JARUMIN barkwanci a Kannywood, Ali Muhammad Idris, wato Maɗagwal ko Ali Artwork, ya yi wa Allah godiya a kan babbar kyautar da ya yi masa ta ɗa namiji.
Idan kun tuna, matar sa Hauwa’u Muhammad Bello ta haihu da asubahin jiya a Asibitin Koyarwa na Barau Dikko da ke Kaduna.
Mujallar Fim ta ba ku labarin hatsaniyar da ta tashi tsakanin jarumin da surukan sa a kan ƙin amincewar da ya yi na a yi mata aiki a fitar da ɗan.

Mun faɗa maku cewa Ali ya je asibitin jiya da safe inda ya yi wa ɗan sa Muhammad Aryan huɗuba, amma likitoci sun ba da umarnin kada a bar shi ya ƙara zuwa saboda kada a ci gaba da rigimar.
Ɗazu dai Ali ya aiko wa da mujallar Fim saƙo inda ya yi godiya ga Allah a kan wannan abin farin ciki da ya same shi na haihuwar ɗan sa na fari.
Ya haɗo da hotunan da ya yi da ɗan nasa a asibitin.
A cikin saƙon, wanda kuma ya wallafa shi a Facebook, Ali Artwork ya ce, “Alhamdu lillah. Masha Allah. Mu na godiya ga Allah subhanahu wa ta’ala da ya mana wannan babbar kyauta da babu mai ba ka irin ta sai Ubangijin sammai da ƙassai, Allahu wahidul ƙahharu.
“Allah mun gode maka da wannan ni’ima da ka mana. Allah ka ba wa mata ta Hauwa’u lafiya da ƙarfin jiki. Allah ka albarkaci wannan yaro, ka ba shi kariya. Allah ka sa mahaddacin Alƙur’ani ne. Allah ka ba shi ikon yin biyayya ga iyayen sa. Allah ka ba shi ikon riƙe gaskiya da amana a duk inda ya ke. Allah ka ba shi ikon riƙo da addinin Musulunci, ka kuma ba shi ikon bin koyarwar fiyayyen halitta shugaban mu, Annabi Muhammadu (S.A.W.).”

Ya ƙare da cewa da Turanci, “Welcome to the world my son, Muhammad Aryan Ali Artwork (Maɗagwal).”
To, amin ya Allah.
Allah Ya Raya Shi Amin