• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, June 19, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Irin Tatsunniyoyin Da Aliyu Kankara Ke Yaɗawa Game Da Shata

by DAGA IBRAHIM SHEME
March 3, 2020
in Mawaƙa
0
Aliyu Kankara da littafin sa mai cike da almarori game da Shata

Aliyu Kankara da littafin sa mai cike da almarori game da Shata

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
ALHAJI Dakta Mamman Shata Katsina fasihi ne da Allah ya keɓanta shi da sauran mawaƙa ta wajen fasaha, zalaƙa, jimawa, samu, farin jini, yawan waƙoƙi da halayya. Ta wajen halayya, za a iya ce masa wandara – wanda idan an yi yamma sai ya yi gabas; wasu na ce masa “wani iri”. To amma fa a inda ya bambanta ɗin, ba da baƙin hali ba ne, sai dai ban-sha’awa, burgewa da kuma bazata.
 
Alh. Shata ya sha yin abubuwan mamaki, kamar shiga kogo ko shiga daji ko tafiya da tsakar dare, ko ya kama maciji; Allah ya hore masa. Haka kuma zai iya furta magana mai ban-mamaki. To amma fa hakan bai keɓe shi daga kasancewa mutum. Ba aljani ba ne kamar yadda za ka ji wani baƙauye ya faɗa; ‘aljanancin’ sa bai wuce na yin abin mamaki irin waɗanda na lissafa ba.
 
To amma wani abin mamaki shi ne yadda wani mutum mai iƙirari da ilimi, Dakta Aliyu Ibrahim Ƙanƙara na Jami’ar Tarayya ta Dutsin-ma, ya zama jagaba wajen yaɗa wasu labarai waɗanda su ka danganci almara ko ƙarya muraran game da Alh. Shata. Ni ya fara ba waɗannan almarorin domin in shigar da su a cikin littafin da na rubuta mai taken ‘Shata Ikon Allah!’ wanda aka buga a shekarar 2006. Da na ƙi amincewa, sai ya ɗauke su, ya ƙara yawan su ma, ya zuba a cikin wani littafi mai mai taken ‘Mahadi Mai Dogon Zamani’, wanda littafin mu ne (wanda mu ka yi tare da shi a baya) ya wanka ya baddala shi ya fito da shi a matsayin nasa.
 
Tatsunniyon ko ƙarairayin su na da yawa, amma ga ‘yan kaɗan na ɗauko daga littafin “Mahadi Mai Dogon Zamani” domin ku yi nazari a kan su.
 
A cewar Dakta Ƙanƙara:
 
1. Shata na rikiɗa. Ka na zaune da shi wani lokaci  sai ka ga ya koma ƙaramin yaro kyakkyawa, sannan kuma sai ya rikiɗa ya koma tsoho tukuf, amma mummuna.
 
 2. Shata ya na hasashen abin da zai faru nan gaba, ko dai abin ya faru a zamanin shi ko kuma ma sai bayan ran shi. Wai malamai sun ce ya na da wasu rauhanai ne da ke masa bushara da abin da zai faru a gaba. Ya bada misali da cewar Shata ya san za a kashe Shugaban Ƙasa Janar Murtala kwana uku kafin a kashe ɗin, har ma ya faɗa wa wasu mutane a Kano. Kuma wai ya taɓa miƙa wa wani babban yaron sa farin yadi ya ce masa, “Karɓi, likkafanin ka ne, domin sauran kwana uku ka mutu!” Kuma kwana ukun na cika, babu ko ciwon kai, hadimin na Shata ya mutu.
 
 3. Wai a ranar bikin ‘yan Sarki a Kano, a farkon zamanin Sarki Murabus, an ga wata mace ta shigo fagen da ake bikin, ta na riƙe da takori tsirara, ta na wurwura ta, ta nufi Shata kai-tsaye. Amma Shata ya na ɗaga yatsa sama sai aka ga matar ta ɓace.
 
4. Wani lokaci idan ka je wurin Shata, to aljani za ka taras a zaune, kuma Shatan ne!
 
 5. Idan Shata ya yi maka zambo ya zage ka a waƙa, babu wanda zai kalli abin a matsayin cin fuska, sai dai a ce yabo ne. Kenan kowa yanzu ya na kallon “Gagarabadau” a matsayin yabo ne.
 
 6. An taɓa kawo ruwan batir (acid) a gaban Shata a wani ƙauyen Funtuwa, ana hira, aka ce duk wanda ya sha shi zai mutu. Sai Shata ya ce ƙarya ne. Sai aka kamo wani ɗan akuya aka ɗura masa ‘acid’ ɗin a baki, nan take ya mutu. Sai Shata ya karɓi kwalbar ‘acid’ ɗin ya juye ruwan kaf a bakin shi, ya haɗiye. Ana tsoron me zai faru, amma ba abin da ya same shi.
 
 7. Idan Shata zai yi wasa a otal a Kano ko a Funtuwa, jama’a ta taru, to ba a ganin Shata ya na shigowa filin wasan, sai dai kawai a gan shi a tsaye a tsakiyar filin!
 
8. Ana taro wata rana a Mararrabar Jos, sai ƙudan zuma su ka dirkako mutane, kowa ya watse ban da Shata. Da gungun zumar nan su ka zo daidai goshin Shata sai su ka tsaya cak, kamar sun ci karo da bango, sai su ka juya su ka tafi. Can kuma sai su ka sake dawowa, su ka dai tsaya a daidai goshin sa, su ka kuma tafi, har sau uku, ba su iya taɓa shi ba.
 
9. Wai Alh. Kabiru Kazaure (wanda mun san shi) ya faɗa wa Ali Ƙanƙara cewa sun taɓa raka Shata zuwa bakin madatsar ruwa (dam) ta Kazaure. Sai Shata, ba tare da ya tuɓe tufafin sa ba, ya shiga cikin ruwan dam ɗin nan. Su na tsaye har tsawon minti 40, sannan sai su ka ga Shata ya fito, kuma tufafin sa ba su jiƙe ba ko ɗis!
 
10. Shata da yaran sa sun zo wucewa ta kusa da wani rafi da ya cika da ruwa, a Jihar Kaduna, sai Shata ya tsaya da mota ya ce su yi gaba, shi sai ya zo. Ba tare da ya cire kayan jikin shi ba, sai ya auka cikin rafin nan ya nutse. Sai da aka yi awa biyu sannan ya fito, kuma sai su ka ga kayan shi ba su jiƙe ba ko kaɗan.
 
 11. Aljana ce ta fara auren mahaifin Shata, shi ya sa bai yi aure da wuri ba. Sai da aka kai shi wajen wasu bokaye su ka yi masa girka, sannan aljanar ta amince ya yi aure (ya yi mata kishiya kenan?).
 
 12. Bokaye sun yi wahayi da irin matar da mahaifin Shata zai aura, su ka ce “za ta ɓullo ne daga gabas”. Kuma wai hakan aka yi.
 
13. Ranar da za a haifi Shata, an ji kalanguna su na tashi da tsakar dare a samaniyar Musawa, kuma duk mahaluƙin da ke karkarar Musawa ya ji wannan kiɗan.
 
 14. Aljanu sun ɗauke jariri Shata kwana uku bayan an haife shi, ba su dawo da shi ba sai a ranar suna kawai aka gan shi kwance a zanin goyon shi.
 
Akwai ire-iren waɗannan tatsuniyoyin da damar gaske waɗanda Ali Ƙanƙara ke yaɗawa game da Shata a gidajen rediyo da na talbijin rubuce-rubuce sa da jawaban sa. Kaɗan na kawo.
 
Babbar matsalar waɗannan tatsuniyoyin ita ce ba wai Ƙanƙara ya kawo su ne a matsayin wai-wai ba (wato ‘legend’) don masu karatu ko saurare su ji yadda wasu mutane a da su ka ɗauki Shata, a’a, shi ya kawo su ne a matsayin dahir (‘historical facts’), kuma ya na so mutane su amince da su a matsayin gaskiya domin shi ɗin nan ya gaskata su.
 
Hakan ne ya sa iyalin Alh. Shata ba su jin daɗin kwakwazon da Ƙanƙara ke yi game da maigidan su. ‘Ya’yan sa sun yi sun yi su hana shi, ya ƙi hanuwa. Akwai lokacin da Barr. Jamila Shata ta ɗauki lauya da niyyar maka Ƙanƙara a kotu, amma ta ƙyale shi; illa iyaka sai ta hana gwamnatin Katsina ƙaddamar da littafin bayan Ƙanƙara ya nemi gwamnatin ta tallafa masa. Ni shaida ne, domin ni ne na dinga tausasa Jamila ta yi haƙuri domin a lokacin ina ta ƙoƙarin hana shi fito da littafin, wanda da farko ya amince amma daga baya ya bi kiɗan mazugan sa, ya fito da shi.
 
Babu mamaki ganin cewa iyalan Dakta Shata ba su aminta da kamfen ɗin da Ali Ƙanƙara ya ke yi a kan maigidan su ba. Dalili shi ne sun san cewa duk da shu’umancin Shata, zai yi wuya mutum mai hankali ya ɗauki waɗancan almarorin na Ƙanƙara a matsayin gaskiya, har ya tafi ya na yaɗa su. Idan kai mai karatu ka yarda da su, to ruwan ka, amma su ba su yarda ba. Haka ni ma.
Previous Post

Umar M. Shariff: Nasihar mahaifin mu kafin ya rasu jiya

Next Post

Rikicin a-yaga ya kutso kai cikin MOPPAN

Related Posts

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi
Mawaƙa

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi

April 19, 2025
Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala

October 28, 2024
Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala

July 16, 2024
Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara
Mawaƙa

Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara

May 13, 2024
Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 
Mawaƙa

Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 

December 7, 2023
Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala
Mawaƙa

Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala

December 3, 2023
Next Post
Ahmad Sarari (a hagu) da kuma Sani Rainbow

Rikicin a-yaga ya kutso kai cikin MOPPAN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!