FURODUSA a Kannywood, Usman Alhassan, wanda aka fi sani da Usman Aibu, ya bayyana harkar fim da cewa wata masana’anta ce da ke da ɗimbin arziki a ɓangarori da dama. Ya ce duk inda ka mayar da hankalin ka, to za ka samu alheri a cikin sa.
A wata tattaunawa da ya yi da mujallar Fim, Usman ya fara bayani ne da tarihin zaman sa a cikin masana’antar tsawon lokaci.
Ya ce: “Ni na shigo wannan masana’anta ta fim tun a 2000; ka ga a yanzu na shafe sama da shekaru ashirin kenan. Kuma a lokacin na fara ne da matsayin yaro a kamfanin Sarauniya da ke Sabon Titin Mandawari a wajen maigida na, Bala Ahmed, wanda shi ne ya koya mini wannan sana’a.
“Cikin waɗanda mu ka zauna da su akwai irin su Falalu A. Ɗorayi, Abubakar Lulu, da sauran su.
“Farko dai na shigo harkar ne da niyyar yin aktin, daga ƙarshe kuma sai na ga abin ba zai yiwu ba. Sai na rikiɗe na koma furodusa, wanda na fara fim nawa na kai na mai suna ‘Aibu’ wanda daga nan na samu sunan da a ke kira na Usman Aibu.
“To, tun daga wannan lokacin dai mu na cikin wannan masana’anta mu na ta faɗi-tashi, ba mu daina ba.
“Sannan bayan wannan na yi finafinai da yawan da ba za su lissafu ba musamman lokacin da na juya harka ta zuwa finafinan barkwanci wanda a cikin su na yi fim kamar ‘Ibro Ɗan Siyasa’, ‘Ibro Ɗan Sabga’, ‘Ibro Gari Ya Yi Zafi,’ da sauran su.
“To har zuwa yanzu dai mu na cikin masana’antar, ba mu fita ba, saboda ita masana’anta ta na da faɗin gaske wadda idan ka maƙale a wani lokon sai ka yi shekara da shekaru ba ka haɗu da wani ba, kuma kowa da ka gani cin arzikin ta ya ke yi, domin masana’anta ce mai ɗimbin arziki, duk ta inda ka raɓe za ka samu arzikin.”
To shin me Usman Aibu zai ce game da sauyin da aka samu a industiri? Kuma yaya sauyin ya shafe shi?
Amsa: “A yanzu da harka ta juya to sai na ga ba zan bari a tafi babu ni ba tunda ba ni da wata sana’a da ta kai girman fim. Don haka a yanzu da aka juya ake yin finafinai masu dogon zango don haka sai mu ka dage da ni da maigida na Bala Ahmed mu ke samar da finafinai a wannan lokacin don ya zama ba a bar mu a baya ba, wanda a yanzu mu na da fim ɗin da mu ka fitar mai suna ‘Ɗayan Biyu’, wanda fim ne da ya ke cike da abubuwan mamaki da kuma al’ajabi na daga abubuwan da su ke faruwa a yanzu na gurɓacewar matasa. Sai kuma na biyun da shi ma za mu fitar da shi, sunan sa ‘Mai Ƙosai’.
“Don haka mutane su tsaya su jajirce wajen abin da su ka saka a gaba, wanda hakan ne ya ke sa a kai ga samun nasara.
“Saboda haka mu saka ƙoƙarin cigaba, domin ta hakan ne zai kawo bunƙasar masana’antar Kannywood baki ɗaya.”