A DAREN jiya Asabar Allah ya yi wa jarumar Kannywood Alkharina Ahmad rasuwa a gidan su da ke Ƙofar Durɓi, Katsina.
Jarumar, mai kimanin shekaru 40, ta rasu ne bayan ta yi fama da rashin lafiya, wanda hakan ya sa ta koma gidan su da ke Ƙofar Durɓi don samun kulawar magabata.
An yi jana’izar ta a safiyar yau Lahadi.
Alkharina jaruma ce da ta shafe sama da shekaru 15 a cikin harkar fim, inda ta yi finafinai da dama, waɗanda suka haɗa da ‘Kamanni’ da ‘Mafarki’.

Marigayiyar ta taɓa yin aure har ta samu haihuwar ɗa namiji wanda a yanzu haka yana nan da ran sa.
Allah ya jiƙan ta, ya yafe mata kurakuran ta, amin.