• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, June 6, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Hausawa Ko Turawa?

by DAGA DAKTA MARYAM ALI ALI
July 26, 2021
in Tsokaci
1
Hausawa Ko Turawa?
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

DUBI waɗannan hotunan. Yanzu saboda Allah waɗannan ‘yanmatan sun yi kama da mawaƙan Hausa!? 

Ko dai su mawaƙan da daraktocin da su ke bai wa waɗannan ‘yanmatan irin waɗannan suturun da sunan waƙar Hausa ba su da mafaɗa ne? Ko dai su na da wata manufa ne? 

Abu wasa wasa sai daɗa haɓaka ya ke. In su na son su waƙoƙin Turanci, su nemo Turawa su yi musu rawa; ba wanda ya ce kar su yi, amma akwai wulaƙanci da rainin hankali a cusa yarinya a cikin tsukakkun kaya a sa ta rawa da su, wai kuma waƙar Hausa, kowa kuma ya zuba ido ya na kallo. 

A duk lokacin fa da mutum ya rasa al’adar sa, to ya rasa ta, an gama cin sa da yaƙi, ya zama hoto. 

Ya kamata waɗannan mawaƙa su yi wa kan su faɗa. Ba abin da zai hana su bai wa waɗannan ‘yanmatan kayan Hausawa su sa in ya zama dole sai sun yi rawa da waƙa da su. 

Ba wani burgewa ba ne a sa kayan Turawa. Mayar da kai baya ne. Saboda ko Turai ka je da kayan ka na gida sai ka fi burge su, sai ka ga su na tsayawa su na ma magana. Amma ka sa nasu ko kallo ba ka ishe su ba. 

Shi ya sa da na ga su Rahama Sadau wai an je Amerika an sa ƙananan kaya har da ƙona gashi na ce kash!, waɗannan sun kwafsa. Allah Ya kyauta.

Dakta Maryam Ali Ali malama ce a Sa’adatu Rimi College of Education, Kumbotso, Kano

Loading

Tags: Ali NuhuHamisu Breaker Dorayihausa filmsHausa musicKannywoodKhairat Abdullahimawakan hausaRahama SadauSunusi Oscar442
Previous Post

Tsakani na da Afakallah da kuma Momee Gombe – Sunusi Oscar442

Next Post

Sai da aka biya N5m kafin ‘yan bindiga su sako ni – furodusa Ali Bulala Gusau

Related Posts

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?
Tsokaci

Aure Da Saki A Fim: Gangan Ko Gaske?

March 7, 2025
‘Arewa Republic’. Kun gani ba?
Tsokaci

‘Arewa Republic’. Kun gani ba?

February 10, 2025
Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa
Tsokaci

Rukuni huɗu na masu kallon fim ɗin Hausa

February 7, 2025
Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na
Tsokaci

Barka Da Zagayowar Ranar Haihuwar Ka Miji Na

September 1, 2024
Dakta Aliyu U. Tilde
Tsokaci

Arewa: Tsakanin Ilimi Da Sana’a

June 12, 2024
Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida)
Tsokaci

Shawara ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

June 10, 2024
Next Post
Sai da aka biya N5m kafin ‘yan bindiga su sako ni – furodusa Ali Bulala Gusau

Sai da aka biya N5m kafin 'yan bindiga su sako ni - furodusa Ali Bulala Gusau

Comments 1

  1. Jamila Adamu Yaro says:
    4 years ago

    Allah sarki Dr Maryam ai sai dai ire iren mu muyi ta sharhi amma ba abun da zai canja,ai babban laifin duk na hukuma ne, in duniya da gaskiya su directors da producers su saka kannen su mata mana a roll din, amma dayake kudi suke nema, su kuma ‘yan matan duniya na rudunsu ga mafiya yawansu ba tarbiya daga ganin su fitsara ta mamaye su tun daga gidan da suka fito, illah akwai lokacin da ba za ayi ba. Yanzu ai yayin album ne yazo saboda ba rawan da wakan a finafinai, shiyasa kasuwan su yake ci. Yau ina ‘yan copyn Indian film sun gama kasuwan su, ba don sun so ba sai don zamani yazo mana da drama series, a shekarun baya da Rabiu Bebeji Allah jikan sa da Prof. Abdallah Uba suke sharhi kan illar copyn India a mayar dashi Hausa films, ai producer’s din cewa suka yi hassada ake musu don an ga suna samun kasuwa(to yau su samu, aiga ‘yar manuniya ta nuna).Ina jinjina wa uban tafiya Malam Sheme, da producers Ahmad Bifa da shirin sa na ZAMAN AURE,Falalu Dorayi da shirin sa na GIDAN BADAMASI, Aminu Saira, Nazir Sarkin Waka, Nazifi Asnanic da shirin su na LABARINA,Ibrahim Birniwa da shirin sa na SIRRIN BOYE, sai Lawan Ahmad da Nura Mustapha Waye da shirin su na IZZAR SO. Allah qara daukaka da basira

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!