FITACCIYAR jarumar Kannywood Hadiza Muhammad, wadda aka fi sani da Hadizan Saima, ta bayyana godiyar ta ga Allah saboda irin nasarorin da ta samu ta dalilin fitowar ta a cikin finafinai.
Jarumar, wadda ficen ta ya ƙaru ne sakamakon fitowar ta a cikin finafinan nan masu dogon zango na ‘Labari Na’ da ‘Kwana Casa’in’ da ake haskawa a gidan talbijin na Arewa24, ta bayyana haka ne a tattaunawar da mujallar Fim ta yi da ita.
Hadiza ta ce: “Ko da yake ba ‘Labari Na’ da ‘Kwana Casa’in’ ba ne finafinan da su ka fito da ni, amma da ya ke an ce sarki goma zamani goma, to da yawa mutane sun fi sani na da waɗannan finafinan, kuma ina godiya ga Allah da su ka zama silar samun ɗaukaka ta a yanzu.”
A farkon ‘Labari Na’ dai ta fito ne a rayuwar talauci, a ‘Kwana Casa’in’ kuma ta fito a matsayin mai kuɗi. Da mu ka tambaye ta yadda ta ke ji game da waɗannan rol ɗin da ta hau, sai ta amsa da cewa: “To, ai shi jarumi inda zai nuna ƙwarewar sa shi ne duk rol ɗin da aka saka shi ya zama ya yi daidai da shi.
“Domin ka ga a ‘Labari Na’ mu na cikin rayuwar talauci, duk da dai daga baya ai ka ga mun shiga rayuwa ta jin daɗi. Amma shi ‘Kwana Casa’in’ na fito ne a matsayin mai kuɗi wadda ba ma a ƙasar na ke ba, wani dalili ne ya dawo da ni, kuma daga ƙarshe ma sai na koma.
“To ka ga akwai bambancin rayuwa da aka nuna a cikin su, ko? Don haka abin burgewa ne a ce na iya samun kai na a irin wannan matsayin da zan iya duk wani rol da aka ba ni. Kuma ina godiya ga Allah da baiwar sa ce da ya ba ni har na zama hakan.”
Jarumar ta yi godiya ga dukkan masoyan ta masu kallon ta a fim kuma su na yi mata fatan alheri. Ta ce ta na tare da su kuma ta na alfahari da su, ta na fatan Allah ya bar su tare cikin aminci.
![]()







