• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, October 4, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kiran Daso ga matan Kannywood: Mu kiyaye saka sutura mai nuna tsiraicin mu

by DAGA ABBA MUHAMMAD
August 3, 2022
in Labarai
2
Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso)

Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCIYAR jaruma Saratu Giɗaɗo (Daso) ta jan hankalin ‘yan matan masana’antar finaginan Hausa na wannan zamani a kan saka ire-iren sutura masu nuna surar jikin su.

Daso ta wannan tsokacin ne lokacin da aka ba ta damar yin magana a taron saukar Alƙur’ani da yi wa ƙasa addu’a wanda mawaƙi Dauda Kahutu (Rarara) ya shirya a Kano a shekaranjiya Litinin.

Jarumar barkwancin ta yi amfani da wannan damar ta ce, “Ya kamata mu mutunta kan mu a duk inda mu ke. Haka kuma don Allah mu kiyaye saka suturar da zai nuna tsiraicin mu, musamman ‘yan matan mu na wannan zamani. Hakan ba daidai ba ne, mu kiyaye.”

Daso ta yi addu’ar Allah ya ƙara kare su daga sharrin mahassada da maƙiya.

Mujallar Fim ta yi nazarin cewa ba tun yau ba ake magana kan yadda wasu daga cikin jarumai mata su ke shiga mai nuna surar jikin su, wanda ya sa su na shan suka a wurin jama’a.

Daso da wata jarumar a wajen taron

Ba ‘yan fim ne kaɗai ke yin wannan ɗabi’ar ba, amma ganin cewa su sanannu ne ya sa ake ɗora dukkan laifin a kan su.

Sannan kuma su na iƙirarin cewa su faɗakarwa su ke, kenan su malamai ne a cikin al’umma, tunda jama’a na kwaikwayon wasu abubuwan da su ke nunawa a finafinan su, amma duk da haka ba su kiyaye abin da zai zubar masu da ƙima a idon al’umma.

Yawancin malamai idan su na wa’azi su kan yi misali da wasu abubuwa da ‘yan fim su ke yi, musamman mata.

A matsayin su na masu faɗakarwa, bai kamata a ce su na shiga irin wanda zai nuna surar jikin su ko wani ɓangare na jikin su ba, domin ko a rayuwar su ta zahiri ba ta fim ba wasu daga cikin su haka su ke saka sutura mai nuna surar su.

Misali, akwai lokacin da jaruma Fati Washa ta saka wata rigar ‘yan ƙwallon Nijeriya, wanda ba ta saka rigar mama a ciki ba, har kan maman ya fito ƙuru-ƙuru ana ganin alamar sa. A lokacin babu irin maganar da ba a yi ba soshiyal midiya.

Ita ma jaruma Maryam Yahaya a ‘yan wasu watannin baya, bayan ta tashi daga rashin lafiya ta tafi ƙasar Dubai shaƙatawa, ita ma ta yi hotuna sanye da kayan da su ka nuna kan maman ta ba rigar mama a ciki.

Hotuna sun jawo ce-ce-ku-ce a soshiyal midiya, har wasu na faɗin cewa jarumar kwanan nan ta tashi daga rashin lafiya amma jinyar da ta yi ba ta sa ta yi hankali ba.

Ganin irin abu da ke faruwa ne, musamman ga jarumai mata na wannan zamani, ya sa Daso ta yi wannan tsokacin.

Loading

Tags: Fati WashamalamaiMaryam YahayamataSaratu Giɗaɗoshigasoshiyal midiyasuturatsiraicitufafi
Previous Post

Ban taɓa rubuta waƙa ba, inji Hussainin Danko

Next Post

Zarah Diamond ta dawo ruwa!

Related Posts

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Rashin lafiyar Kamaye: Sauƙi ya fara samuwa
Labarai

Rashin lafiyar Kamaye: Sauƙi ya fara samuwa

September 17, 2026
Next Post
Zarah Diamond

Zarah Diamond ta dawo ruwa!

Comments 2

  1. Pingback: Matan Kannywood mu kiyaye sanya Sutura mai nuna tsiraicin mu - Mama Daso - HausalLoaded.Com
  2. Pingback: Matan Kannywood mu kiyaye sanya Sutura mai nuna tsiraicin mu – Mama Daso – Arewarank.Com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!