• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

INEC ta tura Manyan Kwamishinoni 3 wajen zaɓen ƙananan hukumomin Abuja

by DAGA WAKILIN MU
February 9, 2022
in Nijeriya
0
Farfesa Mahmood Yakubu ya na jawabi ga mahalartan taron

Farfesa Mahmood Yakubu ya na jawabi ga mahalartan taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta tura Manyan Kwamishinoni (National Commissioners) guda uku domin su sa ido kan zaɓen Gundumar Birnin Tarayya (FCT) wanda za a yi a ranar Asabar mai zuwa, 12 ga Fabrairu.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya faɗi haka a wajen wani taro na masu ruwa da tsaki a zaɓen wanda aka yi a ranar Talata a Abuja.

Mahmood ya ce za kuma a tura Kwamishimonin Zaɓe na jihohi (REC) guda shida su tallafa wa takwaran su mai kula da gundumar ta FCT don ganin an yi zaɓe babu mishkila.

Yakubu, wanda ya bada tabbacin cewa INEC ta sadaukatar da kan ta wajen ganin an yi zaɓe fisabilillahi, ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a zaɓen da su mara wa hukumar baya ta hanyar ganin an yi zaɓe cikin kwanciyar hankali.

Shugaban ya yi la’akari da cewa idanun INEC na kan dukkan jami’an ta, “na wucin-gadi ne ko na dindindin,’’ domin a tabbatar da cewa sun bi doka da oda sosai.

Ya ce: “Dukkan jam’iyyu, ‘yan takara da magoya bayan su, su ma su yi hakan.

“Babu wanda zai amfana idan an lalata tsarin ko an aikata wani mugun abu. A bar masu zaɓe a FCT su zaɓi shugabannin su a  wajen takara ba tare da tsangwama ba, zaɓe mai nagarta kuma cikin kwanciyar hankali.”

Shugaban ya ce hukumar tasa ta ɗauki ma’aikatan wucin-gadi isassu kuma ta horas da su domin zaɓen.

Ya ƙara da cewa an kai dukkan kayan aiki masar haɗari zuwa ƙananan hukumomin, yayin da kuma Babban Bankin Nijeriya (CBN) zai kai kaya masu haɗarin zuwa Ofishin INEC na FCT da ke Garki, a ranar 10 ga Fabrairu.

Ya ce, “An sawo kayan aiki da ba su shafi na magani ba, za a raba su ga masu zaɓe da ma’aikata don su kare kan su daga cutar korona ( COVID-19) kamar yadda kundin tsarin mulki na hukumar ya tanadar.

“An gama shirye-shirye dangane da sufuri, wanda ya haɗa da samar da babura don shiga lunguna da kuma kwale-kwale don shiga yankuna masu rafuka.

Wani sashe na mahalartan taron

“Za mu yi amfani da kayan tallafi irin su keken rubutun makafi mai yin jagora ga jefa ƙuri’a da kuma gilasan likita domin ƙara girman rubutu saboda masu matsalar gani raɗau.”

Yakubu ya ce an saisaita kuma an shirya komfutar tantance masu zaɓe wadda ake kira ‘Bimodal Voter Accreditation System’ (BVAS)  don a yi amfani da ita a zaɓen, sannan ya ce an sake nazarin aikin ta daga zaɓen da aka yi a baya a Anambra.

Ya ce, “A wuraren zaɓe da jama’a su ka yi yawa, hukumar za ta yi amfani da na’urar BVAS sama da guda ɗaya domin a samu sauri wajen tantance masu zaɓe.

“Haka kuma za mu yi amfani da ƙarin ma’aikata a irin waɗannan wuraren. Mun kuma amince da hukumomin tsaro su tura ƙarin ma’aikata don tabbatar da zaman lafiya da doka.

“Haka kuma mun yi isassun shirye-shirye wajen ayyukan tallafi da sufuri don  kai ɗauki da hanzari idan har aka samu mishkilar da ba mu tsammani a ranar zaɓen.

“Bayan haka, za a wallafa sakamakon zaɓe a gidan yanar ganin sakamako na wannan hukuma, wato ‘INEC Result Viewing portal’ (IReV) kai-tsaye a daidai lokacin da aka gama zaɓe kuma aka ƙirga ƙuri’u a cibiyoyin zaɓe a ranar zaɓe.”

A cewar sa, shi ma wannan zaɓen na Gundumar Birnin Tarayya bai zo ba tare da ƙararraki ba domin akwai ƙararraki takwas a kotu yanzu haka, su na ƙalubalantar zaɓen fidda gwani ko matakin karatu na ‘yan takara.

Ya ce a yayin da wasu daga cikin ƙararrakin su na gaban Kotun Ƙoli ta Ƙasa, babu hukunce-hukuncen da su ka yi karo da juna ko tsawatarwar kotu a ko’ina kan kada a yi zaɓen.

Ya ce: “Bari in yi amfani da wannan dama in yi godiya ga sashen shari’a, musamman Babbar Kotun FCT, kan yadda su ka yi tsayin daka kan ruɗun da ‘yan neman tada tsaye da masu ɗokin zuwa kotu ke yi, waɗanda sau da yawa su kan ɓata wa kotuna da INEC lokaci ta hanyar kai ƙara a kan ko da ƙaramar magana ce.”

Ya bayyana cewa INEC ta yi rajistar ƙungiyoyin sa ido guda 58 (53 na gida, da 5 na ƙasar waje) waɗanda za su tura aƙalla mutane ‘yan sa ido 2,242 zuwa wuraren zaɓe.

Yakubu ya ce hukumar ta yi wa kafafen yaɗa labarai 45 rajista waɗanda za su tura ‘yan jarida 340 domin ɗaukar labarin zaɓen.

Sannan ya nanata kiran da ya yi na cewa sayen masu zaɓe ta kowace irin hanya, ciki har da sayen ƙuri’a a wurin zaɓe, babban karya doka ne.

Ya ce, “Dokar nan ta hana amfani da wayar salula da sauran kayan ɗaukar hoto a cikin rumfar zaɓe ta na nan.”

A nasa ɓangaren, Ministan Gundumar Babban Birnin Tarayya, Malam Muhammad Bello, ya bada tabbacin cewa gwamnati za ta bada gudunmawa ga INEC da sauran masu ruwa da tsaki  don tabbatar da an yi zaɓe mai nagarta ba tare da wata ƙumbiya-ƙumbiya ba a ƙananan hukumomin gundumar.

Shi kuma Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Alhaji Usman Baba, cewa ya yi hukumar ‘yan sanda, a matsayin ta na jagora, ta na aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran hukumomin tsaro wajen bada yanayin da ya dace don yin zaɓe cikin kwanciyar hankali. 

Baba, wanda a taron ya samu wakilcin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda (DCP) Mista Basil Idegwu, ya ce a shirye ‘yan sanda su ke su tabbatar da cewa sun tura ƙwararrun ma’aikata da kayan aiki a lokacin zaɓen.

Sufeto-Janar ɗin ya bada tabbacin cewa ma’aikatan sa za su yi aiki bisa ƙwarewa kuma za su tabbatar da zaɓe maras mishkila wanda babu aikata dabar siyasa ko wasu ayyukan laifi a cikin sa.

Ya ce: “A ɓangaren rundunar ‘yan sandan Nijeriya, an yi ƙoƙari wajen ganin an yi zaɓe maras matsala.

“Wasu daga cikin hanyoyin da aka tsara na tabbatar da zaɓe maras matsala, mai inganci, shi ne an yi nazari kan inda barazana za ta iya ɓullowa, tattara bayanai da musayar bayanan sirri da sauran hukumomin tsaro wanda ya sa aka gane wuraren musamman da ake da barazana a dukkan yankunan ƙananan hukumomin.”

Babban Darakta na ƙungiyar Yaiga Africa, Mista Samson Itodo, ya bayyana jin daɗi kan cewa lallai INEC za ta iya gudanar da zaɓe mai inganci.

Sai dai Idoto ya yi kira ga INEC da ta tabbatar da cewa na’urar BVAS ta yi aiki sosai yadda ya kamata, sannan a fara zaɓe da wuri a ranar zaɓen kamar yadda aka tsara.

Ya yi kira ga ministan FCT da ya roƙi Shugaba Muhammadu Buhari da ya rattaba hannu a kan Gyararren Ƙudirin Zaɓe domin ya zama doka saboda a ƙarfafa ingancin manyan zaɓuɓɓukan ƙasar nan.

Misis Felicia Sani, wadda ita ce Shugabar Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa Maza da Mata ta Nijeriya ta Ƙasa, kira ta yi ga matasa da mata da su kiyayi aikata duk wani abin tada hankali a lokacin zaɓen na FCT.

Misis Felicia ta ce ta bada shawara ga mata da su gargaɗi ‘ya’yan su a kan aikata tada hankali, ta ce, “a ko yaushe a tuna da cewa akwai rayuwa bayan zaɓe.”

Mahalarta a zauren taron

Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) ta ruwaito cewa akwai ‘yan takara 475 waɗanda jam’iyyun siyasa 18 su ka tantance su, ciki har da APC mai mulki da kuma babbar jam’iyyar adawa ta PDP, domin shiga takarar hawa kujerun ciyaman da kansila a Bwari, Abaji, Gwagwalada, Kuje, Kwali da Ƙwaryar Garin Abuja (AMAC).

Rahoton ya ce ‘yan takarar sun yi rantsuwar za su tabbatar da an gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali.

Loading

Tags: 'yan sandaFarfesa Mahmood YakubuFCT ministerFCT pollHukumar Zaɓe ta ƘasaINECkwamishinonin zaɓeMalam Muhammad BelloResident Electoral CommissionersYiaga Africazaben Gundumar Birnin Tarayya
Previous Post

Sakamakon ƙazafi: Kotu ta kulle Sadiya Haruna wata 6 a kurkuku

Next Post

Ƙungiyar Tarayyar Afrika ta zaɓi Swahili a matsayin harshen da za ta riƙa aiki da shi

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Shugabannin ƙasashen Afrika a wajen wani babban taron su a Habasha

Ƙungiyar Tarayyar Afrika ta zaɓi Swahili a matsayin harshen da za ta riƙa aiki da shi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!