• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, May 15, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

INEC ta yi wa daraktocin ta 4 ritayar dole

by DAGA WAKILIN MU
December 28, 2023
in Nijeriya
0
INEC ta yi wa daraktocin ta 4 ritayar dole
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

 

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta tilasta wa daraktocin ta huɗu yin ritaya.

Shugaban Kwamitin Wayar da Kan Masu Jefa Ƙuri’a a hukumar, sannan Kwamishinan Tarayya, Mista Sam Olumekun, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba a Abuja.

Yi masu ritayar dole ɗin ta biyo bayan fara aiki da sabuwar dokar da ta ƙayyade wa’adin shekaru takwas ga kowane daraktan da ke aiki ƙarƙashin Gwamnatin Tarayya.

Olumekun ya ce, “Bisa aiki da umarnin da Gwamnatin Tarayya ta bayar a cikin wata sanarwa mai lamba HSCF/SPSO/268/T3/2/37, wadda aka fitar a ranar 27 ga Yuli, 2023, Hukumar Zaɓe ta bi wannan umarnin ta hanyar umartar dukkan daraktocin da su ka shafe shekaru takwas su na aiki a INEC, ko sama da haka, da su gaggauta yin ritaya.

“Bisa tsarin wannan umarni, daraktoci huɗu daga INEC za su ajiye aiki su tafi ritaya. Biyu daga cikin su Shugabannin Sassa ne a Hedikwatar INEC da ke Abuja, sauran biyu ɗin kuma Sakatarorin Tsare-tsaren Ayyuka ne a wasu ofisoshin hukumar da ke jihohi.”

Sai dai kuma ya yi ƙarin hasken cewa wannan tsarin bai shafi manyan jami’an hukumar masu aiki a ɓangaren kula da lafiya ba, kamar yadda ita kan ta takarda mai lamba MH 7205/T31 ta nuna, wadda aka fitar a ranar 7 ga Satumba, 2023.

“Hukumar Zaɓe na yi wa daraktocin da sallamar ta shafa fatan alheri a rayuwar da za su ci gaba, bayan yin ritayar su,” inji Mista Olumekun.

Loading

Tags: daraktociHukumar Zabe ta Kasa (INEC)ritayaSam Olumekun
Previous Post

Jarumi a Kannywood Abdallah Amdaz zai zama mai igiya biyu Asabar mai zuwa

Next Post

Muhimman Al’amurran Kannywood A Cikin 2023

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Abba El-Mustapha ya na karɓar takardar naɗa shi Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai daga hannun Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Dakta Baffa Bichi, a ranar Juma'a

Muhimman Al'amurran Kannywood A Cikin 2023

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!