• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Hukumar Zaɓe za ta ɗage zaɓe a Edo da Ondo in akwai tashin hankali

by DAGA WAKILIN MU
August 6, 2020
in Nijeriya
0
Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC)

Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za ta dakatar da shirye-shiryen gudanar da zaɓuɓɓukan gwamnoni da za a yi a jihohin Edo da Ondo idan har abubuwan da ‘yan siyasa ke aikatawa ya jawo tarzoma da karya doka. 
 
Kwamishina na Ƙasa kuma  shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe a hukumar, Mista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a Abuja ran Alhamis bayan an yi taro tsakanin hukumar da masu ruwa da tsaki a zaɓuɓɓukan inda aka tattauna kan al’amura da dama, ciki har da shirye-shiryen zaɓuɓɓukan.
 
Mista Okoye ya ce hukumar ta yi lura cikin damuwa matuƙa da yadda al’amura ke ƙara rincaɓewa wajen abubuwan da jam’iyyun siyasa, ‘yan takara da magoya bayan su ke aikatawa tare da furta maganganun tada fitina a daidai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da zaɓuɓɓukan.
 
Ya ce: “Waɗannan abubuwan sun haɗa har da lalata kayan kamfen na abokan adawa kamar su allunan talla tare da yaƙar juna ta hanyar rikici da furta muggan kalamai.  
 
“Ya na da muhimmanci jam’iyyun siyasa, ‘yan takara da magoya bayan su su sani cewa akwai dokoki da ƙa’idoji da aka shimfiɗa  waɗanda wajibi ne a bi su a lokacin yaƙin neman zaɓe.
 
“Hukumar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen aiwatar da nauyin da ya rataya a wuyan ta na tabbatar da an bi doka da oda.
 
“Saboda haka, lallai ne kada jam’iyyu da ‘yan takara su yi tunanin hukumar ba za ta aiwatar da ƙudirin ta na tabbatar da an bi dokoki da ƙa’idoji ba kuma ta hukunta duk wani wanda ya zaɓi ya karya su.
 
“A shirye hukumar ta ke ta tabbatar da an gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali a jihohin biyu da kuma sauran zaɓuɓɓukan cike gurbi na Majalisar Tarayya da Majalisun Jihohi.”
 
Okoye ya ce tilas ne jam’iyyun siyasa su fahimci cewa ana shirin gudanar da zaɓuɓɓukan gwamnonin Edo da Ondo ne a daidai lokacin da annobar korona ta mamaye duniya kuma hukumar na aiki tuƙuru don tabbatar da cewa an kiyaye dukkan matakan kare kai daga cutar kamar yadda hukumar zaɓen da hukumomin kiwon lafiya su ka tanadar.
 
Ya ce a yayin da annobar ta ke ragargazar jama’a, ya zama wajibi kada a ƙara jibga wa mutanen jihohin Edo da Ondo nauyin fitinar tashin hankali a lokacin zaɓuɓɓukan.
 
“Tilas ne jam’iyyu su tuna da cewa akwai lokutan da dokokin tsarin mulki da na hukumar zaɓe su ka shata wa zaɓuɓɓukan Edo da Ondo kuma barazana ko ainihin aiwatar da tarzoma zai iya rusa waɗannan lokutan har su haifar da rikici da ya danganci tsarin mulki.
 
“Hukumar za ta ci gaba da tuntuɓar masu ruwa da tsaki a jihohin biyu a kan buƙatar da ke akwai ta gudanar da zaɓe cikin kwanciyar lumana, musamman ganin cewa ta kashe maƙudan kuɗin jama’a don shirya zaɓuɓɓukan.
 
“Hukumar za ta ɗauki babban mataki kan duk wani abu da ‘yan siyasa za su yi wanda zai tada hankalin jama’a.”
 
Okoye ya ce za ta yi aiki tare da haɗa gwiwa da hukumomin tsaro don magance duk wani abu ko wata barazanar tada hankali kafin da kuma lokacin zaɓuɓɓukan.
 
“Tilas ne hukumomin da aka ɗora wa alhaki a zaɓuɓɓukan, musamman waɗanda su ka danganci mahance rashin zaman lafiya da yaɗa maganganun ɓatanci da yin amfani da kafofin yaɗa labarai ta hanyar da ba ta kamata ba, su tashi tsaye a aikin su don tabbatar da cewa an hukunta duk wanda aka kama ya na karya doka.”
 
Hukumar ta kwantar wa da al’ummomin Edo da Ondo hankali da cewa ta ƙudiri aniyar yin zaɓe bisa adalci da lumana a jihohin biyu, sannan ta yi kira a gare su da su mara wa shirin goyon baya.
 
 
 
 
 
 

Loading

Previous Post

Mayu ne su ka kashe jarumar Kannywood Asma’u Adam, inji majiya

Next Post

Aya da tsakuwa a littattafan tarihin Shata

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Littattafan biyu: Zaɓi na zaɓe!

Aya da tsakuwa a littattafan tarihin Shata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!