ALLAHU Akbar! Allah ya yi wa wani babban mai tallafa wa harkar adabi a Nijeriya, ciki har da harkar finafinan Hausa, rasuwa, wato Farfesa Sule Bello.
Ya rasu a yau Lahadi, 3 ga Oktoba, 2021, bayan gajeren rashin lafiya.
Sule Bello ya rasu a Zariya, ya na da shekaru 73 a duniya.
Kafin rasuwar sa, babban malami ne a Sashen Tarihi na Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.
Haka kuma shi ne shugaban wani tsagi na jam’iyyar PRP na ƙasa.
Wata majiya ta ce za a yi jana’izar sa a gidan sa da ke Titin Maiduguri a unguwar Hotoro GRA, a Kano.
Majiyar ta ce kwana ɗaya kafin rasuwar sa, wato jiya, an shirya zai gabatar da wata lacca wadda wata ƙungiyar matasa ta shirya a kan batun samun ‘yancin Nijeriya, a wani taro da aka yi a Kano, to amma saboda ciwon sa ya tashi sai ya tura wakili.
Mujallar Fim ta gano cewa Farfesa Sule Bello ya taimaka wa harkar shirya finafinan Hausa a lokacin da ya ke riƙe da muƙamin Daraktan Hukumar Tarihi da Al’adun Gargajiya ta Jihar Kano (History and Culture Bureau). Kwanan nan ma ƙungiyar dattawan Kannywood ta naɗa shi shugaban kwamitin amintattu na Gidauniyar Kannywood (Kannywood Foundation).
Farfesa Sule Bello ya bada gagarumar gudunmawa a fagen kyautata al’adu, karantarwa, binciken tarihi da kuma gwagwarmayar siyasa a Afrika.
Mutum ne mara tsoro wajen faɗin gaskiya komai ɗacin ta.
An haifi Farfesa Sule Bello a Kano a ranar 5 ga Janairu, 1953. Ya yi karatu a Ƙaramar Makarantar Firamare ta Gidan Makama (1959 – 1962), Kano, da Babbar Makarantar Firamare ta Rano (1963-1966). Daga nan ya shiga Kwalejin Rumfa, Kano.
Sule ya yi karatun share fage a Jami’ar Ahmadu Bello, wato ABU, Zariya (1971-1972), sannan aka ɗauke shi ya karanta Kimiyyar Siyasa (Political Science) da Tarihi a jami’ar, ya gama a 1975.
An ɗauke shi aikin koyarwa a jami’ar a 1976. Ana cikin haka ya yi karatun digiri na biyu a fannin Tarihi a nan dai ABU ɗin, wanda wannan digirin ne aka ɗaga aka ba shi digiri na uku (PhD, History) a 1982. Taken kundin digirin sa na uku shi ne ‘State and Economy in Kano’ inda ya yi nazarin tattalin arzikin Kano a zamanin mulkin mallaka.
Farfesa Sule Bello ya ci gaba da koyarwa a Jami’ar Ahmadu Bello (in ban da lokacin da ya je ƙaro karatu a Jami’ar Kent, Canterbury, a Ingila) har zuwa 1987 lokacin da ya zama Daraktan Hukumar Tarihi da Al’adun Gargajiya ta Jihar Kano (History and Culture Bureau, HCB). Daga can kuma aka naɗa shi Daraktan Hukumar Fasaha da Al’adu ta Tarayya (National Council for Arts and Culture), Abuja, muƙamin da ya riƙe har zuwa shekarar 2000. A can ma ya ci gaba da taimaka wa harkar fim da sauran nau’o’i na fasaha da al’adun mutanen Nijeriya.
A cikin Yuni 2006, Sule Bello ya koma Jami’ar Ahmadu Bello domin ci gaba da koyarwa tare da dawo da martabar al’adar binciken tarihi da gabatar da laccoci da aka san Sashen Tarihi da shi a da, musamman a zamanin su marigayi Dakta Yusufu Bala Usman.
A tsakanin 2006 da 2009 ya riƙe muƙamin shugaba (HOD) na Sashen Tarihi na jami’ar. A cikin 2015 kuma ya zama Daraktan Cibiyar Bincike kan Cigaban Ƙasa (Institute of Development Research) ta ABU, sannan aka naɗa shi Daraktan Cibiyar Binciken Tarihi da Adanawa (Centre for Historical Research and Documentation) ta ABU, wurin da aka fi sani da Gidan Arewa ko ‘Arewa House’ da ke Kaduna.
Da ya ƙare, sai ya koma jami’ar ta ABU ya ci gaba da aikin sa na koyarwa. A lokacin ne ya shiga harkar siyasa tsundum, inda ya shiga jam’iyyar PRP, wato ‘Peoples’ Redemption Party’, ya yi cuɗanya sosai da jagoran ta, Alhaji Abdulƙadir Balarabe Musa.
Mujallar Fim ta gano cewa bayan rasuwar Balarabe Musa, Farfesa Sule Bello ya jagoranci yadda za a farfaɗo da martabar jam’iyyar domin ta sake yin tasiri a fagen zaɓe. A kan hakan, sun yi aiki mai yawa, to amma rikici ya lulluɓe jam’iyyar domin kuwa an tsaga ta gida biyu inda shi Farfesa Sule Bello ya zama shugaban tsagi ɗaya.
Mutuwar Farfesa Sule Bello ta biyo bayan ta wani zaƙaƙurin malamin tarihin a jami’ar ABU, wato Farfesa Ɗahiru Yahya, wanda ya rasu a ranar 3 ga Fabrairu, 2021. Mutane da yawa sun gigita, har ana ganin jami’ar ba ta taɓa ganin rashi da ya girgiza ta ba irin waɗannan rashe-rashe biyu tun lokacin da Dakta Yusufu Bala Usman ya rasu a cikin 2005.
Allah ya jiƙan su baki ɗaya, amin.