MALAM Khalid Imam ya na ɗaya daga cikin matasa ‘yan asalin arewacin Nijeriya waɗanda su ka bayar da gudunmawa ga cigaban al’umma ta hanyar rubutu. Kuma a fagen rubutu, shi ba ya da gefe, domin kuwa ya ciri tuta a fagen rubutun zube, wasan kwaikwayo, waƙoƙi da kuma maƙaloli a cikin jaridu, sannan ya na rubutun ne da Hausa da Turanci.
Khalid, wanda malamin makaranta ne a Kano, ya rubuta littattafai waɗanda su ka yi fice, wasu ma su ka ci gasar rubutu.
Mujallar Fim ta nemi ji tarihin sa da irin gwagwarmayar da ya sha a fagen rubutu daga bakin sa, inda ya fara da bayyana cewa: “Ni an haife ni a garin Kano, cikin unguwar Yakasai, a shekarar 1973.
“Kuma tun a gida na fara karatu na Arabiyya, sannan na ci gaba da karatun boko har zuwa mataki na jami’a, wanda a yanzu ina kan yin digiri na na biyu.”
A kan yadda ya fara rubutu kuwa, cewa ya yi, “Tun ina sakandire na ke da sha’awar rubutu saboda yawan karance-karance da na ke yi na jarida, musamman rubutun da Ibrahim Sheme ya ke yi a jaridar ‘Weekly Trust’, wanda shafin sa ya zama abin karantawa a gare ni duk sati, don haka ya saka mini son rubutu.
“A kan haka na fara rubutu wanda har ta kai ga an wallafa wasu rubutun da na yi a littattafai da maƙalun ilimi a ƙasashen duniya kamar su Amurka da Jamus da Indiya da Poland.
“Amma dai a fagen rubutu an fi sani na da rubutun wasan kwaikwayo da waƙa, wanda a sanadiyyar hakan ne na zama zakara a fagen gasussukan wasannin kwaikwayo har sau biyu.”
Da mu ka tambayi Malam Khalid babbar nasarar da ya ke ganin ya samu a wannan aiki na fasaha da ya sa a gaba, sai ya amsa da cewa: “Babbar nasarar da na samu ita ce a shekarar 2014 ɗalibai na mata masu koyon rubutu a ƙarƙashi na su ka kafa tarihi na zama ɗalibai na farko a Nijeriya da su ka lashe kyaututtukan zinariya da azurfa da tagulla da aka tanada a fagen gasar ɗaliban sakandire na rubuta waƙe da harshen Turanci ta ƙasa da ƙasa ta ‘Korea-Nigeria Poetry Feast’, wadda aka gudanar a can birnin tarayya, Abuja.”
Khalid Imam memba ne a kwamitin ƙoli na Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA) wanda ƙungiyar ta kafa don koya wa ɗaliban sakandire dabarun rubutu kuma aka ɗora masa alhakin tsarawa da kulawa da dukkan ayyukan kwamitin a Jihar Katsina.
Sakamakon nasarar aikin kwamitin ya sa aka buga cikakken littafi wanda ya ƙunshi rubutun ɗalibai ‘yan sakandire zalla mai suna ‘Beyond Limits’ a shekarar 2013.
Baya ga haka, Khalid ne shugaban kamfanin wallafa na ‘Whetstone Arts &Translation Services’, kuma Edita ne a shafukan adabi na mujallar Turanci ta wata-wata mai suna ‘Platform’.
Littattafan da ya rubuta su ne: ‘Justice, Fairness and the Quest for Engalitarian Societies’, ‘The Amigo Sisters’, ‘Sodangi’, ‘The Song of San Kano’, ‘Letter to My Students’, sai kuma littafin haɗin gwiwa mai suna ‘A Clan of Madmen’.
Babban littafin sa mafi shahara a yanzu shi ne ‘Kundin Hirarrakin Bukar Usman’.
Saboda gudunmawar sa ga al’umma da ciyar da ƙasa gaba, ƙungiyar Inuwar Jama’ar Kano ta karrama shi da lambar yabo a shekarar 2011. Haka kuma an ba shi wasu lambobin yabon daga jaridu da hukumomi da ƙungiyoyi masu yawan gaske a Nijeriya da ƙasashen waje.
Don haka a yanzu dai idan ana maganar ‘yan Nijeriya da su ka bayar da gagarumar gudunmawa ga cigaban adabin nahiyar Afrika, to tabbas Malam Khalid Imam ya na cikin su.