FITACCEN jarumin Kannywood, Yakubu Muhammad, ya sake nuna kishin sa ga addini da al’umma bayan ya gina wata sabuwar makarantar Islamiyya ta zamani tare da miƙa ta kyauta ga al’ummar unguwar Hotoro Tishama da ke Ƙaramar Hukumar Nasarawa a Birnin Kano.
Makarantar, wadda aka gina tare da samar mata da dukkanin kayan karatu da ake buƙata, an miƙa ta ne a wani taro na musamman da aka gudanar a yammacin jiya Juma’a.
An gina makarantar ne domin ta kasance sadaƙatul jariya ga mahaifin jarumin, marigayi Sheikh Usman.
An miƙa makarantar ga Alaramma Malam Muhammad Tukur, wanda zai jagoranci harkokin koyar da Alƙur’ani Mai Girma da sauran ilimomin addinin Musulunci ga yara da matasa a yankin.
Taron ya samu halartar manyan jaruman Kannywood da suka haɗa da Ali Nuhu, Sani Musa Danja, Abba Al-Mustapha, Abdul Amart, Falalu A. Ɗorayi, Nazifi Asnanic da sauran fitattun mutane daga masana’antar shirya finafinai da al’umma baki ɗaya.
Da yake jawabi a wajen taron, Alhaji Yakubu Muhammad ya bayyana cewa tun a wata ziyara da ya kai unguwar Tishama ne ya lura da yadda yara suke karatun Islamiyya cikin mawuyacin hali a ƙarƙashin wani tsohon gini da bai dace da yanayin karatu ba.
Ya ce: “Lokacin da na ga halin da yaran suke ciki, sai na yanke shawarar sayen wannan gida mai ɗakuna huɗu tare da banɗaki, na gyara shi gaba ɗaya, na samar da kayan karatu, domin a mayar da shi makarantar Islamiyya mai inganci da za ta amfani al’ummar yankin.”

Jarumin ya ƙara da cewa sanya wa makarantar sunan mahaifin sa wata hanya ce ta neman ci gaba da isar da ladar wannan aikin alheri gare shi, yana mai fatan Allah ya sanya ta zama abin amfanar al’umma na dogon lokaci.
Mahalarta taron da mazauna unguwar sun bayyana jin daɗin su tare da yaba wa Yakubu bisa wannan gagarumin aiki na alheri. Sun ce gina makarantar zai taimaka matuƙa wajen bunƙasa ilimin addini, kyawawan ɗabi’a da tarbiyyar yara a yankin.
Wannan aiki na Yakubu Muhammad ya sake nuna yadda fitattun mutane za su iya amfani da matsayin su da dukiyar su wajen kawo cigaba mai ɗorewa ga al’umma, musamman a fannin ilimi da tarbiyya.
![]()







