• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, October 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Kasafin kuɗin Ma’aikatar Yaɗa Labarai na 2024 ya yi kaɗan, a ƙara shi, inji Majalisar Dattawa

by DAGA WAKILI
December 13, 2023
in Nijeriya
0
Kasafin kuɗin Ma’aikatar Yaɗa Labarai na 2024 ya yi kaɗan, a ƙara shi, inji Majalisar Dattawa

Sanata Godswill Akpabio, Shugaban Majalisar Dattawa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

KWAMITIN Majalisar Dattawa Mai Lura da Harkokin Yaɗa Labarai ya nuna rashin amincewa dangane da ƙarancin kuɗaɗen da kwamitin ya ce Gwamnatin Tarayya ta ware wa Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai a Kasafin 2024.

Shugaban kwamitin, Sanata Kenneth Eze, shi ne ya nuna hakan a lokacin da Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana a gaban kwamitin domin ya kare kasafin ma’aikatar sa a ranar Talata a Abuja.

Eze ya ce, “Haba jama’a, ai waɗannan kuɗaɗe cikin cokali bai yiwuwa a ce da su kaɗai za a yi amfani har a samu biyan buƙatar yaɗa manufofin ƙasar mu. Muddin waɗannan kuɗaɗen ne aka ware wa wannan ma’aikatar, to ba inda za mu iya cimma gaci. Ta yaya za a iya wayar da kan jama’a ta hanyar yaɗa labarai da kyawawan manufofi da waɗannan kuɗaɗe ƙalilan?

“Ma’aikatar Yaɗa Labarai fa wuri ne mai muhimmancin da wajibi ne a yi wa wurin riƙon kazar kuku, ba riƙon sakainar kashi ba. Ina magana idan har fa ana so a samu biyan buƙatar samun nasarar Ajandar Daidaita Nijeriya da mu ke magana, to dole ma’aikatar yaɗa labarai ce a sahun gaba.

“Wannan ma’aikata ce za ta kasance mai haska wa ƙasar nan fitilar kyawawan ɗabi’un jama’ar ta, kuma akwai wawakeken giɓi tsakanin gwamnati da jama’a, wanda wannan ma’aikatar ce tilas za ta iya cike giɓin.”

Sanatan ya ƙara da cewa, “Na duba a cikin kasafin, amma ban ga ko sisi da za a kashe a Hukumar Kula da Jaridu ba, ban ga Hukumar APCON ba, kuma ban ga kasafin wasu hukumomin da ke ƙarƙashin wannan ma’aikata ba.

“Shin gwamnati na so ta shaida mana cewa an rushe waɗannan hukumomin kenan, yadda har za su iya aiki ko ba ma’aikata a cikin su?

“Wa zai biya albashin su? Watannin baya ba da daɗewa ba fa aka naɗa wa hukumomin sababbin Manyan Daraktoci da Manyan Sakatarori.

“Mai Girma Minista, wannan batu ne fa mai muhimmanci ga wannan kwamiti, kuma tabbas za mu duba wannan lamari.”

A nasa bayanin, Minista Idris ya shaida wa sanatocin cewa za a ƙaddamar da Shirin Cusa Ɗa’a, Kishin Ƙasa da Kyawawan Ɗabi’u (NVC) cikin 2024.

Ya ce akwai gagarumin aiki a gaban ma’aikatar sa wajen tabbatar da samun nasarar shirin cusa ɗa’a da kishin ƙasa, wanda naira biliyan 1 da aka ware wa ma’aikatar sa, a matsayin kuɗaɗen gudanar da manyan ayyuka, ko kusa ba za su wadata ba.

Loading

Previous Post

Jarumin Kannywood Isma’il Koli zai angwance da Nasira

Next Post

Gwamnan Zamfara ya jajanta wa al’ummar yankunan Zurmi, Maru, Tsafe da kewaye

Related Posts

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa
Nijeriya

Yadda CBN ke tallabe da tattalin arzikin Nijeriya, yayin sa farashin ɗanyen mai ke faɗuwar-‘yan-bori a kasuwa

November 7, 2025
Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji
Nijeriya

Shirin ƙarfafa jari: CBN ya shawarci bankuna marasa ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

November 2, 2025
Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba
Nijeriya

Bankin CBN ya yunƙuro: Naira ta hana dala numfashi mai ƙarfi a ƙarshen Oktoba

November 2, 2025
Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje
Nijeriya

Bankin CBN ya ƙaryata ƙazafin sayar wa manyan dillalan mai dala biliyan 1.259 domin su shigo da fetur daga waje

October 29, 2025
Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai
Nijeriya

Tinubu ya yi adalci ga dukkan yankunan Nijeriya – Ministan Yaɗa Labarai

August 31, 2025
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar da Sababbin Cibiyoyin Maganin Ciwon Daji

July 24, 2025
Next Post
Gwamnan Zamfara ya jajanta wa al’ummar yankunan Zurmi, Maru, Tsafe da kewaye

Gwamnan Zamfara ya jajanta wa al'ummar yankunan Zurmi, Maru, Tsafe da kewaye

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!