowanne darakta akwai inda ya ƙware a bada umarni – ko na ban dariya ne ko na santimental ne, da sauran su. Sai furodusa ya tsara da kuma samo daraktan da zai gudanar da aikin.
Sannan furodusa ya isa ya kori darakta idan bai ba shi abin da ya ke so ba, amma kuma idan aka zo lokeshin darakta gaba ya ke da furodusa domin a lokacin shi ne komai ya rataya a kan sa. Idan ba a samu yadda ake so ba darakta ne ya ke da laifi. Don haka da furodusa da darakta dole ne su fahimci junan su tun kafin a zo lokeshin.
FIM: Ya ka ke ganin yadda ake samun rashin fahimtar juna tsakanin darakta da ɗan wasa?
HASSAN GIGGS: Ni dai ba na samun matsala, domin duk lokacin da zan yi aiki da jarumi na kan zauna da shi na yi masa bayani kan yadda na ke son ya yi a fim. Ka ga kamar fim ɗin ‘Hindu’, sai da mu ka zauna da Adamu (A. Zango) na yi masa bayani. Ka ga yadda na canza masa kamanni. Haka ma a fim ɗin ‘Saki Kowa’, yadda na canza shi ya rinƙa zubar da yau, to duk mu na zama mu tsara ne. Don haka ni dai ba na samun matsala.
FIM: Yanayin aikin ka ya sa ake yi maka kallon wanda ba ya yin ƙyashi ga abokan sana’ar sa har ma mutane da dama sun koyi aiki a wajen ka.
HASSAN GIGGS: To ni gaskiya babu abin da ba na so a duniya kamar na ga ana yi wa wani baƙin ciki, ko a rinƙa yi masa gori. Don haka na koya wa mutane da yawa harkar nan, kamar ɗaukar hoto, tace murya, bada umarni, ina da su da yawa a cikin harkar nan, waɗanda ni na koya masu. Ga shi yau sun dogara da kan su, su na cin abinci. Don haka ba na so na ga ranar da zan yi wa wani baƙin ciki a kan harkar rayuwa, don ba ya cikin tsari na.
FIM: Idan mu ka dubi wani fim da ka bada umarni, wato ‘Saki Kowa’, daga shekarar da ta wuce zuwa wadda mu ke ciki shi ne fim ɗin da ya fi kowane samun lambar yabo. Ko menene sirrin nasarar?
HASSAN GIGGS: E, sirrin nasarar daga Allah ne saboda na ce ‘Saki kowa ka kama Allah’. Kuma duk fim ɗi na idan ka gan shi ina ambato wani abu da zai faranta wa mutum rai. Na yi ‘Gabas’, na yi ‘Tashi’, na yi ‘Sama’, na yi ‘Wani Hani Ga Allah’, sannan na zo na yi ‘Saki Kowa Ka Kama Allah’. To dogaro da Allah da na yi shi ne ya zama sirri na.
Kuma yabon da na samu a fim ɗin ba ni kaɗai ba ne, da furodusa da jarumai da duk wanda ya yi tarayya a cikin fim ɗin ya samu yabo. Nasarar kuma uwa-uba masana’antar finafinan Hausa ita ma ta samu nasara, domin idan ban yi nasara ba to duk waɗanda su ka yi tarayya a harkar su ma ba za su yi ba.

FIM: A harkar fim za ka iya tuna wani abin alheri da ka samu wanda ba za ka manta da shi ba?
HASSAN GIGGS: E, gaskiya alherin da na samu wanda ba zan manta da shi ba shi ne aure na da mata ta shekaru bakwai kenan mu na zaune lafiya duk da ana cewa ’yan fim ba sa zaman aure. Yau ga ni da mata ta Muhibbat, wadda jarumar fim ce, mu na tare a zaman miji da mata, ta na faranta min ina faranta mata. To wannan abin alfahari ne a gare ni da ba zan manta da shi ba.
Don haka ina kira ga masoyan mu su taya mu da addu’a ta fatan alheri da mata ta. Ba wai ba ma samun matsala da ita ba ne; duk auren da aka ce ba a samun matsala to ƙarya ne, amma idan mu ka samu matsala a gida mu ke zama ni da ita mu warware matsalar mu. Don haka tsawon zaman mu da ita ba ta taɓa yin yaji ta tafi gidan su ba.
FIM: Menene saƙon ka na ƙarshe?
HASSAN GIGGS: Saƙo na dai shi ne masoya su taya mu da addu’a. Ni Hassan Giggs, daraktan nan da ya saki kowa ya kama Allah, ya na neman addu’a a gare ku. Na gode.