HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta yi wa sababbin masu zaɓe miliyan 5.8 rajista a aikin da ta ke ci gaba da yi na yi wa masu zaɓe rajista, ya zuwa ranar Litinin, 14 ga Fabrairu.
Hukumar ta faɗa a ranar Litinin cewa mutum miliyan 3.13 daga cikin sababbin da aka yi wa rajistar sun kammala rajistar su baki ɗaya.
Ta ƙara bayanin cewa mutum miliyan 1.3 daga cikin masu rajistar sun yi tasu rajistar ne ta hanyar yanar gizo, yayin da miliyan 1.84 su ka je su ka yi ido da ido.
Ta ce mutum miliyan 1.6 daga cikin masu rajistar maza ne, sannan miliyan 1.5 mata ne, yayin da mutum 27,543 naƙasassu ne.
Hukumar ta kuma ce mutum miliyan 9.9 da su ka yi rajista sun buƙaci a yi masu canjin wurin zaɓe ko a musanya masu katin zaɓen su ko a cike masu bayanan da ke kan katin su.
INEC ta yi la’akari da cewa mutum miliyan 5.2 da su ka bada buƙatar su maza ne, sannan miliyan 4.6 mata ne, yayin da 95,138 naƙasassu ne.