• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, August 10, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zarah Diamond ta dawo ruwa!

by DAGA ABBA MUHAMMAD
August 4, 2022
in Labarai
1
Zarah Diamond

Zarah Diamond

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMAR Kannywood mai tasowa, Zarah Muhammad (Zarah Diamond), wadda ta yi aure a asirce a cikin 2021, ta dawo ruwa, domin kuwa alamu sun nuna auren ta ya mutu.

Tun daga irin hotunan da ta ke ɗorawa a Instagram da kuma bidiyon da ta ke yi a TikTok ya sa mutane su ka fara tunanin babu auren.

A ranar 4 ga Yuni, 2022 jarumar ta ɗora wani bidiyo inda ta nuna su na aikin wani fim mai dogon zango mai suna ‘Amaryar Shekara’, wanda darakta Ibrahim Bala ke bada umarni, inda ita kuma ta fito a matsayin likita mai suna Dakta Ameera. 

Jarumar ta ɗora hotuna aƙalla 11 da bidiyo ɗaya na wannan aikin da su ke yi. A lokacin ne mutane su ka tabbatar da auren ta ya mutu.

Zarah Diamond da Abba Harara: “Ba aure na yi ba”

Haka kuma kwanan nan Zarah ta shiga Instagram ta rubuta cewa: “Ni ba aure zan ba, aiki ne na waƙa da fim wanda su ne sana’a ta, pls.”

Dalilin da ya sa jarumar ta yi wannan rubutu kuwa, an ga wasu hotuna ne da ta ɗauka tare da mawaƙi Abba Harara, wanda su ka yi kama da hotunan kafin aure (pre-wedding pictures), sai mutane su ke ganin kamar aure ta sake yi.

Wakilin mu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin jarumar kan wannan al’amari, amma hakan bai yiwu ba, don har tsawon lokaci wayar ta ba ta shiga idan aka kira, da alama ta canza layin waya.

Idan ba ku manta ba, mujallar Fim ta ba ku labarin yadda jarumar da kan ta ta ba furodusoshi da daraktoci haƙuri a lokacin auren nata a wancan lokacin, ta ce: “Salam masoya na, ‘producers’ ɗi na, ‘directors’ da abokan aiki na, waɗanda na gama da kuma waɗanda ban gama ba, ina mai ba su haƙuri, saboda yanayin zaɓin da Allah ke yi wa dukkanin bayin sa, to ya min zaɓi mafi alkairi a gare ni, saboda haka ba ni da baki ko ‘yancin ƙarasa muku ayyukan ku. 

“Fatan za ku fahimce ni? Allah ya ba ku haƙuri ya kuma musanya muku da alkairi.”

Zarah Muhammad (Diamond)

Haka kuma ta yi kira ga mamallakan shafukan mabiyan ta da su cire hotunan ta da bidiyoyin ta daga shafukan, domin fa ita ta yi bankwana da harkar fim.

A saƙon kiran Zahra Diamond ta ce, “Don Allah masu ‘fans page’ ɗi na, ku yi haƙuri ku dubi girman Allah ku cire hotuna ɗi na da kuma bidiyo-bidiyo ɗi na, kuma ku canza suna na. Na gode.”

Loading

Tags: Abba HararaAmaryar ShekaraaurejarumaKannywoodmutuwar aureZarah DiamondZarah Muhammad
Previous Post

Kiran Daso ga matan Kannywood: Mu kiyaye saka sutura mai nuna tsiraicin mu

Next Post

Hukumar Tace Finafinai da ‘yan fim za su haɗa gwiwa da EFCC wajen shirya finafinai kan cin hanci da rashawa

Related Posts

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama
Labarai

Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama

August 2, 2026
Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11
Labarai

Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11

August 1, 2026
Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano
Labarai

Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano

July 15, 2026
Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu
Labarai

Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu

July 14, 2026
A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti
Labarai

A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti

July 9, 2026
Next Post
Shugabannin na NFVCB da EFCC tare da mashirya fim ɗin a harabar hedikwatar EFCC

Hukumar Tace Finafinai da 'yan fim za su haɗa gwiwa da EFCC wajen shirya finafinai kan cin hanci da rashawa

Comments 1

  1. Pingback: Jaruma Zarah Diamond ta dawo ruwa! - HausalLoaded.Com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!