JAGORORIN Gamayyar Ƙungiyoyin Malamai da Ƙungiyoyin Addinin Musulunci na Jihar Kano sun yi watsi da sanarwar da wasu malamai su ka bayar jiya ta tsige Sheikh Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta jihar.
Bayanin hakan ya na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren ƙungiyar, Dakta Sa’eed Ahmad Dukawa, ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai a yau.
Sanarwar ta ce wancan mataki da waɗancan malaman su ka ɗauka an yi shi ne ba da sanin jagororin ba, kuma babu abin da zai haifar sai fitina a tsakanin malamai da ma Jihar Kano baki ɗaya.
Sanarwar ta buƙaci al’umma su yi watsi da waccan sanarwa da aka fitar, sannan ta ce sun ɗauki wannan matakin ne bisa amincewar jagororin Ƙadirriyya da Izala da ma Tijjaniya kamar su Farfesa Musa Borodo, Sheikh Khalifa Ƙaribullah Nasiru Kabara, Sheikh Abdulwahab Abdullah, Sheikh Ibrahim Shehu Maihula, Farfesa Muhammad Babangida, Dakta Bashir Aliyu Umar, Imam Muhammad Nasir Adam da kuma Dakta Mu’azzali Ibrahim Maibushira.
Daga ƙarshe sun tabbatar da cewa har yanzu Sheikh Ibrahim Khalil shi su ka sani a matsayin shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano domin hakan ne zai tabbatar da zaman lafiyar da ake da shi a Kano.
Idan kun tuna, a jiya mujallar Fim ta ba ku labarin yadda wasu malamai a Kano su ka bayyana sauke Sheikh Ibrahim Khalil daga karagar shugabancin Majalisar Malamai ta jihar.
A wata sanarwa da Ustaz Saifullahi Adam Assudani da Sheikh Khalifa Gama da Sheikh Abdulƙadir Ramadan da kuma Imam Jamil Abubakar su ka sanya wa hannu, malaman sun ce sun ɗauki matakin ne da yawun dukkan malaman jihar.
Sun lissafa wasu laifuka da su ka ce Malam Ibrahim Khalil ya aikata, ciki har da gaza ciyar da majalisar gaba, da rashin aikin da aka ɗora wa majalisar na yin fatawa ga al’umma kan sababbin matsalolin da ke tasowa a wannan zamanin, da yin amfani da ofishin majalisar wajen shirya tarurruka na ƙashin kan sa, ba na majalisar ba, da gaza haɗe kan ɓangarorin Izala, Ƙadirriyya da Tijjaniya a Kano, sannan kuma ya shiga siyasa har ma takara ya ke nema.
Malaman su ka ce sun maye gurbin sa da Farfesa Abdullah Saleh Pakistan.
Sun yi iƙirarin cewa sun ɗauki wannan matakin ne da goyon bayan kowane ɓangare daga Tijjaniya, Ƙadiriyya da Izala.