FITACCIYAR jaruma Samira Ahmad ta gina wa ɗaliban makarantar sakandaren ‘yanmata (GGSS) da ke Jogana rijiyar tuƙa-tuƙa kyauta.
Jarumar ta halarci taron ƙaddamar da rijiyar a ranar Alhamis, 4 ga Maris, 2020.
Ɗaruruwan ɗalibai da malaman su sun halarta.
Mujallar Fim ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Samira amma hakan ba ta samu ba.
Amma wasu daga cikin ɗaliban sun bayyana cewa sun yi matuƙar farin ciki a kan abin da da jarumar da ta yi masu na bazata, ta kuma fidda su cikin fama da kuma wahalar ruwan da su ke yi.
Daga ƙarshe, ɗaliban sun yi wa Samira godiya da fatan alheri ga masana’antar kannywood gaba ɗaya a kan taimakon da su ke ma al’umma.

![]()






