INNA LILLAHI wa inna ilaihir raji’un! Allah ya yi wa mahaifin fitaccen jarumin Kannywood ɗin nan da ke birnin Zariya, Mukhtar Hassan SS, rasuwa.
Malam Hassan Umar ya rasu a yau Litinin, 4 ga Afrilu, 2022 a gidan sa mai lamba 132 da ke tagwayen masallaci, Sabon Layi, unguwar Jushi, Zariya, bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Marigayin mai kimanin shekara 80 a duniya ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya uku.

An yi masa sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, sa’annan aka kai shi gidan sa na gaskiya da ke maƙabartar Nagoyi, dab da iyakar Ban Zazzau.
Allah ya jiƙan shi da rahama, amin summa amin.