HUKUMAR Tace Finafinai ta Ƙasa (NFCVB) tare da wasu manyan masu shirya fim da ‘yan wasa za su haɗa gwiwa da Hukumar Yaƙi Da Laifuffukan Kuɗi (EFCC) wajen shirya finafinai domin yayata yaƙin da EFCC ke yi da cin hanci da rashawa.
A labarin da mujallar Fim ta samu daga NFVCB, an yanke shawarar ne a yau Alhamis lokacin da ɓangarorin uku su ka yi wani taro na musamman a hedikwatar EFCC da ke Abuja kan hanyoyin da za a bi a shirya finafinan.

An yi taron ne lokacin da Shugaban Hukumar Tace Finafinai, Alhaji Adedayo Thomas, ya jagoranci tawagar ƙungiyoyin ‘yan fim da jarumai da sauran masu ruwa da tsaki zuwa wajen taron wanda su ka yi tare da Shugaban EFCC, Malam Abdulrasheed Bawa.

Wannan labarine Mai karfafa guiwa ga mambobin wannan Masana’anta