DA farko dai, ba na fatan wannan cuta ta ‘Coronavirus’ ta shigo mana nan, ina kuma addu’ar Allah ya yaye wa waɗanda su ka kamu da ita, mu kuma da ba mu kamu ba Allah ya tsare mu daga kamuwa.
Amma ina ganin wata magana da aka ce Shehu Usman ya taɓa faɗa ita ke tasiri a arewacin Nijeriya har yau. An ce Shehu Usman Ɗanfodiyo ya taɓa cewa: “Allah ya raba ka da jahilai biyu: Jahilin wani gari da jahilin wani gari.” Ya ƙara da cewa, “Shi wancan jahilin na farko, a garin neman araha a addini ya ke kashe kan sa, shi kuma ɗaya jahilin na ɗaya garin, duk inda ya yi masa rangwame sai ya tsananta wa kan sa.”
Wannan su ne a yau su ka tarwatsu a ko’ina a arewacin Nijeriya.
Babban abin da ke ba ni tsoro shi ne: ba cutar ‘Coronavirus’ ce abin tsoro ba, jahilci da taurin kai da ya yi mana katutu, wanda hakan ya sanya mu ka yi wa ƙaddara mummunar fahimta, mu ka zata cewa komai ma ya same mu – ko da da ganganci ne – za mu iya lafta wa Allah laifin, in an taɓa mu mu ce ƙaddara ce. Ka ga mutum ya yi wa yarinya ciki, in an ritsa shi ya ce ƙaddara ce! Wannan sai a ƙasar Hausa!
A yau na tattauna da mutane da dama a kan me su ke gani a kan matakan da aka ɗauka a duniya wajen shawo kan wannan baƙar fura dakan iblisai da Allah ya jarrabe mu da ita, musamman in aka yi da maganar hana ibada a jam’i?
Da yawa sun nuna rashin gamsuwar su da wannan mataki. Wani aboki na ya ce shi bai ga wani dalili na hana ibada ba domin, shi a tunanin sa, in irin wannan ta faru, kawai a haɗu a yi addu’a sai Allah ya yaye. Amma shi bai ga wata hujja ta hana haɗuwa wuri ɗaya a yi ibada ba.
Wani kuwa buɗar bakin sa sai cewa ya yi ai cutar ma ba ta zo mana nan ba, don me za a rufe mana makarantu a koro mana ‘ya’ya?
Wani aboki na kuma ɗan kasuwa cewa ya yi shi bai ga wata hujja ta rufe kan-iyakokin ƙasar nan ba, kawai a tabbatar duk wanda ya shigo an masa gwaji.
A wata majalisa da na ke zama kuwa, batun mafarki da Manzon Allah aka yi, da maganar cewa ya bada fatawar a duba a Ƙur’ani akwai wani gashi cikin Suratul Baƙara, in an ɗauko silin gashin, to sai a jiƙa a ruwa a sha. Wani ma har cewa ya yi shi fa ‘yar sa ta ɗauko, kuma sun sha.
Shi kuma wani a wurin ya ce ai akwai ma wasu da su ka musa zancen, amma da aka ɗauko Ƙur’anai aka duba sai aka samu gashin a kowanne da aka buda.
Da na dawo gida na tarar da labarin, sai ga Hassan, ɗa na ɗan shekara 5, ya buɗa Ƙur’anin sa izu biyu ya na neman gashin. To shi dai Hassan bai samu ba, ina zaton sai a izu 60 ake samu.
ADDINI, INADA DA LARURA
Ya kamata mutane su fahimta cewa Allah ya saukar mana da addini ne domin ya sauƙaƙa mana rayuwa, ba don ya wahalar da mu ba. Musulunci ba so ya ke a mutu don shi ba, so ya ke a rayu domin sa. Domin in ba mutane, to su wa za su yi Musuluncin? Ya zama dole Musulmi su rayu, in har ana so addini ya wanzu, domin mutane ke addinin ba addini ke mutane ba.
Wannan ne ya kawo mu batun fiƙihun larura a Musulunci. Domin ita larura kan maida haram ya zama halal, saboda Allah ya halicci ɗan’adam rarrauna, don haka sai ya sauƙaƙa masa hanyoyin da zai bauta masa.
In an lura, a duk abin da Allah ya bai wa ɗan’adam a duniya, sai da ya sanya masa ƙalubale a ciki. Da ya ba shi basirar neman abinci, sai ya sanya masa wasu ƙalubale a hanyar neman, haka ma da ya sanya masa sha’awa, sai ya sanya masa wasu ƙalubale a hanyar biyan buƙatar sha’awar. Wannan haka ya ke a ɓangaren neman arziki, muhalli, sutura da sauran su.
Waɗannan ƙalubale su kan zamar wa mutum lalura da har za ta kai ga Allah mai rahama ya ɗauke masa wasu hukunce-hukunce a kan sa. Wasu ma ba su kai matsalar annoba ba, amma Allah ya sauke masa bin wasu dokokin, kuma yadda ya sauke dokokin, shi kan sa ibada ne.
Misali: matafiyi sai aka ce masa ya yi ƙasaru, wato ya rage salloli masu raka’a huɗu zuwa biyu, duk kuwa da cewa raka’a huɗu aka yi umarnin da a yi. Haka ma sanyi kan sanya a yi alwala ba a wanke ƙafa ba, sai a shafi huffi kawai.
Kai, wasu ma sun ce ba sai sanyi ba, domin hadisin ya nuna ba lallai sai da sanyi ba. Lalurar cuta kan iya sanyawa a yi sallah ba alwala, misali mai basir da y ya ke yawan sa shi tusa kan iya yin sallah ko da alwalar sa ta warware.
Ga mai janabar da bai samu ruwa ba, ko kuma ruwan ya yi masa ƙaranci, aka ce an yarda ya yi burgima. Ko kuma in ya yi alwala da ruwan zai iya rasa na sha, aka ce ya yi taimama, ga shi kuwa yin sallah ba alwala kafirci ne.
Kai, saboda tsoron mutuwa Allah ya bai wa Musulmi damar yin salatil kaufi, domin dai so ake a rayu, ba a mutu ba.
Hadisai sun tabbatar da cewa matsaloli sun sha taso wa al’umma a zamanin Manzon Allah (saw), da su kan sa a haƙura da wasu ibadun, komai muhimmamcin su kuwa. An taɓa samun ruwan sama mai ƙarfi da har sai da Manzon Allah (saw) ya umarci Bilalu da ya sanar da mutane su yi sallah a gida ba sai sun zo jam’i ba.
Haka ma larura kan tasovwa al’umma da har ma sallar ta kan gagara. Mu ɗauki waƙi’ar da ta faru a Makka, a shekarar 692, tsakanin Hujjaj bin Yusuf wanda halifa Abdulmalik bin Marwan ya aiko da soja dubu biyu, da kuma Abdullahi bin Zubayr da yadda ya rinƙa ruwan duwatsu a Makka, sai da ya rusa Ka’aba, kamar yadda masana tarihi su ka tabbatar.
A wannan lokaci, ko kuma wannan yaƙi, da aka shafe wata bakwai ana gwabzawa, musamman a lokacin da aka yi wannan balahira a Ka’aba, ai ba maganar ibada, saboda kowa ta kan sa ya ke.
A Yaƙin Harra ma da aka yi a shekarar 682, Marwan bin Hakam ya yi wa garin Madina kaca-kaca, wanda sai da ya kwana uku ya na ɓarna a garin, har ta kai ga an shafe kwanaki ko kiran sallah ba a yi a Masallacin Manzon Allah (saw).
Mutuwa ko kisa kan zo ne a matakin ƙarshe, bayan an tabbatar da duk wata hanyar maslaha ta ƙare. Manzon Allah ya nuna haka a Hudaibiyya. Domin ya zo wa Makka da rundunar da za ta iya ƙare mutanen garin a cikin ƙanƙanin lokaci, amma ya zaɓi sulhu koma-bayan ɗaukar fansar cin mutuncin da korar da su ka yi masa.
Masu tunanin ko a mutu ko a yi rai sai sun yi bautar su yadda su ka saba, ya kamata su natsu su sani, Musulunci ya fi damuwa da rayuwar su ba mutuwar su ba.
Masu ganin akwai wani gashi da ke maganin wannan cuta, su sani Manzon Allah (saw) ya sha yin rashin lafiya, haka ma ‘ya’yan sa da ya ke matuƙar so, kuma ya san da akwai addu’a, kuma ya san in ya roƙa, Allah zai masa, amma magani ya nema, bai tsaya ga addu’a ba kawai. In da da wani gashi da aka gani a Suratul Baƙara, da tuni ya sanar da sahabbai sun rinƙa dubawa su na sha saboda maganin annoba.
Babbar hanya ta magance wannan bala’i ita ce a koma kan koyarwar sa da ya yi, a tsabtace jiki, a tsabtace muhalli, a kuma ɗauki shawarar masana. Ya yi horo da cewa, “Mu tambayi masana in mun kasance ba mu sani ba.” Ya nuna muhimmancin wanke hannu kafin da bayan an ci abinci. Ya bayyana mana cewa “kowacce cuta ta na da magani.”
A bai wa masana dama su nemo mana wannan magani. A kiyaye dokokin da su ka kafa, a nemi shawarar su a kowane lokaci. Wannan shi ne mafita, ba wani gashi da aka gani a mafarki ba.
In kunne ya ji, jiki ya tsira!
Allah ya kiyaye mu daga wannan bala’i da ya dirkako.