• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rahama Sadau: Ban damu da masu zagi na a soshiyal midiya ba

by DAGA ABBA MUHAMMAD
December 17, 2019
in Labarai
0
Rahama Sadau: "A wuri na, ɓata lokaci ne ka tsaya ka na maganar wani"

Rahama Sadau: "A wuri na, ɓata lokaci ne ka tsaya ka na maganar wani"

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

RAHAMA Sadau ta bayyana cewa ita fa ko a jikin ta sukar da wasu mutane ke yi mata a soshiyal midiya. 

 Ta ce kowa da ra’ayin sa, kuma ko me ta yi sai wani ya yi ƙorafin cewa ba ta yi daidai ba, shi ya sa ta ke yin abin ta gaba-gaɗi. 

Shahararriyar jarumar kuma furodusa a masana’antun finafinai na Kannywood da Nollywood ta bayyana haka ne a wata hirar musamman da ta yi da mujallar Fim. 

Rahama Sadau dai ta na ɗaya daga cikin ‘yan fim ɗin da duk abin da su ka yi ya kan zama abin surutu a gari, musamman a kafafen sadarwa na zamani. 

 Ko kwanan nan da ta ɗora wasu hotunan ta a Instagram da Facebook, lokacin da ta ƙaddamar da wani gida mai ɗauke da kamfanonin ta mai suna ‘Sadauz Home’, sai da aka dinga ce-ce-ku-ce a kai. Mutane da dama sun ce shigar da ta yi ba ta dace ba.

Rahama Sadau

Da mujallar Fim ta yi mata tambaya kan irin wannan yamaɗiɗin da ake yi a kan ta, sai Rahama ta ce, “Wallahi mutane ke jin surutun, ba ni ba. 

 “Kamar yadda ka ke magana, haka jiya wani ya zo ya na tambaya na, har ya ke cewa in faɗa masa inda na ke samun ‘courage’ da har ya ke gani na ina dariya. 

 “Ni ba na gani, mutane su ke gani! In mutum miliyan za su yi magana, wallahi ba na gani. Saboda da na ɗora abu na ke yin gaba. 

 “Saboda yadda na riga na ɗora wa kai na, duk abin da ka yi wallahi sai an yi magana a kai. Yau idan hijabi na saka a jiki na, wallahi sai an yi magana a kai. So, kawai ‘just be yourself’, shi ne.” 

Kyakkyawar jarumar kuma ‘yar kasuwa ta yi nuni da cewa duk surutun da za a yi a kan mutum a soshiyal midiya ai ba ya ma daɗewa. Ta ce, “Magana ne da ba daɗewa za a yi ba an daina yin shi an ɗauki wani kuma an ɗora a kai.”

 Ta ce abin baƙin ciki ne a yau yadda mutane su ke bada muhimmanci kan maganar wani can daban wadda ba ta shafe su ba. 

Ta ce: “Ba wani abu da yanzu mutane su ka ɗauke shi da muhimmanci sama da magana: wannan ya yi magana, wancan ya yi magana. Ni ba na ma ɗaukar shi wani abu; da na yi na wuce.”

 A game da irin kiran da za ta yi ga masu irin wannan halayyar ta damuwa da abin da bai shafe su ba kuwa, sai ta ce, “‘Opinion’ ne, ‘opinion’ ni na ɗauke shi. Kuma soshiyal midiyan da ka ke magana, ‘Instagram standard’ ne, a wurin ne kawai za su yi magana. Babu wanda zai zo ya tare ka ‘face-to-face’ ya yi maka magana, bai isa ba wallahi! Iyakar sa fa Instagram, to me zai dame ka? 

“Kawai dai abin da na ke so a gane, shi fa mutum kowa da rayuwar sa, kowa da ‘choice’ ɗin sa, kowa da irin abin da ya ke so a rayuwa. Ni ba zan iya sa maka ra’ayin son kaza ba, kai ma ba za ka iya sa mani ra’ayin son kaza ba. Don haka in ka yi magana a kai na, ra’ayin ka ne ka ji ka na so ka yi, in ka zage ni ra’ayin ka ne.  

“Don haka na ce kowa ya na da ‘opinion’, kuma ‘everybody’s opinion should be respected’.  

“Amma irin waɗannan abubuwan da ke faruwa, gani na ke akwai ‘issues’ da dama da su ka fi wannan. A wuri na, ɓata lokaci ne ka tsaya ka na maganar wani.” 

Loading

Previous Post

Rahama Sadau: Duk mai son aure na ya fito na shirya

Next Post

In da a ce waɗannan marubutan maza ne ba mata ba fa?

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Daga hagu: Balaraba, Fauziyya da Bilkisu

In da a ce waɗannan marubutan maza ne ba mata ba fa?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!