SAU da yawa ‘yan fim su na shiga cikin matsaloli da masoyan su, amma ta fitaccen jarumi Zahraddeen Sani ta sha bamban.
Shi a nasa ɓangaren, Allah Ya haɗa shi da wata mata ne mai son shi wadda bayan sun fara mu’amala ta tsawon kwana huɗu sai abu ya juye, magana ta kai ga zuwa kotu.
Matar, mai suna Adama Muhammad, ta sha alwashin sai ta auri jarumin ko ta halin ƙaƙa.
A ranar Litinin, 30 ga Satumba, 2019 aka duƙa shari’a a wata kotun Musulunci da ke Titin Rock a Tudun Nufawa, Kaduna, inda ta kai shi ƙara a kan cewar ya yi mata alƙawarin zai aure ta amma daga bisani sai ya ƙi.
Da aka aka gabatar da ƙarar, Adama ta ce ta yi tuhumar Zahraddeen Sani
da wasu abokan sa biyu, wato Ishaq Sani da Malam Turaki, a kan saɓa alƙawarin aure.
Lauyan waɗanda ake ƙara, A.A. Liman, ya tashi ya gabatar da kan sa tare da bada haƙurin rashin zuwan Zahraddeen, ya ce jarumin ya wayi gari ‘yar sa ba ta da lafiya, sun garzaya zuwa asibiti.
Ya buƙaci kotu da ta ba su dama don su gabatar da hujjoji game da ƙarar, domin su ma waɗanda ake ƙarar sun riga sun shigar da ƙara a wata kotun kafin ita Adama ta kawo tata ƙarar a nan.
Lauyan ya yi nuni da cewa a domin hakan babu wata kotu da za ta iya sauraren ƙarar Adama har sai an gama da ta su Zahraddeen ɗin.
Liman ya yi wa kotu alƙawarin zai gabatar da waɗannan hujjojin waɗanda ya ce an buga su a wasu jaridu a zama na gaba.
Jin haka, sai alƙalin ya amince, amma ya buƙaci lauyan da ya kawo masu kwafen dukkan jaridun a cikin awa 24. Daga nan ya sallame su.
A ranar Laraba, 2 ga Oktoba, 2019 aka shiga kotun majistare da ke NDA, Badarawa, Kaduna, don sauraren ƙarar da Zahraddeen ya shigar a kan tuhumar Adama na ɓata masa suna.
Jarumin da Adama sun halarci kotun da kan su.
An kira ƙarar ta su da misalin ƙarfe 10:30 na safe, inda aka gabatar da su bayan lauyoyin su sun gabatar da kan su.
Lauyan Zahraddeen ya miƙe ya yi wa alƙali bayanin yadda su ka yi da lauyan wadda ake ƙara, ya ce lauyan nata ya nemi da su koma gida a yi sasanci.
Shi kuma lauyan nata sai ya miƙe ya ce shi fa babu ruwan sa da kes ɗin nasu.
Jin haka sai lauyan Zahraddeen ya ce to babu komai, in su na so ne a zauna a saurari ƙarar sai a ƙara sa masu rana da za a saurari ƙarar in har ba a sasanta su a gida ba.
Alƙalin kotun ta ɗage ci gaba da sauraren ƙarar zuwa ranar 23 ga Oktoba, 2019.
Bayan an fito daga kotun, wakilin mujallar Fim ya ji Adama na faɗin: “Wallahi ko uwa ta ba ta isa ta sa a yi wannan sasancin ba!”
Da wakilin namu ya nemi jin ta bakin ta kan al’amarin, sai ta ƙi.
Shi kuwa Zahraddeen, ya yi wa mujallar Fim bayanin yadda ya haɗu da Adama har abin ya kai su ga kotu. Ya ce, “Akwai wata mata mai sama da shekara hamsin ta shigo rayuwa ta a matsayin ita fan ɗi na ce, ta na kallon finafinai na.
“Kwana huɗu da haɗuwa na da ita na lura akwai wani abu na rashin gaskiya ko rashin iya mu’amala a tare da ita. Haka ta nemi shiga jiki na, na zame.
“Ta rinƙa bin abokai na su ba ni haƙuri, ta na so mu yi soyayya, za ta aure ni, ita P.A. ɗin shugaban Majalisar Dattawa ne, ita budurwar Nasiru El-Rufa’i ce, za ta iya samo mana kwangila, za ta sa a ba mu man fetur, ta san Ibrahim Badamasi Babangida, saurayin ta ne!
“Kuma a ko da yaushe ta ɗauki waya ta ce ta na magana da su ne.
“Wata rana ta gan ni da wata fan ɗi ta mu na magana, ta zo ta nemi ta ci mani mutunci a idon mutane, ni kuma na ga ba zan iya ba, na kai ta kotu.
“Aka neme ta, ta ƙi zuwa; ita ma sai ta shigar da ƙara, inda aka ce lauya na ya kawo hujjoji a cikin awa 24.
“Ni yanzu ban san wani maganar sasanci tsakani na da ita ba, sai na zauna da lauya na tukuna, domin wannan ɓata suna da ta ke neman ta yi, saboda ni ɗan fim ne, za a zubar min da mutunci saboda ina harkar fim, sai an sa duniya ta ƙi ni da sauran su.
“Saboda haka komai na gaban kotu. Mu na jira mu ga me kotu za ta yanke tsakani na da wannan matar da ta zo ta ce lallai sai na aure ta, har ta kai ƙara na kotu.
“Da ma ni na riga na kai ƙarar ta kotun majistare, kafin ita ta kai ni.”
Da wakilin mu ya tambayi jarumin ko akwai wani abu da ya haɗa shi da ita bayan waccan magana ta sai ya aure ta, misali kuɗi ko wani abu makamancin haka da ta ke faɗin sai ta ɓata masa suna, sai ya ce, “Ka san mu mutane ne na jama’a. Za ka iya haɗuwa da mutum a matsayin masoyin ka, saboda ka na fim ka na burge shi, ko da cingam ko suwit ya saya ya ba ka, wannan ba wani abu ba ne, ya yi maka ne saboda soyayya.
“Wani kuma zai iya zuwa ya ce hoto ya ke so ya yi da kai.
“Ni wannan mata babu wani abu da ya shiga tsakani na da ita face neman ɓata mani suna. Ni kuma ba zan yarda ba, sai na ga inda ƙarfi na ya ƙare a kan wannan al’amari.
“Su kuma abokai na da sunan su ya shigo ciki, wato Ishaq da Turaki, laifin su don sun ƙi shiga tsakani na da ita su sasanta mu in ci gaba da kula ta, domin tun da na gano ta, na daina kula ta.
“Yanzu ita a dole sai na aure ta ko ta ɓata min suna!”