• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

BBC Hausa sun fito da sabon shirin YouTube kan mata da matasa

by DAGA IRO MAMMAN
October 1, 2021
in Labarai
0
Madina Maishanu, mai gabatar da 'Mahangar Zamani'

Madina Maishanu, mai gabatar da 'Mahangar Zamani'

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

BBC Hausa sun bayyana cewa a gobe ne za su fara gabatar da wani shiri a kan mata da samari mai suna ‘Mahangar Zamani’ wanda za a riƙa nunawa a YouTube.

A sanarwar da BBC Hausa su ka turo wa mujallar Fim, sun bayyana cewa ma’aikan gidan yaɗa labaran ne za su riƙa haɗa sabon shirin, kuma su wallafa shi a YouTube.

Sanarwar ta ƙara da cewa burin su shi ne matasa da mata su kalli shirin.

Sanarwar ta ce shirin na tsawon minti 25 za a riƙa haska shi sau biyu a mako kuma zai riƙa taɓo al’amuran yau da kullum waɗanda matasa ke magana a kan su.

Wadda za ta riƙa gabatar da shirin dai ita ce Madina Maishanu, kuma wannan shiri na musamman zai riƙa taɓo al’amuran da ake tattaunawa waɗanda za a riƙa wallafawa a kafafen sada zumunta da kuma kafafen yaɗa labarai irin na da.

Madina ‘yar jarida ce wadda ta ƙware a kafofin yaɗa labarai iri daban-daban, kuma ta na cikin rukunin masu aiki a fagen soshiyal midiya. Ta taka rawa wajen jawo hankalin masu saurare da kallo matasa da mata a kafafen sada zumunta na zamani na BBC Hausa. 

Ita ce ta riƙa kawo labarin nan na zanga-zangar da aka yi kan George Floyd kai-tsaye daga gaban fadar White House. 

A tsokacin da ta yi kan shirin, Madina ta ce, “Naɗa ni mai gabatar da ‘Mahangar Zamani’ da aka yi wani cikar buri ne a gare ni. Ina jin daɗin ganin cewa shirin zai kawo mu kan gaba kuma ya ba mu damar samun magance matsaloli.”

Sanarwar ta ce za a bada sanarwar adireshin da mutum zai bi ya shiga wajen shirin a shafukan YouTube da Facebook na BBC Hausa don masu kallo su shiga a duk lokacin da su ka ga dama. 

Editan Sashen Hausa na BBC, Aliyu Tanko, ya ce: “Manufar shirin ita ce ta ba matasa da mata wata murya da kuma damar faɗin matsayin su a cikin al’ummar wannan zamani. Mu na so mu ba masu sauraren mu da kallon mu wata sabuwar fahimta da kuma damar ‘yancin yin muhawara a kan muhimman al’amura.”

Kashi na 1 – Dangantakar malamai da ɗalibai a jami’o’i: Kashi na farko na shirin ya dubi hulɗar da ba ta dace ba tsakanin malamai da ɗalibai a jami’o’in Nijeriya. A dukkan tsawon tattaunawar, masu kallo za su ga ra’ayoyi mabambanta a kan wannan zazzafan maudu’in.

Kashi na 2 – ‘Yancin mata a Arewacin Nijeriya: Wannan kashin zai yi warwarar ma’anoni daban-daban da mutane ke ba kalmar ‘yancin mata (feminism) daga yadda addini ya ƙarfafa mata, da yadda maza ke raina ƙarfin mata zuwa dankwafar da maza tare da cin fuskar su. A wannan kashin za ku ji ra’ayoyi daga wani namiji da wata mace.

Za a wallafa ‘Mahangar Zamani’ daga ƙarfe 10 na safe a ranar 2 ga Oktoba sannan daga nan za a riƙa yi sau biyu a mako.

Ku bi tattaunawar ta amfani da #MahangarZamani. 

Mai neman ƙarin bayani sai ya tuntuɓi wannan imel ɗin: marina.forsythe@bbc.co.uk

Loading

Tags: 'yancin mataAliyu TankoBBC HausafeminismMadina MaishanuMadina Maishanu.Mahangar ZamanimatamatasaSashen HausaYouTube
Previous Post

Hange mafi alheri: Martani ga Assadussunnah a kan Kannywood

Next Post

Shirin ‘No Time To Die’ na James Bond ya yi cinikin £5m a ranar farko a sinimun Birtaniya

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Jaruman shirin, wato Lashana Lynch (a hagu), Daniel Craig da Lea Seydoux sun halarci firimiyar fim ɗin a ranar Talata da ta gabata

Shirin 'No Time To Die' na James Bond ya yi cinikin £5m a ranar farko a sinimun Birtaniya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!