• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, June 4, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Magana ba ta kada min gaba, inji Kabir Bahaushe MC

by DAGA ABBA MUHAMMAD
September 1, 2021
in Ranar Murna
0
Magana ba ta kada min gaba, inji Kabir Bahaushe MC
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

KABIR Sa’idu Bahaushe matashi ne mai gabatarwa a wurin biki ko taron ƙara wa juna sani da sauran tarurrukan jama’a, wato sanƙira ko ‘master of ceremony’ (MC) a Turance. 

Kabir Bahaushe ba ɓoyayye ba ne, musamman ma dai a Jihar Katsina. Haka kuma ya yi fice a soshiyal midiya.

Bugu da ƙari, santalelen saurayi ne, mai ladabi da biyayya ga na gaba da shi. Wannan ne ma ya sa ya taka matsayin da ya ke a kai yanzu.

Ba kasafai ake samun Hausawa su na yin sana’ar MC ba, amma Bahaushe ya riƙe wannan sana’ar da gasken gaske.

Mujallar Fim ta tattauna da shi game da rayuwar sa, yadda aka yi ya fara MC, alaƙar sa da ‘yan fim, da kuma irin ƙalubale da nasarorin da ya samu a cikin harkar, kamar haka:

FIM: Menene tarihin rayuwar ka a taƙaice?

KABIR BAHAUSHE: Alhamdu lillah! Suna na Kabir Sa’idu Bahaushe Ɗanɗagoro, inkiya MC Bahaushe.An haife ni a Ɗanɗagoro (a garin Katsina). Na yi firamare na a ‘Ɗanɗagoro Model Primary School’, na kuma yi sakandare a GRBSS, Ɓatagarawa. Na yi digiri na ɗaya kan darussan koyar da Hausa a Jami’ar Umaru Musa Yar’Adua, inda yanzu kuma na ke digiri na biyu kan Adabin Hausa a jami’ar. 

Ina aiki da gidan rediyon Vision FM, Katsina, a matsayin mai shiryawa da gabatar da shirye-shirye. Sannan kuma ina gabatar da sana’ar MC da taɓa harkokin kasuwanci.

FIM: Ya aka yi ka tsinci kan ka a aikin MC?

KABIR BAHAUSHE: Na tsinci kai na ne cikin wannan harkar tun ina jami’a, a digiri na farko, don gaskiya na yi siyasar makaranta sosai, dalilin da ya gogar da ni na iya yin magana a bainar jama’a, ta yadda idan mu ka je gangamin neman zaɓe sai a ba ni dama na riƙa gabatarwa. Daga nan na soma.

Ana haka, na riƙa bin wani DJ Amo da Rabi’u M. Yaro har na fahimci yadda su ke yi, kuma sun ba ni dama gaskiya. Daga nan, wata rana za a yi jarabawa a jami’a, ba ni da ko sisi, wani gida su ka nemi na yi masu aiki, su ka biya ni da gwaɓi. Na ɗauki cewa duk abin da zai sa na samu kuɗi haka ba abu ne da zan yi wasa da shi ba, sai na ɗauke shi sana’a!

Kabir Bahaushe a bakin aiki a wani taro a makarantar sakandaren ‘yanmata ta Sandamu a Jihar Katsina

FIM: Mecece ma’anar ‘MC’ a Turance da kuma Hausa?

KABIR BAHAUSHE: Ma’anar ‘MC’ dai a taƙaice shi ne ‘master of ceremony’ – mai gabatarwa da jagorancin gudanar da taro, wato ba ma magana ba kaɗai kenan, shiryawa da daidaitawa da sanarwa da sanyawa da dakatarwa. Da Hausa kuwa mai gabatar da taro, kamar yadda ake gabatar da shiri a rediyo kenan ko talbijin.

FIM: Me ya sa ka zaɓi yin MC?

KABIR BAHAUSHE: Na zaɓi na yi MC ne don in dogara da kai na, kuma na natsu a zuciya ta cewa magana ba ta kada min gaba. To kuwa tunda don lada ake yin sallah, sai na ga ai ana samun kuɗaɗen shiga; kuma idan na yi jama’a na jin daɗi, su ƙara kira na.

FIM: Kafin ka fara MC, wace sana’a ka ke yi?

KABIR BAHAUSHE: Kafin na fara MC na yi gwagwarmaya tun kafin shiga jami’a; na yi kanikancin babbar mota da saida jaridu, saboda kanikanci gado na yi.

FIM: Waɗanne wurare aikin MC ya kai ka?

KABIR BAHAUSHE: Aikin MC ya kai ni wuraren da ban taɓa zuwa ba, ko kuma ko na je ba sana’a ta kai ni ba. Amma na je Jami’ar MAAUN na jagoranci bikin yaye ɗalibai a Jamhuriyar Nijar, na je Abuja aiki, da Maiduguri da Kaduna da Sakkwato da Kebbi da Zamfara da Kano da ƙananan hukumomi da dama na Jihar Katsinar mu.

FIM: Waɗanne irin ƙalubale ka fuskanta game da aikin MC?

KABIR BAHAUSHE: Ƙalubale dole ne ya zo a cikin wannan aikin, amma dai ni gaskiya Allah ya sauwaƙe min sosai domin duk wanda ya san ni ya san ni da tsari sosai da sosai. Sai dai ta fuskar mawaƙa da su ke ganin kamar ba a ba su dama; ni kuma idan ba a gayyace ka taro ka zo ba, da ka zo ba ni ba ka dama. 

Akwai wata rana da wani mawaƙin gargajiya ya zo bikin mawaƙa na gala na naɗin sarauta. Ban ma san ya zo ba sam. Ashe ya ƙullace ni. Sai wani yaron sa ya rugo da gudu, sai ya ce da ni na ankare na kauce jami’an tsaro su ka kama shi. 

Sai kuma batun a yi ta cewa mutane su saurara ko su zauna su daina ɗaukar hoto amma ba su bari, duk da har na ma saba mu na yin hikimomin da ake gyara hakan aƙalla.

Kabir Bahaushe tare da Ado Gwanja su na gabatarwa a wani bikin aure

FIM: Waɗanne irin nasarori ka samu a aikin MC?

KABIR BAHAUSHE: Motar da na fara hawa a duniya, Alhaji Ɗahiru Mangal ya ba ni ita kyauta saboda na yi MC. Cikin sa kuma na ke yin kasuwanci da ci da sha da sutura. An yi hira da ni a kafafen yaɗa labarai da dama. Na san mutanen da ban isa a da na yi hulɗa da su ba. Na yi gaba-da-gaba da gwamnoni da sarakuna da hamshaƙai da yawa. An ba ni kyautar kujerar Makka, amma saboda korona ban je ba. Ka ga ai nasarar ma ta wuce ƙirgawa! Ina cikin tafiya, sai in ji yaro a wani lungu ko wani waje ya ce, “MC!” (dariya)

FIM: Bayan MC, kai marubuci ne. Har yanzu ka na rubutu?

KABIR BAHAUSHE: E, gaskiya ina rubutu, amma ba fa na littafi ko soyayya ba. Allah ya yi ni da son karatun mujallu da jaridu, kuma ka san na saida jaridu. Wannan damar ce na samu na fara rubutu a jaridu har na zama wakilin mujallun Al-Irshaad da Muryar Arewa, na kuma riƙa jagorantar rubutu a shafukan su (columnist) kan addini da soyayya.

Har yanzu na kan yi rubutu a jaridu a buga, da kafafen sadarwar zamani, don gaskiya ina so da yawa. Ka san idan kolo ya samu allo! (dariya)

FIM: Me ya sa ake kiran ka ‘Bahaushe’?

KABIR BAHAUSHE: Ana ce min Bahaushe ne domin son da na ke yi wa harshen Hausa. A jami’a ne, a ajin mu na ɗaya da ke da yawan ɗalibai daga sassa da dama na ke yawan amsa tambayoyin wani shehin malamin mu, Farfesa Bashir Aliyu Sallau, sai wani Salisu da ya gan ni sai ya ce, “Bahaushe!” har mutane su ka ɗauka, aka yi ta faɗi. Da na zo takara a aji biyu sai na sanya sunan ‘Bahaushen’, don shi aka fi sani sosai. Ai daga nan har ko’ina sai aka yi ta amfani da shi, har rediyo cewa na ke, “Suna na Kabir Sa’idu Bahaushe”.

Kabir Bahaushe na gabatar da amarya da ango a wani biki a Kaduna

FIM: Ka na da iyali?

KABIR BAHAUSHE: Gaskiya ne, ina da iyali; saurayi kama ta ba iyali ai tsarin bai yi kyau ba! Ina da mata ɗaya da ɗa ɗaya, sunan sa Mahir.

FIM: Mecece alaƙar ka da harkar finafinan Hausa?

KABIR BAHAUSHE: Ina da alaƙa ta ƙut-da-ƙut da finafinan Hausa gaskiya, saboda a da mun yi hulɗa sosai da ‘yan wasa da masu shiryawa saboda shirin Alhaji Sanusi Anu na ‘Daga Bakin Mai Ita’. Ni da aboki na Isah Bawa Doro mu na son harkar sosai, sai mu ka riƙa bin su har aka saba. An taɓa jefa ni ma a wani fim na marigayiya Hajiya Binta Ƙofar Soro mai suna ‘Ɗaurin Zato’. Mun kuma riƙa shirya wasanni a Katsina, mu na gayyato irin su Adam Zango, Ado Gwanja da Jamila Nagudu da Nafisa Abdullahi da Umar M. Shareef da sauran su.

FIM: Ka na da sha’awar fitowa a fim?

KABIR BAHAUSHE: E, gaskiya. Amma na fi so na fito a fim don tallata sana’a ta ta MC ko aikin jarida gaskiya. Don ina son su sosai, abubuwa ne da Allah ya ƙaddara min su a rayuwa.

FIM: Ka na da wata ƙungiya mai suna Kakaki. Menene dalilin ƙirƙirar ta?

KABIR BAHAUSHE: To, ita Kakaki kamfanin kasuwanci ne na musamman domin amsar kwangilar shirya shirye-shirye a kafafen yaɗa labarai daga gwamnati da ɗaiɗaiku da ƙungiyoyi. Sannan kuma ana karrama muhimman mutanen da su ka samu nasara a rayuwar su bisa cancanta da ƙa’idoji gaskiya. Kuma alhamdu lillah, ana samun nasara, kowa na magana ya na jin daɗi kuma ya na so.

Kabir Sa’idu Bahaushe Ɗanɗagoro

FIM: Ka na da sha’awar shiga siyasa?

KABIR BAHAUSHE: Gaskiya ina son siyasa, amma dai ba takara ba sai don a ba ni muƙami. Na san ko ni wanene, ina da yaƙinin ɓangarorin da na ke da ƙwarewa zan taka muhimmiyar rawa ta a zo a gani. Allah ka yi mana zaɓi na alheri, wanda za mu taimaki cigaban al’umma ta fuskoki da dama.

FIM: Bayan MC da ka ke yi a yanzu, ka na yin wata sana’ar?

KABIR BAHAUSHE: E, kamar yadda na faɗa, na kan yi kasuwanci da kwangilar yaɗa labarai. Don ka ga ba ni da sakakken lokaci sosai.

FIM: Wanene ubangidan ka a harkar MC?

KABIR BAHAUSHE: A jami’a ubangida na Nura Aliyu Batsari, a waje DJ Amo da Rabi’u M. Yaro tun farko. Yawanci duk sun ajiye abubuwan. Amma dai yanzu MC Big Boy ne na ke ƙara gogewa da yawa a wurin sa, kuma ya na ƙauna ta da cigaba na gaskiya, tunda har aiki ya ke ba ni mu yi tare.

Kabir Bahaushe MC a ofis

FIM: Nawa ne farashin ka idan za ka yi wa mutum MC?

KABIR BAHAUSHE: Iya girman aikin ka iya kuɗin ka, don haka yanayin taron da wurin da aka kama da waɗanda aka gayyata ne abin lura, sai a sanya farashi. Kuma ha-babba da ha-ƙarami duk ana lura da su sosai!

FIM: Ka na da manaja wanda idan za a neme ka sai an fara magana da shi?

KABIR BAHAUSHE: Ba ni da manaja yanzu, amma gaskiya zan yi. Akwai shirye-shiryen musamman da ke akwai don abin ya yi kyau da ƙarko.

FIM: Ka na rainon yara da ka koya wa MC?

KABIR BAHAUSHE: E, akwai waɗanda su ke koyo da abokanai. Wasu ma saboda ni su ke farawa.

FIM: A ina ofishin ka ya ke?

KABIR BAHAUSHE: Ina da ofis a nan Mangal Plaza da ke a tsohuwar ma’aikatar ‘Water Board’ ta Katsina.

Kabir Bahaushe ya buƙaci matasa su riƙa girmama na gaba da su

FIM: Wane jan hankali za ka yi ga abokan sana’ar ka?

KABIR BAHAUSHE: Jan hankalin da na ke masu shi ne a girmama na gaba; wanda ya riga ka suna da ɗaukaka ko ma ya fi ka har abada. Sannan masu tasowa a daina wulaƙanta farashin mu, a kuma daina yin aiki kyauta. A riƙa shiga mai kyau, don wata rana na ga wani da wani koɗaɗɗen yadi a bainar jama’a da takalman roba, abin ya ɓata min rai sosai gaskiya.

Copyright © Fim Magazine
www.fimmagazine.com

Loading

Tags: aureBikiDahiru Barau MangalDandagoroDJ AmoFarfesa Bashir Aliyu Sallauhausa filmsIsah Bawa DoroKabir BahausheKabir Sa'idu Bahaushe DandagoroKatsinaMAAUNMCRabi'u M. YaroTaroUMYUVision FM Radio
Previous Post

KAI-TSAYE: Taron NDLEA da Kannywood

Next Post

Shin isowar Afakallah ce ta janyo ficewar Nabraska da Oscar daga zauren taron Kannywood da NDLEA?

Related Posts

An ɗaura auren darakta a Kannywood, Al-Amin Ciroma da ‘yar’uwar sa Sharifatu
Ranar Murna

An ɗaura auren darakta a Kannywood, Al-Amin Ciroma da ‘yar’uwar sa Sharifatu

May 2, 2025
Ƙarshen tika-tika, tik! A’ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu
Ranar Murna

Ƙarshen tika-tika, tik! A’ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu

April 25, 2025
Darakta Al-Amin Ciroma zai yi amarya a watan gobe, shekaru biyu bayan mutuwar auren sa da Wasila Isma’il 
Ranar Murna

Darakta Al-Amin Ciroma zai yi amarya a watan gobe, shekaru biyu bayan mutuwar auren sa da Wasila Isma’il 

April 20, 2025
Ahlan tare da 'yar sa Hassana, amaryar mako mai zuwa
Ranar Murna

Jarumi a Kannywood, Ahlan zai aurar da ‘yar sa Hassana

February 16, 2025
Daɗi kan daɗi: Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali ta samu jika da digirin digirgir
Ranar Murna

Daɗi kan daɗi: Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali ta samu jika da digirin digirgir

December 20, 2024
Mawaƙi Abdul Respect ya zama angon Hassana Abubakar
Ranar Murna

Mawaƙi Abdul Respect ya zama angon Hassana Abubakar

December 16, 2024
Next Post
Shin isowar Afakallah ce ta janyo ficewar Nabraska da Oscar daga zauren taron Kannywood da NDLEA?

Shin isowar Afakallah ce ta janyo ficewar Nabraska da Oscar daga zauren taron Kannywood da NDLEA?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!