TSOHON Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Arewa (AFMAN), Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama, ya ja hankalin abokan sa na Fezbuk a kan wani mutum da ke amfani da shafin nasa ya na yaudarar abokan sa.
Iyan-Tama ya yi jan hankalin ne a Fezbuk a jiya Litinin, inda ya yi rubutu kamar haka:
“Sanarwa! Sanarwa! Sanarwa!!! Yanzun nan wani aboki na ya kirawo ni ya ce wani wanda bai tsoron Allah ya na amfani da suna na da kuma Facebook ‘account’ ɗi na ya na tura wa mutane saƙo, wai mutum ya ba da N2,000, sannan ni kuma zan tura da ninkin haka.”
Ya ƙara da cewa, “Jama’a, ‘yan’uwa, ba da yawu na ba, kuma a kiyaye, kar wani ya rufta ku. Jama’a a yi ƙoƙari a taimaka a gano min ko waye wannan. Na gode.”
Dangane da lamarin, Kamal Y. Iyan-Tama, wanda yaron Iyan-Tama ne, ya na kuma yi wa kan sa laƙabi da Sarkin Yaƙin Iyan-Tama, cewa ya yi: “Yaro Bai San Wuta Ba… Duk marar kunyar da ke wannan ja’irancin, ya na wasa da wuta ne, bai san za ta ƙona shi ba. Ko dai ya bari ko kuma ya fuskanci fushin sarkin yaƙi.”
Alh. Hamisu Lamido Iyan-Tama mutum ne mai ƙima da mutunci, wanda mutane ke mutuntawa.