FIM ɗin James Bond na ƙarshe da aka saka jarumi Daniel Craig a ciki mai suna ‘No Time To Die’ ya wazgi cinikin tsakanin fam miliyan 4.5 zuwa fam miliyan 5 a ranar farko da aka nuna shi a gidajen sinima a faɗin Birtaniya da Ailand, a ƙiyasin furodusoshin shirin.
Wani rahoto da mujallar Fim ta fassaro daga gidan yanar ‘BBC News’ ya bayyana cewa an ɗage sakin fim ɗin na gumurzu a kasuwa ne sau tari saboda annobar korona, a yayin da ‘yan industiri su ka sanya ido su ga ko fim ɗin zai ɗaga kasuwar zuwa yadda ake samun ciniki kafin aukuwar annobar.
Cinikin da aka yi a ranar Alhamis ɗin nan ya zarce na wanda aka yi lokacin da aka saki fim ɗin James Bond mai suna ‘Spectre’ a cikin shekarar 2015 da kashi 13% amma ya gaza da kashi 26% na shirin ‘Skyfall’ da aka saki a 2012, inji kamfanin da ke shirya finafinan, wato Universal Pictures.
Kamfanin ya ƙara da cewa har wa yau shi ne “sakin fim da ya fi kowanne bada mamaki a Birtaniya a tarihi”.
Universal ya ce an saki ‘No Time to Die’ a sinimu 772 a Birtaniya da Ailand a ranar Alhamis – wanda hakan ya ɗara fim ɗin da ke riƙe da kambin da sinimu 25, wato ‘Star Wars: Rise of Skywalker,’ a cikin 2019.
Kamfanin kimiyyar shirin fim mai suna Gower Street Analytics ya taɓa hasashen cewa wannan fim zai samu cinikin jimillar kashi 92% na dukkan cinikin da za a yi a Birtaniya da Ailand a makon farko na sakin shi.
Sama da mutum 30,000 ne su ka kalli fim ɗin a daren da aka nuna shi a Birtaniya da Ailand, inda aka saida tikiti miliyan 1.6 na tsawon kwana huɗu kafin ranar ta zo, inji kamfanin. Hakan ya zarce cinikin tikiti kafin ranar sakin fim na shirin ‘Spectre’ da kashi 12% kuma ya yi daidai da na ‘Skyfall’ a lokaci guda.
Editan sinimu na mujallar ‘Screen International’, Charles Gant, ya ce cinikin fim ɗin ya kasance “abu mai wahala a yi hasashen shi”. Amma alƙaluman farko sun nuna cewa “fim ne da ya zama tilas mutum ya kalle shi ko da a wane matsayi ya ke”.
Gant ya bayyana hakan da “babban abin jin daɗi ga sinimu”, ya na mai ƙarawa da cewa fim ɗin ya “dawo da ‘yan kallo zuwa wuraren kallo” inda za su ga fosta da tirailar wasu finafinan da za a saki a cikin hunturu da ke tafe, irin su ‘Dune’, ‘Eternals’, ‘West Side Story’ da ‘Venom: Let There Be Carnage’.
A cewar sa, ba lallai ba ne sai ‘No Time To Die’ ya kamo ‘Spectre’ da ‘Skyfall’, waɗanda kowanen su ya yi cinikin jimillar fam miliyan 95 a sinimun Birtaniya da Ailand.
Wannan fim dai shi ne shirin James Bond na Daniel Craig na biyar kuma na ƙarshe. Daraktan nan ɗan Amurka, Cary Joji Fukunaga, shi ne ya bada umarnin sa, sannan taurarin shirin su ne Lea Seydoux, Rami Malek da Lashana Lynch. Ana sa ran zai yi cinikin dala miliyan 90 (wato fam miliyan 66.7) a faɗin diniya a ƙarshen mako na farko na sakin sa a kasuwa.
BBC sun ruwaito cewa yawancin masu sharhi sun yabi fim ɗin, har wasu sun ba shi tauraro biyar a sharhin su bayan an yi firimiyar sa a Zauren Royal Albert a farkon wannan makon.
Sai dai akwai waɗanda su ka soki fim ɗim, su ka ce bai dace da tsawon sa na minti 163 ba.
A wani bincike da wani kamfanin gidajen sinima mai suna Vue ya yi, an gano cewa ‘No Time To Die’ shi ne fim da yawancin ‘yan zuwa sinima su ke so su kalla a bana. Wani ɗan kallo, Steve Williams, wanda ya kalli fim ɗin a London, ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Press Association daga baya cewa ya “dace da jiran da aka yi masa”.
Ya ƙara da cewa “ba shakka kyakkyawan fim ne na ƙarshe ga Daniel Craig”, yayin da wani mai zuwa sinimar, Harry Wheeler, ya ce: “Shi ne fim ɗin Bond da ya fi kowane a tsawon lokaci. Ban je kallo a sinima ba a tsawon sama da shekara ɗaya kuma na ji daɗin sake komawa ta.”
A ƙasar Koriya ta Kudu ne aka fara sakin fim ɗin, a ranar Laraba, sai washegari a Birtaniya da Ailand, Birazil, Jamus, Italiya da kuma Nezalands. Amma ‘yan kallo a Amurka za su jira har zuwa ranar 8 ga Oktoba.
![]()





