• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, August 7, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Sheikh Zakzaky ya ba ni saƙo ga ‘yan Kannywood – Ali Artwork

by DAGA ABBA MUHAMMAD
November 24, 2022
in Labarai
0
Sheikh Ibrahim Zakzaky tare da su Ali Artwork

Sheikh Ibrahim Zakzaky tare da su Ali Artwork

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMIN barkwanci a Kannywood, Aliyu Muhammad Idris, wanda aka fi sani da Ali Artwork ko kuma Maɗagwal, ya bayyana cewa akwai muhimmin saƙo da jagoran Shi’a a Nijeriya, Sheikh Ibrahim Yakub El-Zakzaky, ya ba shi domin ya isar ga ‘yan fim ɗin Hausa.

Amma ya ƙaryata masu cewa ya zama ɗan Shi’a, wai don haka ne ma ya kai ziyara ga shahararren malamin a gidan sa da ke Abuja.

Da ya ke zantawa da mujallar Fim, Ali Artwork ya ce, “Masu yaɗa cewa wai na karɓi Shi’a ƙarya su ke yi. Duk wanda ya san ni, ya san cewa a kowace ɗariƙa ina da mutane. Da ma na saba ziyartar malamai tun ba yanzu ba, irin malaman Izala, Tijjaniyya, Ƙadiriyya da duk wani malami, duba da yanayin sana’a ta na nishaɗantarwa, kowane ɓangare na al’umma su na ji, kuma su na kallo. 

“Sannan a dukkan mutane su na so kuma su na sha’awar abin da na ke yi. Kuma su kan su su na so in zo mu ƙulla mu’amala ko na kasuwanci ko kuma wani abu mai kyau haka. Don haka zuwa na ba wani sabon abu ba ne.”

Maɗagwal ya yi nuni da cewa shi mutum ne wanda ke kai wa malamai na bangarori daban-daban ziyara.

Ali Artwork ya na yi wa Sheikh Zakzaky bayani

Ya ce: “A baya na ziyarci Sheikh Ahmad Gumi, duk da mun je ɗaukar hira da shi ne a kan abin da ya shafi harkar zakka da waƙafi. 

“Sannan na ziyarci ɗan Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, mun yi maganganu da shi. 

“Haka shi ma Sheikh El-Zakzaky mun ziyarce shi ne don mu sada zumunci, kuma mu yi masa jajen abin da ya faru da shi, da sauran su. Wannan shi ne.”

Ali ya ci gaba da cewa, “A cikin mutanen sa akwai masoya na, kuma su na kallon abin da na ke yi na nishaɗi da sauran su. Waɗannan su ne maƙasudin zuwan namu.”

A kan yadda ganawar tasu ta kasance, jarumin ya ce: “Mun ji daɗin tattaunawa da Malam. Ya sanar da mu wasu abubuwa na rayuwa waɗanda ba mu sani ba. Haka kuma ya ba mu shawarwari a kan sana’ar mu da kuma yadda mutane su ke kallon mu a matsayin waɗanda su ke ɓata tarbiyya.

“Malam ya ce gaskiya wannan abu ne wanda bai kamata ba, wannan harka ce da za a iya amfani da ita wurin tura saƙo, mu yi abu mai kyau, kada mu yi abin da zai taɓa ƙima da mutuncin addinin mu, mu rinƙa nuna wa mutane yadda za su yi rayuwa mai kyau, in kuma mun nuna wani abu wanda mara kyau ne, to a ƙarshe menene darasin da ake so a nuna. ‘Akwai ilimi a harkar naku sosai’.

“Malam ya ba mu shawarwari, kuma ya nuna mana irin sukar da ake yi mana a kan harkar duk ba haka ba ne. 

“Sannan ya faɗa mana wasu abubuwa da za mu riƙa amfani da su wurin wayar wa da mutane kai, tunda abin da mu ke yi abu ne mai tarihin gaske.

 

Maiɗakin Sheikh Zakzaky, Malama Zeenat, tare da mawaƙiya Ummi Kano

“Har ya ba mu labarin su ma sun taɓa shirya wani fim a kan Ɗanfodiyo, wanda a lokacin har sun nemi shawarar Sultan na Sokoto da sauran su, amma abin ya turje, aka ƙi barin fim ɗin ya fita, da sauran su. 

“Wannan shi ne abin da mu ka ɗan tattauna kenan a taƙaice. Bayan shi babu wani abu da mu ka tattauna. 

“Ya kuma ce a sanar da ‘yan’uwa ‘yan fim ga saƙon da ya bayar a faɗa masu.”

Bayan mun kammala, mu ka yi sallar isha’i, aka yi addu’o’i.

“Waɗanda mu ka je da su sun haɗa da AGM Bashir, Usman Madobi, Nura Shugaba, Ahmad M. Kubau da kuma mawaƙiya Ummi Kano.”

Sheikh Zakzaky ya na jan maziyartan nasa sallar isha’i

Loading

Previous Post

Hotuna: Bikin auren jaruma Halima Atete a ranar farko

Next Post

Kafin rasuwar Nura Mustapha Waye akwai maganar aure tsakanin mu – Hajara ‘Izzar So’

Related Posts

Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama
Labarai

Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama

August 2, 2026
Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11
Labarai

Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11

August 1, 2026
Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano
Labarai

Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano

July 15, 2026
Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu
Labarai

Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu

July 14, 2026
A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti
Labarai

A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti

July 9, 2026
Labarai

July 4, 2026
Next Post
Aisha Babandi ('Hajara Izzar So') ta na kukan rashin Nura Mustapha Waye a lokacin hirar

Kafin rasuwar Nura Mustapha Waye akwai maganar aure tsakanin mu - Hajara 'Izzar So'

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!