Janairu
* Jarumin Kannywood Shariff Aminu Ahlan ya bayyana jimamin rashin mahaifiyar sa da ta cika shekara tara da rasuwa.
* Jarumi kuma darakta a Kannywood, ya taya matar sa Hajiya Maimuna Garba Ja Abdulƙadir murnar ƙara shekara a rayuwar ta.
* ‘Ya’yan Sallau ‘Daɗin Kowa’, Mu’azzam da Aliyya sun yi saukar Alƙur’ani.
* Mawaƙa a Kannywood, Hassan Sani Abubakar da Hussaini Sani Abubakar su ka cika shekara ɗaya da aure cur da tagwayen matan su.
* Mawaƙi Aminu Ala ya zargi ƙungiyar su ta 13×13 wadda mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ya ke jagoranta da yi masu ingiza mai kantu ruwa kan jam’iyyar ADP ta su Alhaji Sha’aban Sharaɗa.
* Mawaƙi Aminu Ala ya canza sheƙa daga jam’iyyar ADP zuwa jam’iyyar APC.
* Rundunar ‘yan sanda a Jihar Kano ta kama jarumar barkwanci a TikTok, Murja Ibrahim Kunya.
Fabrairu
* Kotun Shari’ar Musulunci da ke Filin Hoki a Kano ta tura jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya gidan yari.
* Gwamnatin Kano ta gargaɗi jarumar Kannywood, Teema Makamashi, da cewa ta san iyakar ‘yancin faɗar albarkacin bakin ta.
* Furodusa a Kannywood, Abubakar Bashir Maishadda ya yi martani kan ƙurar da ziyarar da shi da wasu ‘yan Kannywood su ka kai wa tsohuwar jaruma Halima Atete a gidan mijin ta a Maiduguri, Jihar Borno.
Maris
* Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta gurfanar da mawaƙi G-Fresh Al-Ameen bisa zargin wasa da sallah a wani faifan bidiyo.
* Mawaƙi Nazifi Asnanic ya shiga tsaka mai wuya sakamakon jin sunan sa da aka yi a cikin waɗanda ake tuhuma da tarzomar siyasa a Tudun Wada da ke Jihar Kano.
* Zauna-gari-banza da ba a san ko su waye ba sun ƙona gidan mawaƙi Dauda Kahutu Rarara a Kano, a wani hari da ke da nasaba da siyasa.
* Jarumi kuma mawaƙi a Kannywood, Yusuf Haruna (Baban Chinedu), ya ƙaryata masu cewa an ba su kuɗi ko gida ko mota shi da Rarara.

Afrilu
* Fitattun mawaƙa mata na Kannywood sun kafa sabuwar ƙungiya ta mata mawaƙa zalla mai suna ‘Muryar Mawaƙa Mata A Yau Progressive Association’.
* An gurfanar da mawaƙin siyasa Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) a gaban Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke unguwar Rijiyar Zaki a Kano kan kuɗi naira miliyan goma da dubu ɗari uku.
* Hukumar ‘yan sanda ta Nijeriya ta kama ‘yan sanda da su ke baiwa mawaƙin siyasa Dauda Kahutu Rarara.
* Jarumi kuma mawaƙi a Kannywood, Adam A. Zango, ya saki matar sa, Safiyya Umar Chalawa.
* Hukumar ‘yan sanda ta Nijeriya ta kori jami’an ta uku daga aiki waɗanda su ke tsaron lafiyar mawaƙi Dauda Kahutu Rarara a bisa laifin rashin iya aiki.

* Darakta, jarumi kuma kakakin Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), ya ƙaryata labarin da aka yaɗa a soshiyal midiya wai ya rasu.
Yuni
* Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari ya yi tazarcen shekara uku.
* Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kano ta tare a ofishin ta.
* Kotun Shari’ar Musulunci da ke filin Hoki, unguwar Hausawa ta yanke wa Baban Chinedu hukunci kan ɓata wa tsohon babban sakataren Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i na Jihar Kano, Isma’ila Na’abba Afakallahu.
* Matan da su ka yi harkar fim, daga baya su ka yi aure sun kafa sabuwar ƙungiya domin haɗa kai da taimakon juna a tsakanin su mai suna ‘Kannywood Housewives Association’ (KAHOWA).
Yuli
* Auren tsohuwar jarumar Kannywood Wasila Isma’il da darakta, jarumi kuma kakakin Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Malam Al-Amin Ciroma ya mutu.
* Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa jarumi a Kannywood, Malam Abba El-Mustapha shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano.
* Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta soke dukkan wata takarda ta ba da izinin gudanar da duk wani aiki a masana’antar Kannywood a Jihar.
* Auren jaruman Kannywood biyu mata, Hafsat Idris sa Zahra’u Shata, ya mutu.
* Shahararren darakta kuma jarumi a Kannywood da Nollywood, Ali Nuhu ya lashe matsayin Jarumin Jarumai Na Gasar Finafinan Nijeriya ta nahiyar Europe Golden Awards, a ƙasar Jamus.
Agusta
* Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta dakatar da sayar da finafinai fassarar Indiya da ma sauran duk wani fim da aka fassara shi daga wani yare zuwa Hausa a dukkan faɗin Kano.
* Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya naɗa Sanusi Oscar 442, Tijjani Gandu da Maryam Jankunne manyan muƙamai a gwamnatin sa.
* Tsohon ɗan wasan kwaikwayo Malam Abdullahi Shu’aibu (Ƙarƙuzu), ya yi kira ga jama’a su kawo masa ɗauki bayan ya makance sannan ya na fama da rashin lafiya.
* Hukumar Hisbah ta goyi bayan soke lasisin ‘yan fim da Hukumar Tace Finafinai ta yi.
* Matashin ɗan ƙwallon ƙafa ta Super Eagles, Ahmed Musa ya saya wa ɗan wasan kwaikwayo Ƙarƙuzu gida na N5,500,000 da kyautar N500,000.

Satumba
* ‘Yan Kannywood sun kai wa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da Ministar Fasaha, Raya Al’adu da Harkokin Nishaɗantarwa, Hajiya Hannatu Musawa, ziyara a Abuja.
* Mawaƙin siyasa, Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara), ya ɗauki nauyin gyara hanyoyi a karkarar su ta Jihar Katsina.
* Sakataren Tsare-Tsare (organizing secretary) na Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kaduna, Abubakar Hunter ya yi murabus daga muƙamin shi.
* Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, ta dakatar da shirya finafinai domin sabunta rajista.
Oktoba
* An gudanar da walimar saukar Alƙur’ani na ɗiyar shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, wato A’isha Abba El-Mustapha (Lateefa).
Nuwamba
* Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da jarumin Kannywood Abdul Sahir (Malam Ali na ‘Kwana Casa’in’) daga yin fim na tsawon shekara biyu.
* Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta yi martani kan samamen da Hukumar Hisbah ta fara kawai gidajen Gala da ke ciki da wajen Kano.
* Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana mutuwar Alhaji Usman Baba Pategi (Samanja) a matsayin babban rashi ga ƙasa nan, saboda ɗimbin gudunmawar sa ga cigaban ta.

* Jarumin Kannywood Rabi’u Rikadawa ya bayyana farin cikin sa game da karramawar da ya samu daga ‘Our Nigerian News Magazine’, wanda shi kaɗai ne ya samu karramawar a finafinan Hausa.
* Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana cewa Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano tan a samun cigaba a ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba El-Mustapha.
* Furodusa a Kannywood, Alhaji Sheshe, ya maka jarumin Kannywood, Abdullahi Amdaz, a kotu bisa zargin aikata laifukan ɓata suna a kan ‘yan fim da ya ce ya yi.
* Auren tsohuwar jaruma a Kannywood, A’isha Aliyu (Tsamiya) bai mutu ba.
* An gudanar da Bikin Baje Kolin Finafinan Harsuna Gadon Afrika na Kano, ‘Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival’ (KILAF) a Kano.
* Wani fim mai suna ‘Ngoda’ ya lashe manyan kyaututtukan da aka ci a gasar Bikin Baje Kolin Finafinan Harsuna Gadon Afrika na Kano, ‘Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival’ (KILAF).
* Furodusa a Kannywood Abdul Amart ya saya wa iyalan marigayi Aminu S. Bono gida, shi kuma mawaƙin siyasa Dauda Kahutu Rarara ya ɗauki nauyin karatun ‘ya’yan sa.
Disamba
* Tsohuwar jaruma a Kannywood, Hajiya Fati Ladan, da mijin ta, Alhaji Yerima Shettima, sun yi walimar cikar su shekara goma cur da aure.
* Jaruma a Kannywood da Nollywood, Rahama Sadau ta bayyana cewa ta cika shekara 30 a duniya.
