A YAU ne auren fitacciyar mawaƙiya a Kannywood, Hajiya Maryam A. Baba (Sangandale) da matashin mawaƙi Abdul Kafinol ya cika shekara biyu.
Don nuna murnar zagayowar wannan rana, Maryam ta wallafa wasu kyawawan hotuna guda uku na ita da mijin nata a Instagram.

A ƙasan hotunan, ta yi addu’a mai jan hankali kamar haka: “Shekara biyu yanzu wai! Ikon Allah, 25/82019 – 25/8/2021. Masha Allah! Allah ka ƙara lafiya da arziki da wadata da sutura. Ubangiji ya ƙara bada zaman lafiya a gidan auren mu.”

Ɗimbin masoya sun taya matasan ma’auratan murna tare da addu’ar Allah ya ƙaro ƙauna da ƙaruwa a tsakanin su.
Mu ma a mujallar Fim mun ce amin, tare da fatan Allah ya kawo ƙazantar ɗaki.