* Ma’ajin ƙungiya, Sani Rainbow, ya yi murabus
* An hana ciyamomin jihohi kafa ƙungiya
WANI saɓani ya na neman wargaza haɗin kai a tsakanin shugabannin haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinai ta Nijeriya, wato ‘Motion Picture Practitioners Association of Nigeria’ (MOPPAN).
Ita dai MOPPAN, ita ce uwar ƙungiyoyin masu shirya finafinan Hausa a Nijeriya.
Saɓanin ya jawo har ma’ajin ƙungiyar, Alh. Sani Rainbow, ya yi murabus daga muƙamin sa a jiya Talata, 3 ga Maris, 2020.
Duk da yake bai bada wani dalili na sauka daga muƙamin nasa ba, ana kyautata zaton rashin gamsuwa da abin da ke wakana cikin ƙungiyar ne ya sa ya sauka.
Rainbow, wanda ke zaune a Gusau, Jihar Zamfara, ya aike da takardar aje aiki ne a wani guruf ɗin soshiyal midiya na ƙungiyar.
Hakan ta faru jim kaɗan bayan wata sanarwa da shugaban MOPPAN na Jihar Sokoto, Malam Bello Achida, ya bayar ta wani taro da ciyamomin su ke so su gudanar.
Ciyamomin sun daɗe su na so riƙa yin taro a ƙarƙashin wata ƙungiyar tasu da su ke so ku kafa mai suna ‘Chairmen’s Forum’.
Wasu daga cikin ‘yan kwamitin gudanarwa na ƙasa na MOPPAN ba su amince a yi taron ciyamomin ba domin su na ganin wata maƙarƙashoua ce aka ƙulla masu.
Amma Achida ya ce ba da sunan ‘Forum’ su ka kira taron ba.
Tun da fari, a wata sanarwa da ya bayar, Achida ya ce sun kira taron ne don tattaunawa kan halin da ƙungiyar ke ciki, musamman rashin kataɓus ɗin ta da su ke gani a ƙarƙashin jagorancin Dakta Ahmad Sarari.
Ya ce, “Ina sanar da dukkan shugabannin wannan ƙungiya na ƙasa cewa mun kira ‘meeting’ ne ba da sunan ‘Forum’ ba, mun kira ne a matsayin mu na ‘yan ƙungiya masu riƙe da jihohi.
“Kamar yadda kowa ya sani, jihohi na samun ƙalubale mai ɗimbin yawa, bisa ga rashin samun cikakken labarin abin da ƙungiya ta ke ciki kusan wata biyar, kuma mun samu labarin irin taƙaddamar da ta ke faruwa tsakanin shugabanni na ƙasa. Don haka mu ka kira ‘meeting’ don mu tattauna mu bada shawara.
“Ba zai yiwu mu zura idanuwa mu na kallon matsala, kuma mu yi shiru don gudun wani ko wata ba, don haka idan ba a buƙatar mu yi taro to uwar ƙungiya ta kira taro da mu, ya zamo taro na farko cikin wata biyar na zama shugabanni.
“Don haka mun bai wa shugabanni na ƙasa dama na su kira taro kafin ranar taron Kaduna.”
Bayan wannan sanarwar ne sai kuma ga wata sanarwar ta rushe ƙungiyar ciyamomi daga jami’in yaɗa labarai na MOPPAN na ƙasa, Malam Al-Amin Ciroma.
A sanarwar, mai taken “‘Chairmen Forum’ in MOPPAN Stands Dissolved”, Ciroma ya ce: “Idan an tuna, ba a daɗe da rantsar da sababbin ‘yan kwamitin zartaswa na uwar ƙungiyar masu harkar fim ɗin Hausa ba, wato MOPPAN, ƙarƙashin shugabancin Shugaba na Ƙasa, Dakta Ahmad Muhammad Sarari, a ranar 28 ga Oktoba, 2019, aka yi Allah-wadai da wata ƙungiya kishiyar ta da ta fito, aka yi gargaɗin cewa idan har industiri ɗin nan ba a haɗa kai ba, ‘za mu ci gaba da fama da matsalolin da ke damun masana’antar’.
“Kwamitin gudanarwa na ƙasa na MOPPAN ya yi Allah-wadai da ƙungiyar da wasu rassan mu na jihohi su ka kafa da sunan wai ‘concerned chairmen forum,’ kuma an ce ba za a amince da wannan yunƙurin nasu ba.”
Ya ƙara da cewa kafa ƙungiyar ciyamomin ya saɓa wa tsarin mulkin MOPPAN.
Ciroma ya yi kira ga dukkan ‘yan fim da su yi watsi da ƙungiyar ciyamomin, kada su saurare ta, ya na mai faɗin ya kamata a zama tsintsiya maɗaurin ki ɗaya.
Ya ce MOPPAN ba ƙungiyar siyasa ba ce, sannan ya buƙaci ciyamomin da su tsaya a harkar ƙungiya iya bakin jihar su kaɗai.
Nan take Achida ya mayar da martani game da wannan sanarwa ta rushe ƙungiyar ciyamomin, inda ya ce, “A madadin shugabannin MOPPAN na jihohi ina sanar da dukkanin shugabanni cewa taron mu na Kaduna ya na nan, za mu shigo Kaduna ranar Juma’a, 6 ga Maris, 2020, za mu bar Kaduna ranar Asabar, 7 ga Maris, 2020 in-sha Allah.
“Ina roƙon Allah ya kawo kowa lafiya mu koma lafiya a cikin ƙoshin lafiya.”
Sannan ya sake tura wani saƙon kamar haka: “Bai kamata in yi sa-in-sa da shugaba na ba, amma ita gaskiya ka na iya faɗin ta ta ko’ina ta kama, Allah ya na sheda, kuma za mu maimaita wannan maganganun a gaban Allah.
“Allah kuma ya na sheda mun yi magana da Dakta Sarari, shugaban mu.
“Da fari ya nemi mu maida taron a Kano.
“Bayan na yi wa shugabannin jihohi bayani, su ka bada ƙorafi mu ka yi matsaya da mu yi shi a Kaduna.
“Na sake gaya masa, sai ya ce akwai matsala ‘meeting’ a ranar Juma’a, me zai hana mu maida shi Asabar?
“Mu ka aminta da maida shi ranar Asabar, kuma ya gaya min cewa ba shi da lafiya, amma duk da haka zai zo wataƙila ma tare da wasu ‘Exco’.
“Don haka Allah ya na sheda na, ban yi masa ƙarya ba.”
Mujallar Fim ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Sani Rainbow kan murabus da ya yi, amma ba ta same shi a waya ba. Wakilin mu ya tura masa da tes, amma har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto bai bada amsa ba.
Da mujallar Fim ta tuntuɓi Al-Amin Ciroma kan abin da ke wakana, musamman ƙarin bayani game da rushe ƙungiyar ciyamomi, sai ya ce, “Abin da ya ke faruwa, su waɗannan ciyamomi da su ka zo, sai su ka haɗa wani guruf su ma wai na ciyamomi, wanda kuma ‘is unconstitutional’.
“Mu mun gane cewa akwai manufa da yin hakan a ƙasa, shi ya sa sai mu ka ankarar da su cewa babu wannan a ‘constitution’, don haka bai kamata su ce sai sun kafa ‘Chairmen’s Forum’ ba.
“Su kuma sun dage dole sai sun yi, don tun a baya sun yi wannan yunƙurin an hana su, to yanzu ma haka su na nan an hana.
“‘Point’ na farko, idan ciyamomi duka su ka haɗu a matsayin ƙungiya, waye zai jagorance su? ‘National President’ ne, shi ne zai jagorance su, kuma babu ‘national president’ a cikin su, ya kenan? Ana sarki biyu a gari ɗaya? Ka ga ai ba a yi.
“Sannan ‘point’ na biyu: lokacin Abdulkareem Muhammad ba a yi ba, lokacin Sani Mu’azu ba a yi ba, lokacin Farfesa Umar Faruk ba a yi ba, sai Abdullahi Maikano ne da ya zo, saboda son zuciya irin nashi ya bar waɗannan abubuwa su ka faru.
“Galibin su ba su da wata sana’a sai fim, ba su da ‘investment’, in ka kalle su kaf ɗin su babu furodusa fitacce, babu wani darakta a cikin su da ya san ciwon kan fim, an dai maida abin kawai ‘yan taratsin siyasa. Don haka ba za a kawo siyasa a ‘professional body’ ba.”
Da mujallar Fim ta tambayi Ciroma ko wannan al’amari na da nasaba da aje muƙami da Rainbow ya yi, sai ya ce, “A’a, ba na jin ya na da wata alaƙa, sai dai idan an tambaye shi.

“Kawai dai ya yi ritaya a matsayin shi na ‘Treasurer’. Kuma babu wanda ya san dalilin da ya sa ya aje muƙamin nasa.
“Amma kuma mu a gare mu wannan cigaba ne aka samu, ta yadda idan mutum ya san cewa ba zai iya yin wani abu ba, zai iya cewa da kan sa a naɗa wani, shi ya aje. Ka ga wannan cigaba ne, haka mu ka kalli lamarin.”
Haka kuma mujallar Fim ta tuntuɓi Bello Achida game da maganar ‘Chairmen’s Forum’, sai ya ce, “Ni ban san zancen ‘Forum’ na ciyamoni ba wallahi.
“Ni dai na san za mu yi ‘meeting’ ne mu tattauna matsalolin mu na jihohi, kuma mu kai shawara ga uwar ƙungiya ta ƙasa, sai dai wasu ne su ka fassara mu da hakan.
“Kowace jiha ta na da matsalar da ta ke fuskanta. A kan wannan ne za mu yi ‘meeting’, amma ba taron kafa wata ƙungiya ta ciyamomi ba.
“Kuma ga wani cigaba da mu ka ji na cewa MOPPAN da Arewa za su haɗe a yi tafiya ɗaya. To, in mu Jihar Sokoto ba mu da wannan matsalar wasu jihohin ba za a rasa ba. Don mu a nan da MOPPAN da Arewa da AGN alhamdu lillah mu na tafiya kai ɗaya.
“Wannan ya sa mu ka kira taro don mu tattauna abubuwan da za su kawo cigaba a gare mu, sannan mu tunkari shugabannin mu, mu ba su shawara don mu mu ka zaɓe su, kuma mu mu ka aminta da su jagorance mu.
“Amma sai aka juya abin aka ce wataƙila ma wasu ne su ka turo mu.”