HAƘIƘA duk wanda ya saurari ko ya karanta hirar tsohuwar jarumar Kannywood Hajiya Hauwa Bello Ado Bayero, wadda aka fi sani da Maijidda Ibrahim, dole ya kaɗu, kuma ya tausaya mata.
Tsawon shekaru Maijidda ta jure irin wannan cin mutunci da cin kashin da ake yi mata da ‘ya’yan ta saboda ita ‘yar fim ce, amma hakan bai sa ta bar gidan auren ta ba.
Akwai da dama daga cikin ‘yan fim mata da ke fuskantar makamancin abin da ke faruwa da ita, kuma su ma sun jure sun zauna, wasu kuma ba su da haƙurin da za su zauna ɗin.
Wasu ‘yan fim tun daga lokacin da aka fara maganar auren su ake fara samun matsaloli daga ɓangarori da dama na iyaye da ‘yan’uwa.
Ba a kan mata kawai matsalar ta tsaya ba, har da maza. Akwai gidan da idan ka je neman aure, da an ji kai ɗan fim ne ko mawaƙi sai a dakatar da kai, kuma maganar kenan, ba za a ba ka ba, sai dai idan ita yarinyar ta kafe a kan lallai sai ta aure ka.
Akwai jarumai mata da dama da ke son aure, amma ire-iren waɗannan matsalolin ke hana auren. Sai ka ji ana “ai wane ‘yar fim zai aura”, ko kuma “wance ɗan fim za ta aura”. Daga nan sai ƙananan maganganu su taso, “ai ‘yar iska ce” ko kuma “ɗan iska ne”, “mutanen da ke rayuwa a otal”, da dai sauran su.
A yau ‘yan fim mata sun koma saka kowane irin kaya, walau a fim ko kuma a zahiri, musamman a soshiyal midiya. Wannan ya sa dole a riƙa yi masu kallon ‘yan iska ko marasa tarbiyya, wanda a zahiri idan har ka yi mu’amala da su za ka gane ba haka ba ne
Abin mamaki, wasu daga cikin mutanen da ke zagin ‘yan fim masoyan ‘yan fim ne sosai. Su na kallon finafinan su, har su na da gwanaye a cikin su, sai ma ka ga su da kan su su na neman su da soyayya ko ka ji su na alfahari da cewa “na san wane ko wance”, amma da zarar ‘ya’yan su sun zo masu da maganar auren ‘yan fim, sai su ƙeƙasa ƙasa su ce, “Allah wadaran naka ya lalace, ba zai yiwu ba.”
Me ya sa hakan ke faruwa? Laifin ‘yan fim ɗin ne ko na waye?
To, magana ta gaskiya ana iya cewa laifin ‘yan fim ne. Dalili kuwa shi ne rashin nuna halin ko-in-kula da damuwa da irin waɗannan abubuwa da ke faruwa da su, musamman idan sun zo aure ko kuma a gidan aure.
Idan aka yi duba da irin yadda ake kallon ‘yan fim da mutunci a shekarun baya, a yanzu ba a yi masu irin wannan kallon. A yau ‘yan fim mata sun koma saka kowane irin kaya, walau a fim ko kuma a zahiri, musamman a soshiyal midiya. Wannan ya sa dole a riƙa yi masu kallon ‘yan iska ko marasa tarbiyya, wanda a zahiri idan har ka yi mu’amala da su za ka gane ba haka ba ne. Sai dai kuma da ma masu iya magana sun ce yanayin shigar ka, yanayin yadda za a fassara ka.
Tsohuwar fitacciyar jarumar nan Halima Adamu Yahaya ta taɓa aiko da saƙo a filin wasiƙu na mujallar Fim inda ta ja hankali da kuma jan kunnen ƙannen ta mata ‘yan fim da su riƙa duba rayuwar su a gaba. Ta ce, “A lokacin mu kayan da mu ke sakawa a fim ya bambanta da irin waɗanda su ke sakawa yanzu. A lokacin, kaya za ki saka da zai rufe miki ko’ina na jikin ki, sannan ba ya nuna surar jikin ki.” Ta ce amma kuma duk da haka idan ‘ya’yan su su ka je makaranta ana tsangwamar su da cewa ‘ya’yan ‘yan fim ne ‘yan iska, da sauran su. Halima ta nuna wa jarumai mata da su kiyaye da irin shigar da su ke yi da kuma yanayin yadda su ke gudanar da rayuwar su, don kare mutuncin su.
Hirar jaruma Maijidda Ibrahim ya tuna mani da wannan wasiƙa ta Halima Adamu Yahaya. Sai kuma ga shi maganar da ta yi ta yi daidai da abin da ya faru tsakanin Maijidda da dangin mijin ta.
Masu iya magana dai sun ce gani ga wane, ya ishi wane tsoron Allah! A yau jarumai mata ba su damu da duk irin zagi da cin mutuncin da ake yi masu ba. Za su saka kaya irin yadda su ke so, su yi kitso tare da ƙarin gashi duk da yake su na sane da cewa haramun ne. Haka kuma a wannan zamanin da soshiyal midiya ta zama ruwan dare game duniya, su kan yi abubuwan da za su zubar masu da mutunci da ma masana’antar baki ɗaya. Ta wani ɓangaren ma nan ne wurin cin mutuncin juna idan wani abu ya haɗo su da juna.
A tsawon shekara 23 mujallar Fim ta sha faɗakarwa tare da wayar da kan ‘yan fim game da abubuwan da za su taɓa mutuncin su da masana’antar su, amma kuma ƙalilan daga cikin su ne ke amfani da shawarwarin. Wasu gani su ke yi a haka ɓata masu suna ake yi.
Ya kamata wannan abu da ya faru ga Maijidda Ibrahim ya zama izina ga sauran ‘yan fim mata.
Mu na yi wa Maijidda fatan Allah ya yaye mata wannan musiba da ta ke ciki ita ‘ya’yan ta.
Hakika maganar halima adamu gaskiyane domin kuwa lokacin da take sana’ar fim sun kasance suna isar da sakone me alaka da al adar hausa da kuma kare martabar addinin musulunci. Amma yanzu zakaga gabada cikin kashi 100 duk 70 suna koyi ne da indiya da yahudawa 30 ne kawai masu isar da sako irin na malan bahaushe. Kaga yarinya tasa wando da riga irin na yan iska duk alaurata a bayyane tana rawa da wani kato ko ina aka samo haka a al adar hausa, duk da yake laifin masu tace fim ne kuma kusa duk da ku bakwa fitowa a fim tun da gomnati tasaku wakilai domin kula da abunda zai bata al adarmu da addinin mu to sai Allah ya kamaku. Allah mustapha waye domin kuwa da za a samu masu kishi irinsa da kannywood ta samu gyara. shawarata gareki maijiddah kirike mijin komin wuya komin domin aure ibadane kuma aljannarki na karkashin miji kada kibari yan matan kannywood su hure maki kunne kirabu da mijinki don kinga suna sayen motoci na miliyoya duk wadda bata tuba ta daina aikin fasikanci ba to tasan makomarta