• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 30, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

In da a ce waɗannan marubutan maza ne ba mata ba fa?

by DAGA BALA ANAS BABINTALA
December 17, 2019
in Marubuta
0
Daga hagu: Balaraba, Fauziyya da Bilkisu

Daga hagu: Balaraba, Fauziyya da Bilkisu

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
WAƊANNAN SHIRGA-SHIRGAN MATAYE MARUBUTAN, SHIN DA A CE MAZAJE NE WAI MATAYE NAWA KOWACE ZA TA AURA NE?
 
1. Balaraba Ramat Yakubu
2. Rahma Abdulmajid
3. Bilkisu Yusuf Ali
4. Fauziyya D. Sulaiman
5. Maimuna Idris Sani Beli
6. Amina Hassan Abdulsalam
 
Tarihin rubutun ƙirƙirarrun labaran Hausa ba zai taɓa cika ba tare da an sanya sunayen waɗannan mashahuran matayen ba. Ba wai na zaɓe su ba ne don su kaɗai ne shahararru, na zaɓe su ne don kasancewar su masu aƙida iri ɗaya, wato aƙidar namiji na tauye haƙƙin mata.
 
Abin tambaya a nan shi ne, wai waɗannan matan shida, da mazaje ne yaya ɗabi’ar su za ta kasance ts yaya ɗabi’ar su za ta kasance tsakanin su da matayen su? 
 
A matsayi na na marubuci namiji, na ɗora su ɗaya bayan ɗaya a mizani, na yi nazarin su a matsayin mazaje. 
 
Zan ɗauke su daki-daki na yi sharhi dangane da fahimtar da na yi masu.
 
 
Daga hagu: Amina, Rahma da Maimuna
 
1. HAJIYA BALARABA RAMAT
 
Daɗaɗɗiyar marubuciya wadda littattafan ta mafi rinjaye su ke zargin maza da rashin yin adalci ga mata, mace ce mai raha da saurin sabo da mutane. Hakika Hajiya da namiji ce ‘yar kasuwa ce. Ba na raba ɗaya biyu da namiji ce mata huɗu za ta yi. 
 
Hujja: Mace ce mai ƙasaita. Saboda haka dole ta auri mata huɗu don ta kece raini. 
 
In da a lokacin bayi ne ma, to har da ƙwarƙwarori.
 
2. RAHMA ABDULMAJID
 
Sayyada ta fara rubutu tun ta na da ƙarancin shekaru, ko da yake ba duk rubutun ta ke nuna zargi ga maza su na tauye mata ba, amma ba ɓoyayyen abu ba ne ga duk wanda ya san ta a zahiri ba ta ɓoye ra’ayin ta ga yadda maza ke tauye mata. 
 
Ta na da raha kuma ba ta baƙunta a duk inda ta samu kan ta. Muhawara da ita ba ta da daɗi saboda mayyar kafa hujjoji ce.
 
Kasancewar ta malamar addini kuma hadima, muƙaddima, in da namiji ce ko shakka ba na yi mata huɗu za ta aure, kuma ba za ta bar su a gari ɗaya ba. Za ta rarraba su ne, mai yiwuwa ta bar ɗaya a Lagos, ɗaya a Abuja, ɗaya a Kaduna, ɗayar kuma a Kano.
 
3. BILKISU YUSUF ALI
 
Nana Bilkisu, mai cin tudu biyu kenan, addini da boko. A rubutun ta da lafazan ta ba ta taɓa ɓoye namiji ba ɗan goyo ba ne. Ga ta dai ‘yar boko ce, amma malantar addini da hidima ta rinjayi bokon a ɗabi’ar ta, wanda hakan ya sanya in da namiji ce ko tantama ba na yi mata uku zuwa huɗu za ta aura saboda ƙasaitar malanta.
 
4. FAUZIYYA D. SULAIMAN
 
Magen Lami kenan, ba cizo ba yakushi! Mace ce mai kazar-kazar, ba ta san lalaci ba. Ko da yake yawancin mutane za su yarda da ni cewa ba ta ɗauki duniya da zafi ba, amma ta shigo cikin wannan rukunin ne saboda tunani iri ɗaya da na sauran ‘yan’uwan ta cewa maza na tauye mata. 
 
Hausawa sun ce da ganin kura za ta ci akuya, mutum na kallon ta ya san in da namiji ce ba ta yi kama da masu zama da mace ɗaya ba. Tabbas, in da namiji ce mata biyu za ta yi. 
 
Hujja: ba safai mutum mai kazar-kazar ke iya zama da mace ɗaya ba.
 
5. MAIMUNA SANI IDRIS BELI
 
Dila sarkin wayo! A duk cikin rukunin matan nan babu mai wayon ta, duk da kasancewar ta ‘yar ƙaramar ko kuma na ce mai ‘yar tsabar cikin su. Ita ma ta yarda lallai namiji ba ɗan goyo ba ne, duk da cewa da namiji ce dole mata uku za ta aura. 
 
Hujja: don ta raba kawunan su kada su haɗe mata kai.
 
6. AMINA HASSAN ABDULSALAM
 
Amina ita ce mafi ƙarancin maganar cikin su, haka nan baturiyar cikin su. Zai yi wuya mutum ya gane cikakken ra’ayin ta game da rashin kirkin maza, saboda rashin yawan maganar ta. Amma dai ita ma ta yarda namiji ba ɗan goyo ba ne.
 
Saɓanin sauran matan da na yi bayani a kan su, Amina cikakkiyar Nasara ce, babu shakka in da namiji ce zai yi wuya ta auri mace fiye da ɗaya.
 
Wannan shi ne ra’ayi na game da waɗannan matayen marubuta. 
 
Abin tambayar a nan shi ne, wai waɗannan matan in da mazaje ne za su iya yi wa mata adalci kamar yadda su ke boloƙoƙon nema wa mata ‘yancin kuwa? Ko dai su ma sajewa za su yi kawai ruwa ta sha? Sau tari na kan yi tunanin yaƙin su da maza ya fi kama da siyasa maimakon neman ‘yanci.
 
*
 
Bala Anas Babinlata fitaccen marubuci ne mazaunin Kano

Loading

Previous Post

Rahama Sadau: Ban damu da masu zagi na a soshiyal midiya ba

Next Post

RAHMATA

Related Posts

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 
Marubuta

Gasar rubutu: Ba a taɓa ba marubutan Hausa dama irin wannan ba – Balannaji 

January 1, 2025
Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Zubairu Balannaji ya zama gwarzon gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 31, 2024
‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

‘Dakan ɗaka…’: Kanawa sun lashe gasar rubutu ta Hukumar Tace Finafinai

December 20, 2024
Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai
Marubuta

Mutane 15 sun yi nasarar zuwa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar rubutu na Hukumar Tace Finafinai

November 30, 2024
Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau
Marubuta

Tsakanin matan aure biyu da budurwa ɗaya za a san gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 a yau

November 27, 2024
Ƙungiyar matasa da mata za ta naɗa Ado Gidan Dabino Sarkin Mawallafan Arewa
Marubuta

Gasar rubutu: Hukumar Tace Finafinai ta bayyana gwaraza 50 na zagayen farko

November 24, 2024
Next Post
Dr. Aliyu U. Tilde

RAHMATA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!