FITACCIYAR furodusar Kannywood, Hajiya Mansurah Isah, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta fito da wata doka da za ta sa gidajen sinima su riƙa nuna finafinan Hausa a duk faɗin Nijeriya.
Mansurah, wadda tsohuwar jaruma ce, ta bayyana haka ne cikin wani guntun bidiyo mai tsawon sakan 59 da ta wallafa a Instagram a yau.
Furodusar ta bayyana mamaki kan yadda gwamnati ta ke da ikon sa hannu kan yadda ake gudanar da sana’ar sinima a Nijeriya amma ta kasa umartar masu gidajen sinima su riƙa haska finafinan Hausa.
A bayanin da ta yi cikin kakkausar murya, Mansurah ta ce, “Ashe Gwamnatin Tarayya ta na iya saka hannu a harkar sinima a Nijeriya? Ai ni da ban sani ba!
“To mu masu shirya finafinan Hausa wane laifi mu ka yi ne da har za a ce ba za a riƙa haska finafinan mu ba a duk faɗin Nijeriya?”
Furodusar ta yi nuni da cewa gidajen sinima su na nuna finafinan Yarbanci da na Ibo da na Turanci daga kudancin ƙasar nan, na Hausa kaɗai ne ba za su nuna ba.
Ta ce, “To me ya sa mu furodusoshin finafinan Hausa aka bar mu a baya?
“Haba! A taimaka mana mana, a taimaka mana. A yi doka.”
Furodusar ta yi kira ga jami’an hukuma da su fito da dokar da za ta sa gidajen sinima su riƙa nuna finafinan Hausa kamar yadda su ke nuna na ‘yan Nollywood.
Ta ce, “Ku nuna yaren ku, ku nuna al’adar ku. Ku ƙaunace mu. Ku sa finafinan mu a dinga nunawa a duk Najeriya.”
Ta yi nuni da yadda ake kawo fim ɗin Turanci a Kano a dinga haska shi, amma ba za a iya ɗaukar fim ɗin Hausa a kai shi Legas a riƙa nunawa ba.
“Meye dalili? Me mu ka yi?” inji ta.
Bugu da ƙari, Mansurah ta yi nuni da yadda ‘yan Kannywood su ke mara wa gwamnati baya, amma kuma ita ba ta taimaka masu ta wannan fannin.
Ta ce, “Ba ma zagi, ba ma cin zarafin ku, amma duk da haka mu ne koma-baya.
“Me ku ke so da mu? Na roƙe ku da girman Allah ku taimaka mana.”
Ita dai Mansurah, a makon jiya ta saki sabon fim ɗin ta da ta saki mai suna ‘Fanan’ ya kafa tarihi wajen samun babbar riba irin wadda ba a taɓa gani ba a gidajen kallo na Kano cikin ‘yan shekarun nan.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labarin yadda gwamnati ta hana a nuna wani fim ɗin Hollywood mai suna ‘Eternals’ a gidajen sinima na Nijeriya saboda ya na ɗauke da jigon luwaɗi.
A da, an tsara cewa za a fara nuna fim ɗin ne a ranar Juma’a da ta gabata.