• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 30, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

INEC ta ƙudiri aniyar ci gaba da aiki da lokutan da ta tsara na rajistar masu zaɓe

by DAGA WAKILIN MU
May 17, 2021
in Nijeriya
0
INEC ta ƙudiri aniyar ci gaba da aiki da lokutan da ta tsara na rajistar masu zaɓe
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce ta na nan kan bakan ta na yin aiki da jadawalin da ta tsara na ci gaba da aikin rajistar masu zaɓe daga ranar 28 ga Yuni a duk faɗin ƙasar nan.

Mista Festus Okoye, wanda shi ne Babban Kwamishinan INEC mai kula da wayar da kan masu zaɓe da yaɗa labarai, shi ya bayyana haka a wata hira da ya yi da Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) a Abuja ran Lahadi.

Okoye ya ce hukumar na nan kan bakan ta, musamman da yake ta samu gidan yana wanda za a yi amfani da shi a wajen aikin.

Ya ce, “An kusa kammala gina gidan yanar yin rajista ta hanyar intanet kuma za a yi aiki da shi wajen yin rajistar masu zaɓe wanda za a fara a ranar 28 ga Yuni.

“An gwada gidan yanar an yi ‘yan gyare-gyare. Zai kasance ya na da maganaɗisun da ke nuna yankunan da ake yin rajista da kuma rumfunan zaɓe.

“Hukumar na ci gaba da aikin ta kuma ta na aiki a cikin tsarin da ta yi na lokuta.”

Hukumar NAN ta ruwaito cewa INEC ta riga ta tsaida 28 ga Yuni a matsayin ranar da za ta ci gaba da aikin rajistar masu zaɓe wanda ta ɗage a baya, kuma ta shigo da sabuwar hanyar kimiyya.

Kwamishinan ya kuma lissafa wasu muhimman ayyuka waɗanda za a yi a cikin lokutan da aka tsara, kafin a kai ga ci gaba da aikin rajistar.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya riga ya bayyana cewa za a ci gaba da aikin har zuwa kashi na uku na shekarar 2022.

Haka kuma Yakubu ya bayyana cewa hukumar za ta maye gurbin tsofaffin na’urorin ɗaukar bayanai kai-tsaye, wato ‘direct data capture (DDC) machine,’ waɗanda aka shigo da su a cikin 2011, don yin rajistar masu zaɓe, da sabuwar hanyar fasaha mai suna ‘INEC Voter Enrolment Device’ (IVED).

A cewar sa, waɗannan sun haɗa da faɗaɗa hanyoyin da masu zaɓe za su samu rumfunan zaɓe ya zuwa ranar 11 ga Mayu, da gina tare da gwada gidan yanar yin rajista ya zuwa ranar 15 ga Mayu da kuma isowar sababbin na’urorin IVED ya zuwa ranar 31 ga Mayu.

Ya lissafa wasu ayyukan da su ka haɗa da ɗaukar ma’aikatan rajistar aiki tare da horar da su, ya zuwa 14 ga Yuni, da kuma ci gaba da aikin rajistar a ranar 28 ga Yuni.

Loading

Tags: Festus OkoyeHukumar Zabe ta KasaINECNigeria electionsProf. Mahmood YakubuVoters registration
Previous Post

Abin da ke jawo ƙwacen akawun na Fesbuk

Next Post

‘Yan wasa 500 za su fito a diramar ‘Gidan Dambe’, inji Tantiri

Related Posts

Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Next Post
‘Yan wasa 500 za su fito a diramar ‘Gidan Dambe’, inji Tantiri

'Yan wasa 500 za su fito a diramar 'Gidan Dambe', inji Tantiri

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!