A JIYA aka fara ruguntsumin bikin auren jarumar Kannywood, Halima Yusuf Atete, a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Kamar yadda mujallar Fim ta ba ku labari, za a ɗaura auren Halima ne da sahibin ta Mohammed Mohammed Kala a jibi Asabar, 26 ga Nuwamba, 2022 da safe a masallacin Juma’a da ke Abuja Sheraton Bus Stop a Maiduguri.

Shagulgulan bikin sun haɗa da ƙwallon ƙafa a ranar Laraba; Ranar Margi (Margi Day) da rana a yau Alhamis; Daren Larabawa (Arabian Night), da daren gobe Juma’a, dina bayan ɗaurin aure a ranar Asabar, sai kai amarya ɗakin mijin ta a ranar Asabar ɗin.
Jiya aka sa amarya a lalle, aka fara ruguntsumin bikin.
A nan, za a iya ganin hotunan fara bikin waɗanda mujallar Fim ta samu.

