JAMA’AR unguwar Ɗanbare da ke cikin birnin Kano sun wayi gari jiya Juma’a cikin jimami bayan gano gawar wani matashi mai suna Isma’il Makaya a gidan fitacciyar jarumar TikTok, Fati Cele.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne bayan an ji ƙarar neman taimako daga cikin gidan, inda Fati take ihun cewa gobara ta tashi a gidan ta. Nan take maƙwabta suka garzaya domin kai ɗauki, sai dai a lokacin da suka shiga gidan, sun tarar da gawar Isma’il, wanda aka ce saurayin ta ne, yana ɗauke da raunuka tare da alamun ƙonewa a wasu sassan jikin sa.
Marigayin ya kasance ɗan kasuwa ne mai sana’ar sayar da kayan kwalliya a unguwar Hotoro da ke cikin birnin Kano.
Bayan faruwar lamarin, jami’an ‘yan sanda na ofishin Ɗorayi Babba sun tsare Fati domin gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar, yayin da hukumomin tsaro suke ci gaba da tattara bayanai domin gano haƙiƙanin abin da ya faru.
A yau Asabar ne aka gudanar da jana’izar marigayi Isma’il Makaya a gidan su da ke Unguwa Uku ‘Yan Awaki, a Ƙaramar Hukumar Tarauni ta Jihar Kano, inda ‘yan’uwa da abokan arziki suka halarta cikin alhini.
Wasu bayanai daga mutanen da ke kusa da Fati Cele sun ce ita da marigayin sun taɓa samun saɓani a baya wanda ya kai ga rabuwar su, sai dai daga baya sun sake sasantawa tare da dawo da dangantakar su.

Fati Cele, wadda ‘yar asalin Jihar Borno ce, tana zaune ne a matsayin mai haya a unguwar Ɗanbare. Ta yi suna sosai a TikTok, inda take da mabiya sama da 32,500. Haka kuma an san ta da fitowa a wasannin talla na gala a wani gidan gala da ke Sabon Garin Kano.
Tun bayan aukuwar lamarin, dandalin TikTok ya cika da saƙonnin ta’aziyya da alhini daga abokai da masoyan marigayin, yayin da wasu suke kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar abin da ya jawo rasuwar sa.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan Kano ba ta fitar da cikakken bayani kan sakamakon binciken da take gudanarwa ba.
![]()







