JARUMIN Kannywood, Isma’il Ishaq Koli, shi ma dai ba za a bar shi a baya ba a wannan shekara, domin kuwa zai shiga sabuwar shekarar 2024 da sabuwar amarya.
Za a ɗaura auren sa da sahibar sa, Nasira Zakariyya Aliyu, a ranar Juma’a, 29 ga Disamba, 2023 da misalin ƙarfe 1:00, a masallacin Juma’a na Government Collage da ke Kurmin Mashi, Kaduna.
A cikin katin gayyatar, Koli ya ce, “Wannan aure ya na nufin wani muhimmin cigaba a gare ni.
“Zan yi farin ciki in ka samu damar halartar bikin wannan rana ta musamman.
“Duk dalilin da ya sa ba ka samu halarta ba, don Allah ka saka mu a cikin addu’o’in ka da mu ka hau wannan sabuwar tafiya. Saƙonnin fatan alkhairin ku babban abu ne a gare mu. Za mu yi farin ciki da addu’o’in ku.”
To, Allah ya kai mu da rai da lafiya.